← Book details Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 93

Sashe 87

Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bappa yace "Ta tafi bata tsaya ta saurare ni ba, bata kuma ta蓳a yimin haka ba, HAMDAH, bata ta蓳a ketare magana ta ba, hakika tana cikin tsoro da tuno rayuwar ta ta baya tana tsoron kada ta kuma shiga halin da ta shiga a baya."
cikin rawar murya da zubda kwalla Ya Mas'ud yace "Bappa numfashin Ya SALEEM yana kokarin barin jikin sa."
salati Bappa yayi da sauri ya shige cikin 蓷akin in da likitoti suke tsaye ca a kansa.
tuni kowa ya fara kwalla su Aunty Rafee'at har da jan shassheka,
Mamie tayi baya duk daure zuciyar ta da take sai da hawaye suka zubo mata,
ta zauna a gefe tana mai cigaba da zubda kwalla.
da sauri Ummi ta nufi kofar fita tayi waje,
direba ta saka ya kaita gida da sauri tana isa,
direct sashin ta ta wuce tun daga parlour take jiyo shesshekar kuka, da sauri ta karasa cikin bedroom.
ina zaune cikin 蓷akin naha蓷a kai da guiwa sai rusar kuka nake,
a sannu ta karaso kusa da ni ta zauna gefe, a hankali ta dafa kafa蓷a ta tare da kiran suna na tace
"HAMDAH na tabbata kinsan kuna da 蓷acin rabuwa irin na mutuwa, HAMDAH ga uwa can tana kukan rabuwa da 蓷an ta da yake kokarin barin duniya a ta sanadiyyar ki, shin bazaki zamo mai yafiya a rayuwa ba, shin kin san falala da tarin lada a gun duk wan da ya ceci wani daga fa蓷a wa wata halaka, 蓷an uwan ki ne fa shi shin ashe bazaki zamo mai share mana hawaye ba, ni mahaifiyar ki ina mai rokon ki da kije ki ceci 蓷an uwan ki, ba zanyi miki dole ba amma ki sani har idan SALEEM ya mutu duk ahali zamu rataya miki alhakin mutuwar sa a kanki,
sannan baza mu ta蓳a dai na ganin ki a matsayin wan da takasa taimakon ahalin ta ba."
Ummi ta mike tana sharar kwalla ta nufi kofa zata fita,
da gudu na mike naje na ruko hannun Ummi, cikin muryar kuka nace
"Ummi na kiyi hakuri kar kuyi fushi da ni Ummi ina jin tsoro ina jin tsoro ne."
kai ta girgiza min tare da share min hawaye ta ruko hannuna gam-gam
cike da karfafa guiwa tace
"Babu abun da zai faru da yardar Allah kisawa zuciyar ki hakan, zamu tsaya miki da karfin ikon Ubangiji babu abin da zai kuma faruwa."
kai nashiga gya蓷a wa alamun gamsuwa yayin da hawaye ke ci gaba da zuba a ido na.
ta janyo hannuna ta ha蓷o da na su Naseem muka fita.
koda muka iso asibitin hannuna Ummi ta kuma ruko wa tana 蓷auke da Ahmad karami Naseem da Nasmah suna gaban mu, muka shiga asibitin.
su Mamie da Aunty Rafee'at Aunty Jaleela Nusaiba Fauza suna tsastsaye a bakin kofar 蓷akin da Ya SALEEM yake ko wannen su kuka yake da hawayen sa,
jiki a sanyaye muka karaso in da suke, hankali tashe Ummi ke tambayar su lafiya. cikin zubda kwalla
Aunty Jaleela tace "Ummi Ya SALEEM baya numfashi."
tuni hawaye yafara zuba a idanun Ummi,
niko jiki na ne ya 蓷au ki 蓳ari, Ummi ta kuma ruko ni gam ta janyo ni muka shige cikin 蓷aki.
doctors ne ke tsaye a kansa suna ta fafutukar ceto numfashin sa,
Bappa Abba Abbu Ya Mas'ud suna tsaye a gefe.
Bappa sai anbaton sunan Allah yake Ya Mas'ud ko sai sharar kwalla yake, lokaci zuwa lokaci Abba ke kai hannunsa karkashin idanunsa yana share 蓷an guntun kwallar dake fito masa, a 蓳angaren Abbu ma haka.
蓳arin jiki na ne ya karu lokacin da idanuna ya sauka kan Ya SALEEM dake kwance ko matsi baya yi babu alamun numfashi tattare da shi,
sosai jiki na ke kakkarwa, zuciya ta tayi rauni tausayi mai ha蓷e da kawa zucin 蓷an uwa suka lullu蓳e ni, ko ba komai Ya SALEEM jina na ne dole naji makamancin hakan a tattare da ni, domin 蓷an uwa yawuci wasa koda ace kuwa a kullum yana kuntatawa rayuwar ka, ka gansa a gaban ka tamkar mutacce dole zuciyar ka ta girgiza.
da sauri na fizge hannuna da gudu na fasa sakanin doctors 蓷in na fa蓷a a jikin sa tare da girgiza shi ina fa蓷in
"Ya SALEEM kar ka mutu ka tashi dan Allah ka tashi kar ka mutu Ya SALEEM Ya SALEEM Ya SALEEM".
na karasa da kiran sunan sa da karfi ina mai jijjiga shi.
tuni Naseem da Nasmah suka saki kuka suna kiran Daddy Daddy.
sosai nake gargiza shi ina kiran sunan sa yayin da nake rusa kuka mai karfi,
a raina ina ayyana shike nan babban yayan mu ya tafi ya barmu, duk miskilancin halin sa da rashin dariyar sa muna son sa a haka, ga 拼an uwa na da mahaifiyar sa tana kukan rashin sa, hakika rashin wani naka na da zafi, shike nan shima ya tafi bazai dawo ba, kamar yadda Inna da Ahmad suka tafi tafiyar da babu dawowa..
wani kuka ne nakuma sake wa da karfi ina fa蓷in
"Ya SALEEM kai kar ka tafi dan Allah kada ka tafi ka barmu ka tashi Ya SALEEM ka tashi."
nayi maganar ina mai girgiza shi da karfi.
fuska ta na kife cikin kirjin sa ina jujjuya fuskar tawa da gogashi cikin kirjin nasa ina mai ci gaba da kukan.
a sannu ya sauke wani irin numfashi mai tsawo kana yashiga motsi da idanunsa.
cikin matukar mamaki likitotin ke kallon ikon Allah, mutumin da numfashin sa ya tafi bugun a gogon hannun sa ne ka蓷ai yake iya tabbatar musu da yana raye shima bugun hannun nasa yana daf da tafi dan sai ya 蓷au tsawon mintina masu dama kafin ya 蓷an buga sai ka lura sosai kafin ga gane hakan shima,
da sauri su Bappa suka maso suna mai mamakin hakan suma, dan gaba 蓷aya sun gama cire rai da shi suna jiran jin ta bakin likitotin kawai.
da sauri na 蓷ago kai na jin yana motsa jikin sa na kurawa fuskar sa iso, ganin idanunsa suna motsi a lamar yana son bu蓷e su.
da sauri nace "Ya SAKEEM bu蓷e idanun ka Ya SALEEM ka bu蓷e ka hu蓷e kada ka tafi ka harmu."
a hankali yashiga bu蓷e idanun nasa har ya ida bu蓷e su a kan fuska ta,
a sannu ya 蓷ago hannunsa ya sauke sa kan nawa ya rike shi gam, a hankali ya juya fuskarsa in da su Naseem suke yayi musu alama da hannu da suzo in da yake, suka matso bakin gadon suka kwantar da kansu a jikin sa, numfashi mai sauti ya sauke yana mai da蓷a damke hannuna tare da shafa kan yaran da hannunsa guda.
gaba ki 蓷aya 拼an cikin 蓷akin farin ciki ne bayyane a kan fuskokin su,
hatta likitotin, 蓷aya daga cikin Dr ya dube ni da murmushi yace
"Sannu da taya mu ai kin da ke kokarin gagarar mu."
"Itace maganin ai."
蓷aya Dr dake kusa da shi ya fa蓷a yana 蓷an dariya...

Ya Mas'ud yafita da sauri sai gashi da su Mamie sun shigo har suna rige-rigen shigo wa.
fuskar Mamie 蓷auke da murmushi mai bayyana tsantsar farin cikin ganin sa ya farfa蓷o daga sammanin mutuwar da suka saka masa.
kowa sai sannu yake masa, sai dai babu wan da ya amsa shi, hakan bai dami kowa ba dan kowa yasan hakan halin sa ne.
hannu na dake cikin nasa na 蓷an motsa ina kokarin janye hannun nawa,
dan irin kallon da yake min yasa ni jin wani iri cikin jikina, ga kuma idanun kowa a kanmu.
gam yada 蓷a rike hannun nawa bai kuma fasa bina da irin wannan kallon ba.
Aunty Rafee'at da bakin ta ya kasa rufuwa dan murna ta juyo ta kalli mijin ta Dr Farouq, shima murmushi yayi tare da 蓷an dungurin ta cikin kasa da murya ya ce
"Kin ga yayan ki ko so nason kashe shi ga kallon da yake mata kamar bashi bane 蓷azu ke kokarin mutuwa."
hararar wasa tayi masa tace
"To an fa蓷a maka so karya ne."
yace "Ni zan bada shaida ba karya bace gashi ina kan fama da shi a kan ki."
ya karasa maganar da kashe mata ido,
dariya tayi tana ture kafa蓷ar sa...

Hannu na na zare cikin nasa da 蓷an sauri cikin jin kunya ganin su Abbu sun matso kusa da shi suna yi masa sannu,
shiko idanunsa na kaina, yana yi min wani irin kallon cikin ido.
baya nayi ina mai jin kunya.
bayan wasu 蓷an mintina likitoti sukace a 蓷an bashi guri ya huta bayan sun masa allurai...
a ranan da yamma Ya SALEEM yace shi zai koma gida, Dr Farooq yace ya bari ya da蓷a jin kwarin jikin sa,
yace shi sam zai tafi dan shi lafiyar sa lau,
sai da su Bappa suka sa baki kafin da kyar ya yarda.
kwanan sa uku a asibitin kullum a can muke wuni dukan mu, idan na shiga 蓷akin yi masa sannu da jiki haka zai kafe ni da ido yata kallo na kamar bai ta蓳a sani na ba.
su Nasmah kam ko da yaushe suna jikin sa, sai dare idan zamu koma gida suke rabuwa da shi.
ranar da ya cika kwana hu蓷u yace bazai kuma kara kwana cikin asibitin ba, dun dole a ka bashi sallama.
nuka koma gida kowa hankalin sa kwance da farin cikin samun lafiyar sa.....
Chapter 87 · 0% Book details