← Book details Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 93

Sashe 45

Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel · about 6 min read

a hankali ta mike ta isa can gaban gado ta 蓷au Laptop saman bedside ta dawo in da nake ta zauna agefe na akasa in da nake zaune, kana ta kunnan Laptop 蓷in ta daddannan sannan ta aje a gabana.
hotuna da bidiyoyin kaddarori ne suka rika bayyana ciki, manya manyan gine gine gidaje masana'antu daga nan gida Nigeria har kasashen ketare,
ido na ware ina kallon tulin tarin dukiyar, da bansan ma'anar nuna min shi da take ba.
zuwa can ta saki dariya tare da rufe Laptop 蓷in tace
"Wannan ka蓷an ne daga cikin dukiyar Alhaji Tijjani Sabil wan da ayan zu yazamo mallakin Ahmad Tijjani Sabil, bayan tulin dukiyar da shi kansa Ahmad 蓷in ke da shi, HAMDAH."
takuma kiran suna na tana mai dubana da kyau sannan tace
"A rayuwar nan na yanzu baka da burin daya wuce kazamo abin kwatance aduk in da kake duk in da ka shiga arika nuna ka, kayi fintinkau cikin kawayen ka, misali kamar ke a yanzu da kika zamo abin fa蓷a,
na tabbata kina so kida 蓷a fin haka,
idan kuma kinso a yanzu zaki fi hakan cikin sauki zaki da蓷a mallakar dukiya mai tarin yawa, ki 蓷aukaku a duniya, cikin sauki idan kina da bukata a yanzu zaki iya zamowa haka."
shiru nayi ina sauraran ta da 蓷inbin mamaki cikin raina, taya za'ayi nasami wannan dukiyar datake ta misalta min shi 蓷innan? ai ko lokacin da nasami dukiya ban samu ta sauki ba sai da rayuwa ta dana 拼a拼ana takusa salwanta, amma kuma take cewa zan sami ninkin ba ninki kuma cikin sauki, to ni wace 蓷aukaka kuma 蓷aukakar da Allah yayi min yanzu ma na gode masa..
katse min tunani tayi da fa蓷in
"Kin shiga tunanin ta ya hakan zai kasance ko?."
sai ta saki wani dariya tare da cigaba da fa蓷in
"Cikin ruwan sanyi ma kuwa, idan kika ha蓷a kai dani zakiji da蓷i idan kuma kika bijire zaki fa蓷a cikin halaka, ina nufin rayuwar ki zata salwanta."
ido na waro da sauri na 蓷ago na dube ta,
wani irin hatsabibin murmushi ta sake kana ta girgiza kai tace
"Kwarai kuwa,
kin auri Ahmad bawai dun kina son sa ba sai dun son da shi yake miki, nasami labari sosai kan cewa bakya son shi kuma ina da tabbacin cewa har yau ba son na shi kike ba,
me zai hana muha蓷a karfi da karfe kibi ta wannan hanyar kici moriyar dukiya mai tarin yawa, ki kara kan naki, ki da蓷a zamowa abin kwatance a duk fa蓷in kasar nan da ketare baki 蓷aya."

Zuwa yanzu maganar nata yafara jefari cikin firgici da tsoro dan na rasa me take nufi dahar zata yi min barazana da salwanta rayuwa ta.
蓳ari jikina ya soma a raina nake fa蓷in
"Innalillahi'wa'inna'ilaihirraju'un,abin da nayi gudu shiyake kuma tunkaro ni."
maganar ta najiyo tana fa蓷in
"Za蓳i yarage naki idan kin so a yau zaki iya aiwatar da komai."
ta mike tsaye taje taja drower har ta dawo ta zauna in da ta tashi kaina na sunkuye, yayin da firgici mai tsanani ya shige ni, sai nanata kalmar
Innalillahi'wa'inna'ilaihirraji'un nake.
"Ungo kar蓳i rike wannan." da sauri na 蓷ago ina duban abin da take mika min 蓷in
wani kullin magani ne cikin laida, hannu na na 蓳ari na kar蓳a tare da kura masa ido.
tace "Wannan maganin shine hanya mafi sauki da zakibi ki mallaki dukiya mai yawa ki kara kan naki,
ki zuba wa Ahmad a cikin abinci ko sha, idan yaci zai kwanta jinya ba kada kiji tsoro dan ko
likitoci bazasu ta蓳a gane wani abu yaci ba, kuma baza'a ta蓳a gane ciwon me yake damin sa ba a haka zai tafi daga nan kuma zance ya kare, zamu raba dukiyar biyu ki 蓷auki rabi na 蓷au rabi,
tun rabar dana sami labarin auren ku na kasance cikin farin ciki dan na tabbatar zaki iya aiwatar wa tun da ba son shi kike ba."
wani irin 蓳ari hannuna da ilahirin jikina suka 蓷auka cikin tsananin mamaki tashin hankali na 蓷ago na dube ta murya na rawa nace
"Kashe shi za'ayi." wani irin kafurin dariya tayi tace
"Kwarai kuwa nasan aiwatar da hakan bazai baki wuya ba tun da bason shi kike ba, ko da ace kina son shin ma so 蓷in banza ku蓷i ai yafi miki shi, yana mutuwa kuma zaki sami wanda yafi shi."
gaba 蓷aya 茩wa茩walwa ta ya tsaya cak ya daina ai ki firgici da tashin hankali su suka dabaibaye ni,
ta ko ina 蓳ari yake a jiki na.
kisa nice zan kashe mutum da hannuna wai uwa ce ke son gusar da 蓷an ta anya ba mafarki nake ba?, da sauri na mussuke idanuna ina mai ware su a kanta maganar ta na natsinkayo a sama
"Kada ki 蓳ata min shiri yin hakan babban kuskure ne, na tabbatar miki rayuwar ki dana 拼a拼an ki zasu salwanta,
kiyi tunani ki dubi tulin tarin dukiyar nan ace suda蓷a zamowa mallakin ki ki zamo abin nuni da fa蓷a a duniya, ba pillow zaki danne kansa da shi ba ba kuma wuka zaki da蓳a masa aciki ba, wannan ka蓷ai zaki zuba masa cikin abinci daga nan shike nan arziki ya dawo naki."
hannuna mai maganin ta rike ta kalle ni tana dunkule min maganin cikin hannuna, cike da karfafa guiwa ta cigaba da fa蓷in
"Kada kiji tsoron komai ko ki tsaya tunani ki rika tuna tulin tarin dukiyar nan ki ai watar kada kiji komai babu wan da zai zarge ki dan babu ta in da za'ayi a gane, ku蓷i yafi komai a rayuwa."
maganin ta kar蓳a a hannuna ta蓷au jakata ta jefa shi ciki tarufe tana fa蓷in
"Ki kula kada a sami matsala faruwan hakan babban matsala ce ga rayuwar ki."
kai na girgiza da sauri, murmushi tayi zata kuma magana akayi sallama daga bakin kofa, zaman ta ta gyara da sauri ta蓷an matsa gefe,

Ahmad ne rike da su Naseem a hannun sa suka karaso suka zauna,
fuska ta fa蓷a蓷a da murmushi tadubi Ahmad tana fa蓷in
"Sannu Ahmadu numfashin Sabil an dawo."
yace "Eh Hajiya bar ka da gida."
tace "Yauwa Ahmad Allah yayi albarka ya tsare gaban ka da bayan ka."
"Amn amin." ya amsa yana mai murmushi. ya mike ya dube ni sannan yace
"Muje ko yau kinyi wa Hajiya wuni."
da sauri tace "A'a kam sai dai rabin wuni dai, tamayi kokari a hakan dan tafi wancan Rasheedat 蓷in mai isa da kafafa."
murmushi kawai yayi, yayi waje tare da 蓷aga kiran da ya shigo wayar sa yanzu.
jiki a sanyaye na mike, itama ta mike tare da 蓷aukar jakata ta mika min sannan ta dube ni da kyau tace
"Ki kula ki ai watar da komai ya tafi dai-dai kada a sami wata matsala, ni zan kula da komai daga baya, ki kawar da abin da bakya so ki kuma sami karin dukiya mai yawa, ki 蓷aukaka a duniya, kada kiji komai zan tsaya miki."
ta dafa kafa蓷a ta tana mai kuma jaddada min.
yau ma har kofar parlour ta yi min rakiya tana,
ina dai-dai zama ta cikin motar na sauke numfashi da karfi har sai da ya juyo ya kalle ni.
a hankali na maida baya na na jingina da jikin kujerar motar, gaba 蓷aya jiki na ya gama sanyi.
gefen da nake ya waigo ya dube ni kana ya mai da duban sa kan titi yace
"Madam ya dai?."
idanuna na lumshe batare da na amsa shi ba..
har muka isa gida idanuna a lumshe yake yana gyara parking najiyo Muryar sa daf da ni yana fa蓷in
"Ko na 蓷auke ki nashi da ke ne?, naga kamar kin gaji."
a hankali na bu蓷e idanuna na jiki a sanyaye kai hannu na bu蓷e marfin motar nafita..
Chapter 45 · 0% Book details