← Book details Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 93

Sashe 26

Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yau Monday kamar yan da nasa ba na rako su Nasmah gun mota, Yakubu dake goge motar yayi saurin bu蓷e motar nasaka su ciki,bayani na yiwa yakubu kamar yan da mukayi da shugaban makarantar su idan sun je za'a ha蓷a su da wani domin yayi musu jagora zuwa 蓷aya makarantar.
ina tsaye ina 蓷aga musu hannu har suka fita...

Kai tsaye Yakubu ya蓷au hanyar makarantar, kamar koda yaushe hira yake da yaran yanata washewa da dariya kamar yan da suma suke ta washe baki.
suna isa bakin get 蓷in makarantar yayi parking yafito, kana ya bu蓷e musu suka fito, suna fita suka shige cikin makarantar direct office suka nufa daga nan aka ha蓷a su da wani malami da zai kai su 蓷aya makarantar, suka fito tare.
suna fita bakin get 蓷in school 蓷in,
wata lafiyayyi zazzafar mota tayi parking a gefe, tun kan motar ta kakarasa parking Naseem yafara murna yana fa蓷in
"Laa ga Daddy yazo laa ga Daddy yazo."
Nasmah ma kuwa ihun murna ta sake tare da sa gudu sukayi gurin motar.
da sauri ya bu蓷e motar ya fito yaware hannayen sa ai ko da gudu suka shige jikin sa ya rungume su, duk suka saki dariya har dashi, kana ya mike yashiga 蓷aga su yana cillasu sama sai kya-kya ta dariya suke.
sai da yayi wa kowannen su haka har sau uku kana yadire su kasa,
Yakubu ya karaso in da suke yana washe baki da fa蓷in
"Ranka shi da蓷i barka da war haka."
amsa wa yayi fuska a sake sai dai gaba 蓷aya hankalin sa na kan su Nasnah da suke ta zuba masa surutu.
shima wannan malamin da aka ha蓷o su da shi ya karaso yana fa蓷in
"Barka da zuwa yella蓳oi."
yace "Yau wa, yaya ji da 蓷aliban?."
malamin yawashe baki tare da fa蓷in
"Muna kai kam."
yace "Masha Allah."
malamin ne ya dubi yakubu da kuma yaran yace
"To muje ko."
yayi maganar yana duban motar su.
sai a lokacin Ahmad ya 蓷ago da kallon sa kan yaran yadawo da shi kan su Yakubu kana yace
"Ina kuma za'a je ba makaranta za'a shiga ba?".
yayi maganar yana shafa kan su Naseem.
malamin yace "A'a zamu tafi da sune 蓷aya makarantar mu."
duban sa Ahmad ya kuma da alamun tabbayoyi 蓷auke a fuskar sa,
kana yace "Wacce makarantar kuma?."
yace "茒aya daga cikin makarantar mu ne za'a mai da su."
da fuskantar mamaki Ahmad yace
"Har sun gama wannan makarantar ne da za'a tura su wata makarantar daban?."
kai malamin ya girgiza tare da fa蓷in
"A'a ai za'a sauya musu makarantar ne anyi musu transfer can ne."
蓷an shiru Ahmad yayi kana yace
"Malam 蓷in yana ciki?."
kai malamin ya gya蓷a tare da fa蓷in
"Eh yana ciki." yace
"Okay to muna zuwa." yafa蓷a tare da gyara rukon Naseem da Nasmah a kowani hannun sa guda, ya janyo su suka shige cikin makarantar.

Malamin ya dubi Yakubu dake ta washe baki yace
"Wai nikam da ma 拼a拼an Ahmad Tijjaji Sabil ne kake kawowa makaranta?."
Yakubu ya da蓷a washe baki yace "A'a 拼a拼an me *HAM'NAS* Company ne fa."
"Au 拼a拼an mai *HAM'NAS* Company ne to shi Ahmad Sabil dangin su ne? lallai Allah mai yin yan da yaso yaha蓷a family guda da tarin dukiya."
Yakubu yace "Eh 拼an uwa ne."
yafa蓷i hakan ne kawai dan bashi da amsar bashi, dan shi kansa bai isa yace suna da dangan taka ko basu da shi ba, a matsayin sa na mai ai kin gidan ba lallai dole yasan dan gin gidan ba, san nan kuma baya so ya disga kan sa gaban malamin, ko ba komai shi ma za'a rika yi masa kallon wani...
suna nan tsaye
zuwa can Ahmad yafito shi ka蓷ai batare da yaran ba.
ido suka zuba masa ganin yafito shi ka蓷ai, yakaraso in da suke, duban malamin yayi tare da fa蓷in
"Ka koma kacigaba da koyar da 蓷aliban ka, kai kuma ka koma gida ka dawo da wuri ka 蓷au ke su."
yakara she maganar da duban Yakubu.
Yakubu yace
"Ranka shi da蓷e hajiya tace na tsaya sai mun kai su kafin na komo gida."

Yace "Kar ka damu kaje ka abin ka."
yace To. yashiga mota in da tuni malamin ma yakoma cikin makarantar.
shiko Ahmad a hankali ya isa jikin motar sa ya shige ciki...

Da misalin karfe 12
a hankali na mike na shige bayi wanka nayi ha蓷e da 蓷auro al'wala nafito,nashirya cikin wani doguwar rigar atamfa pauda da man lip kawai na goga sai turare dana fesa a jikina,
a hankali na isa jikin window labulen window'n na蓷an janye shi gefe tare da zuge glass.
ido na kurawa furannin da suke ta ka蓷a wa gwanin ban shawa,
idanuna na sauke can bakin get jin karar bu蓷e get 蓷in, da murmushi nake kallon kofar,
dan nasan su Naseem ne suka dawo, 蓷an gimtse annurin fuska ta nayi ganin ba motar kai su makaranta bane wata motar ne daban ta shigo.
a sannu motar ta isa ta gyara parking a gefen farfajiyar gidan,
an 蓷au tsawon minti 10 kafin aka bu蓷e motar,
ido na waro cikin tsananin mamaki da shiga shoc ganin wan da yafito daga cikin motar, cikin matukar kufula nake kallon sa yayin da yazaga 蓷aya gefen ya bu蓷e, sai ganin Naseem da Nasmah nayi sun fito daga cikin motar suna ta washe ba ki.
"What! me nake gani haka, yaran da nasa a canza musu makaranta domin sa wai bin su yakuma yi?."
cikin matukar 蓳acin rai nasaki labulen da sauri na juya nafita a 蓷akin na nufi kasa,
da sauri na ke sauka har ina ha蓷a step cikin hanzari nakarasa sauka nayi waje da sauri.

Suna tsate jikin mota sai zuba masa surutu suke shiko sai binsu da murmushi mai ha蓷e da dariya yake,
tun kan na karaso in da suke nashiga fa蓷in
"Kai malam wai meye hakan ne, wai meye gamin ka da yaran nan ne kam?!."
dai-dai lokacin na iso in da suke, kugu na rike cikin masifa nacigaba da fa蓷in
"Meye da lilin ka na wani shishige musu da kake kana ta wani cusa musu
wani ra'ayi meye nufin ka da su?."
maganar nake a tsai-tsaiye kuma cikin 蓷aga murya cikin masifa nakuma fa蓷in
"Bana bukatar wani ya ra蓳e su da manufa irin naka kagane ko malam?."
tun da na fara maganar ido kawai ya zuba min batare da yace komai ba, idanun sa kan lip 蓷ina, a sannu ya蓷an yi baya ya jin gina bayan sa jikin mota hannayen sa ya sarkafe a kirjin sa, harshen sa ya蓷an zuro waje yalashi pink lip 蓷in sa,
har lokacin fuskar sa na 蓷auke da murmushi wan da dimple suka da蓷a kawata annurin fuskar sa.
cikin kuma 蓷aga murya na dubi su Naseem nace
"Idan baku wuce kun shiga ciki ba na rantse sai na 蓳a蓳蓳ala yaro anan gurin ku wuce mutafi nace!."
nafa蓷a ina nuna musu hanya.
Nasmah tace "Mommy ja mu jo."
ido na waro wato ma na jira su kenan sai sun gama abun da suke.
shiko wani murmuahi yakuma sakewa.
tsayuwar sa ya gyara tare da duban yaran kana ya mai da duban sa kai na sannan yafara magana
"Zaki 蓳alla su?."
ya fa蓷a tare da kuma sakin wani murmushi kana ya 蓷an sun kuya yarage tsawon sa dai-dai tsawon yaran ya dubi ko wannen su yace
"Kuje ciki ayi muku wanka kuci abinci ku kwanta ku huta kuyi bacci idan kun tashi kuyi karatu gobe zan tambaye ku karan tun da kukayi kun ji ko?."
kai suka gya蓷a masa suna fa蓷in
"Tom." yace "Yauwa to maza a je ciki."
Naseem yace "Daddy dakajo anjima?."
kai yagya蓷a yana mai cigaba da wannan murmishi wan da kamar da shi aka gina fuskar sa yace
"Sosai ma zan zo mana."
Chapter 26 · 0% Book details