← Book details Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 93

Sashe 58

Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwance nake a kan dago na tasa 蓷an karamin ciki na gaba wan da yanzu watan sa hu蓷u kenan.
idan bama kasan da cikin ba, bazaka ce da wani halitta cikin cikina ba, dan bai wani fito sosai ba, bakamar irin cikin su Naseem lokacin da ya kai watanni hu蓷u ya fi sosai kamar wan da yafi watan nin sa ba.
Ahmad ne ya shigo 蓷auke da plt a hannunsa, perpesun kayan ciki ne ha蓷e da ganyen ogu da dafeffen kwai a gefe, wanda yasha kayan kamshi da na yaji sai tashi da kam shi yake,
ya dire plt 蓷in saman table kana ya hayo gadon ya zauna ya tankwashe kafafun sa a gaba na yashafo fuskata yace
"Kyakkyawa ta taso kici perperun gashi na 蓷ebo miki."
fuska na 蓳ata nace
"Ni na koshi ba 蓷azun nan ci ba, ni bana jin yunwa yanzu."
ido ya waro yace
"To ai ba sai kinji yunwa ba, bakiji abin da Dr yace ba kirika cin abinda zai kara miki jini da kuzari da lafiyar baby na ba ga perpesun can cikin tukunya ko kwata baki ciba, kuma yanzu nasa Zulai ta kuma girka miki gwaten wake da hanta."
ido na waro nace "Nayi yaya da shi sauran perpesun ma kaje ka basu su ci ni nagaji da ci, kullum-kullum kawai mutum yayi ta ci."
yace
"Dan Allah ki taimake ni kitashi ki ci,cin wa蓷an nan abubuwan fa sune samin lafiyar ki data baby na, so kike a sami wata matsala? dan Allah ki tashi ki ci kada yayi sanyi."
ya saka hannu ya 蓷ago ni, ya tallafo ni ya ware kafafun sa ya sani sakiyar cinyar sa, kana ya mika hannu ya 蓷au plt 蓷in yasaka shi gabana, ya 蓷ibo perpesun a cokali zai kai bakina.
kar蓳i cokalin nace
"Ni zan ci da kaina." yace "To ci
maza dan Allah ki cinye duka."
nace "To Allah ka蓷an zan ci dan bana jin yunwa."
yace "To ci dai."
a hankali nasoma ci, ganin na fara ci sai ya da蓷a gyara zaman sa da kyau, a sannu ya tura hannunsa cikin riga ta ya kife hannunsa kan ciki na, wani nannauyar ajiyar zuciya ya sauke a hankali yashiga shafa cikin.
bai fi cokali biyar na ciki ba nace nakoshi.
da sauri yace "Please kyakkyawa ta ki蓷an kara ka蓷an."
nace "Allah nifa na koshi."
duk yan da ya matsa kan na kara ko ka蓷an ne naki daya masa sai na sa masa kuka, ai da sauri ya rungume ni yashiga rarrashi na..

Washegari tun da sassafe ya 蓷aga ni da kyar na bu蓷e idanuna dan bacci ne fal a ciki,
yace "Tashi muje kiyi wanka mutafi asibiti yau zaki fara awu, dan likita yace cikin na cika wata hu蓷u yakamata ki fara yin awu kin ga yau Monday dai-dai kenan."
fuska na 蓳ata nace
"Ni bacci nake ji kabari ba yau ba."
da sauri yace "A'a ina, duk da dai baccin da awun duk suna da amfani amma dai muje a duba lafiyar baby in mun dawo sai ki cigaba da baccin kinju kyakkyawa ta."
ya karashe maganar da tsi
gar rarrashi.
kai na gya蓷a masa a hankali.
murmushin nan nasa mai narka zuciya ya sakar min kana ya sauke bakin sa kan goshi na ya manna min kiss,
idanuna na lumshi tare da kuma bu蓷e su, ya 蓷ago yana kallon fuska ta a hankali ya furta
"Ina son ki kyakkyawa ta."
idanuna na kuma lumshe wa a lokaci guda na bu蓷e, tabbas na gama yarda da son da yake yimin a koda yaushe ina hango sona acikin kwayar idanunsa.
idanunsa cikin nawa cikin sanyin murya yace
"Yaushe zaki fa蓷a min kema kina so na da bakin ki?."
kasa nayi da nawa idon batare da nace komai ba.
murmushi yayi yace "Ko a iya haka ma na gode."
duban sa nayi da fuskar tambaya jin ya fa蓷in haka.
murmushi ya kuma tare da 蓷aga min gira kana yace
"A fa蓷a min 蓷in ne dai ajin ya hana amma gashi nan ina hango shi."
yasa yatsar sa karkashin idanuna.
kai na nayi saurin kawar wa tare da yunkurin mike wa, 拼ar karamar dariya yayi ya taimaka min na mike tsaye yayin da ya soma zolaya ta.
"Ajin nan ya ishe ni haka a ajiye shi a gefe a fito fili a fa蓷a min ana sona, tun kafin ajin ya tsinke dan wata jiya ta tare ni a hanya tace tana sona, nace ta bari tukun da wan da nake so idan bata ce tana sona ba zan zo na amshi soyayyar ta."
baki na ta蓳e dan yanzu na gama karantar kalar zolayar sa nace
"Ayya ai da ka amince mata kawai."
da sauri ya leko fuska ta yace
"To ai ke nake jira 拼ammata idan baki fa蓷an kina sona ba sai na koma gurin ta."
"Yi maza kaje ka sanar mata kada ka maka anan."
nafa蓷a ina kokarin wuce sa, da sauri ya ruko ni yace
"Bari dai na 蓷an kara jira tukun."
ya janyo hannuna muka shiga bayi.
bathtub ya cika da ruwa mai 蓷umi,
kana ya tu蓳e min kayan jikina, na shige ciki na zauna ina mai jin da蓷in ruwan, na lumahe idanuna.
da sauri na bu蓷e idanuna jin motsin sa cikin ruwan sai ganin sa nayi shima a tu蓳e,
ya 蓷au sosa da sabula yashiga wanke ni shima yana wanke jikin sa a haka akayi wanka,
kana ya ruko ni muka fito bedroom,
koda nazo sa kaya hana ni yayi sai da yagama sumbatar ciki na kafin ya saka min da kan sa.
muna gama shiri muka fito muka dadda an gama wa su Naseem shirin School.
a saman dinning duk muka yada zangon mu, sai da ya ha蓷a musu abincin da duk sukace suna so kafin ya juyo kai na.
perpesun naman zabbi ya zuba min ha蓷e da tea mai kauri yana kokarin zubo wani abun nace masa
ya isa wannan 蓷in ma ba iya cenyewa zan yi ba. ciki na ya shafo
yace "Yanzu fa zaki fara kamata yayi ki fara da mai yawa."
duban su Naseem yayi yakamo kumatun su yace
"Kanin ku yakusa isowa Yaya Naseem da Aunty Nasmah."
washe baki sukayi cike da jin da蓷i Naseem yace
"Daddy ina kanin?."
ciki na ya shafa yace "Ya na nan yakusa fito wa."
da sauri Nasmah ta mike tazo kusa da ni tana kokarin jan riga ta sama.
hannunta na bige nace
"Ke meye haka?."
tace "Mommy danga kanin ne fa."
fuska na 蓳ata nace "Ka dani ko."
dariya yayi sosai kana ya蓷an sakaita dariyar, ya dafa kanta yace
"Zaki gan shi?." kai ta gya蓷a tana washe baki.
yace "To ba ri ki ganshi."
juya kujerar da nake yayi yadurkusa kana ya saka hannu yana kokarin jan rigata sama, nayi saurin rike hannunsa nace
"Me ye haka?." juya hannun nawa yayi yarike cikin nasa kana yajan je rigar da 蓷aya hannunsa, yace
"Kibar yara suga 蓷an uwan su."
tafin hannunsa ya kife kan cikin yana 蓷an shafawa yace
"Nasmah zo ki gani ga kaninku a nan yaron yana nan a nan."
dariya sukayi har suna rige-rigen
ta蓳a cikin.
Naseem yace
"Daddy ni ban ganci ba."
yace "Yana cikin ciki yakusa fita ku ganshi."
sallen murna suka yi suna fa蓷in
"Ye damuga yaro, Mommy data samo mana yaro."
kafa na shiga bubbugawa a kasa nace
"Kuma na fasa cikin abincin."
da sauri ya saki rigar yace
"Yi hakuri kyakkyawa ta ci mu tafi o."
sai da yayi ta lallami na kafin na soma ci.
hannu ya saka muka ci tare muna ci yana karawa da dabara yayin da yake ta jana da wasa har naci da yawa sosai.
bayan mun gama muka fito waje in da Talatu ke biye da mu rike da school bag 蓷in su.
ko da akazo shiga mota dirjewa yaran sukayi suka ce sam moton Daddy'n su zasu shiga, fuska na 蓷aure nayi musu tsawa nace
"Maza ku shige kusha mota kutafi so kuke kuyi latti."
da sauri yace
"A'a a'a kyale su kushiga muje, Talatu sa musu jakar su cikin mota."
da sauri tace to.
ya bu蓷e musu motar suka shiga, Talatu saka musu jakar su cikin motar,
kana ya bu蓷e min nima na shiga, ya zaga gefen direba ya shiga ya ja motar, mai gadi ya bu蓷e get muka fice a gidan..
sai da yafara bi ta makarantar su da kansa ya sauka ya ruko hannunsu ya shiga da su cikin makarantar kafin ya fito muka nufi asibiti.

Muna shiga cikin asibitin batare da 蓳ata lokaci ba aka gama kimsa mana komai,
koda nazo shiga 蓷akin awu tare da shi muka shiga, yana tsaye yana kallon komai, idan yaga nurse 蓷in ta蓷an danna cikin sai yace wai tayi a hankali kada a sami matsala, a haka a ka gama muka fito muka nufo gida.

Tun daga lokacin idan wata ta zagayo lokacin zuwa awu yayi da shi muke zuwa kuma yana tsaye za'ayi komai....

Haka rayuwa yaci gaba da tafiya,
sosai Ahmad ke kula da ni baya kaunar yaga wani damuwa ko 蓳acin rai tare da ni, bazai ta蓳a samin sukuni ba har sai yaga ya gusar min da damuwa ya sanyani farin ciki....
a yanzu cikina watan sa 7 yafito 蓷as da shi, haka zai tasani gaba ya tu蓳e min riga yayi ta kallon cikin, yana ganin in da yake motsa wa, yayi ta sumbatar sa, idan nace ni na gaji ya kyale ni.
sai yace ai ba da ni yake ba da babyn sa yake, wai yana mika masa gaisuwa....
Chapter 58 · 0% Book details