← Book details Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 83 OF 93

Sashe 83

Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

After 5 hr.
Sai a lokacin na farka daga doguwar sumar dana tafi,
a hankali nashiga bu蓷e idananuna dasuka yi min mugun nauyi, maganar Ummi na najiyo a kusa da ni, da sauri na yunkura zan mike, Ummi tayi saurin rike ni tana fa蓷in
"Yi a hankali HAMDAH."
nace "Ummi ni tashi zanyi." Mamie dake zaune a gefe da waya a kunnen ta tana fa蓷in
"Mun iso sai dai har yanzu bata farfa蓷o ba."
sai kuma tayi saurin kashe wayar ta mike tazo ta rike ni tana fa蓷in "Zaki iya tashi?."
kai na gya蓷a, tace "To tashi." suka taimaka min na mike zaune,
kokarin durowa a gadon nake Ummi tace
"Da kata HAMDAH ina zaki ko fisari kike ji?."
kuka na fashe da shi nace
"Ni gun Ahmad zan je." hawaye Ummi ta share Mamie tace "Kiyi hakuri HAMDAH, ki tsaya ki da蓷a samin sauki tukun."
kai na shiga girgiza wa ina fa蓷in "A'a ni gurin sa zanje ni dai zanje."
duk yan da suka kai da lalla蓳i na fir naji nace nidai gurin sa zani, haka suka hakura suka kyale ni.
na sauko a gadon da gudu nafita a room 蓷in, nashiga waige-waige room 蓷in da aka kwantar da Ahmad na nufa a guje na tura kofar na shiga, turus nayi cikin 蓷akin ganin babu kowa ciki. sai kuma na juya a guje tare da kuka sakin kuka nayi,
su Ummi da suka biyo baya na suka ruko ni.
Mamie ta rike ni gam tana fa蓷in
"Ki nutsu HAMDAH." nace "Ni gida zan tafi an mai da Ahmad gida nidai gida zanje."
Su Mama Inna Wuro Ummi Mamie duk kanin su hawaye suke cike da matukar tausaya min, Ahmad karami na goye a bayan Mama yana bacci sai sauke ajiyar zuciya yake.
Mamie tace "To muje gidan...
ko da muka iso gida direba na dai-dai ta parking na fito da gudu nayo cikin side 蓷i na,tun daga parlour'n kasa nake fa蓷in
"My kana ina My kadawo gida ko."
har na haura sama ban fasa kiran sa ba, na shige bedroom ina ta waige-waige.
Ummi data biyo baya na da sauri ta ruko ni tana fa蓷in
"HAMDAH kidawo cikin hayyacin ki, ki nutsu kiji ni, Ahmad ya rasu mutuwa kuma ba karya bace, yanzu addu'a ka蓷ai yake bukata shi da ma yayi kyakkyawar tafiya ki nutsu ki sawa zuciyar ki salama ki fauwalawa Allah komai, hakika akwai ciwo amma ki daure, ki daure jin 拼ata 拼ar albarka Allah ya baki ikon cin jarabawar ki."
"Ummi yanzu shima ya tafi kenan bazan sake ganin sa ba kenan Kamar Inna."
kwai Ummi ta shiga girgiza wa tana kwalla.
rungume Ummi nayi tare da sakin wani irin kuka, bata hanani yin kukan ba sai bubbuga bayana da take itama tana kwalla.
su Mama suka janye ni a jikin ta suka zaunar dani bakin gado na zube a gadon ina mai ci gaba da rusar kukan..

Basu hanani kukan ba sai da nayi sosai kafin suka fara rarrashi na, da ban baki har nayi shiru,sukayi ta bani baki ha蓷e da nasihohi nidai ina nan zaune amma hankali na baya gurin, nan Ummi suke shaida min tare suka zo da su Abbu suna gidan Ahmad can in da ake zaman makoki...

Bayan kwana uku..........!

Mommyn Twin ce
8/19/22, 11:01 - Ummi Tandama馃槆: 37

Haka zan rungume Ahmad karami nata kuka cike da tausayin sa da kuma tausayin kaina,sai Mamie ko Ummi sun kar蓳e sa, tun ranar da Ahmad ya rasu Ahmad karami yaki shan nono,
Ummi tace a 蓷aga shi kawai a nonon tun da ya makai na yaye...
A ko da yaushe su Ummi suna tare da ni basa ta蓳a barina na zauna ni ka蓷ai,yau su Aunty Rafee'ta suka zo ita da Aunty Jaleela da Ya Masa'ud da Goggo Hauwa,
da yamma suka 蓷unguma suka je gidan Ahmad domin yi wa 拼an uwan sa da Aunty Rasheedat ta'aziyya har da su Mamie.
kamar yadda suma 拼an uwan nasa suke zuwa har dama 拼an uwan Aunty Rasheedat domin yimin ta'aziyya.
Abba Bashir da mahaifiyar Aunty Rasheedat su tun ranar rasuwar ma suka zo nan..
tare da su Abbu su Ummi suka dawo dan yau an gama zaman makoki...
ranar bakwai da safe Alhaji Bashir da mahaifiyar Aunty Rasheedat da ita Aunty Rasheedat 蓷in da wasu daga cijin dangin su, da shaidu da kuma laiyoyi, da manyan malamai suka zo.
duk kanin mu muka hallara a parlour'n kasa.
Aunty Rasheedat na rungume da Ahmad karami a jikin ta, ta kura masa ido sai kawai ta fashe da kuka, ni ma kukan na fashe da shi dan nasan abun da nake ji a raina itama shi take ji.
rarrashin mu akatayi tare da yi mana nasiha har sai da zuciyoyin mu suka sami salama, kana a ka soma gudanar da abin da ya taramu wato rabon gado.
duk kanin dukiyar Ahmad da kaddarorin sa na nan gida Nigeria da kuma na kasashen waje da wan da aka kashe shi domin sa wan da ya damkawa manajan banki, duk aka ha蓷o kansu.
batare da 蓳ata lokaci ba malamai suka fara gudanar da rabon gado kamar yadda shariya ya shar'anta, duk kannnin mu uku a ka dan kawa kowa abin da ya gada ni Aunty Rasheedat da kuma Ahmad karami, nayi mamakin tulin dukiya da kandarorin da Ahmad karami ya gada,
daga mahaifinsa nakuma yi mamakin tulin taren dukiya irin na Ahmad.

Washegari su Abba Abbu Mamie Aunty Rafee'at Aunty Jaleela Ya Masa'ud suka koma Bauchi, yarage saura Ummi na,
Ummi tana iya bakin kokarin ta wajen ganin ta gusar min da damuwa ta dan ko nan da can bata matsawa koda yaushe tana tare da ni.
yanzu Mama ma ta dawo side 蓷ina ita ma muna tare..
lokacin da mukayi arba'in Ummi tace zata koma gida,
washegari bayan ta gama shiri ta je sashin su Bappa bayan sun gaisa take sanar masa yau insha Allah zata koma sannan ta 蓷aura da fa蓷in
"Bappa ina so na tafi da HAMDAH tadanje tayi kwana biyu."
Bappa yace
"Kwarai kuwa kinyi tunani me kyau tafiya da ita 蓷in shiyafi saboda acan zata zauna cikin yan'uwanta da iyayenta tunaninta zai ragu akan zamanta anan 蓷in, Allah yatsare yakiyaye hanya."
Ummi ta amsa da Amin...
ina zaune dasu Naseem da Nasmah suna gefena sai rikici suke min kaman kullum Naseem daya ware baki zaiyi kuka yace "
Mommy ina Daddy kince zai dawo."
kwalla nashare nace "Naseem nace muku daddy zai dawo daddy yayi tafiya zai dawo." Nasmah tace "Mommy nikam kikaini gun Daddy kinji Mommy."
kaina girgiza yayin da hawaye yake zuba a idona inajin yadda yaran suke bori Naseem yasaya yana fadin nikam ki kiramin Daddy, yami kamin wayata, yana ci gaba da fa蓷in na kira masa Daddy.
kuka nafashe dashi na rungume yaran ajikina ina mai matuqar missing na Ahmad.
Ummi ce tashigo ganin ina kuka tayi saurin isowa tana fa蓷in
"HAMDAH lafiya?." kaina girgiza ina fadin "Ummi Ahmad yatafi bazan iya qiranshi a waya ba Ahmad yatafi kenan bazai dawo ba, bazan sake ganin sa ba, suma so suke su gansa."
kuka sosai nafashe dashi Ummi ta rungume ni tana rarrashi na, kana tace na tashi naha蓷a kayana zamu tafi Bauchi tare, baza ta iya tafiya ta barni cikin halin da nake cikin nan ba.
babu musu namiqe danni ma nasan tafiyar zai fi min bazan iya jure Ummi tatafi tabarni Anan ba.
ita ta tai makamin mukashirya kayanmu tasa su Talatu suka fita dasu,
gabadaya yan gidan suka rako mu parking lot,
nace Mama ta komo part 蓷ina tun da ba kowa ciki kafin mu dawo,
suna tsaye har
muka shiga mota, muna 蓷agawa juna hannu muka fice a gidan.
muka dauki Hanyar Bauchi...
koda muka iso Bauchi naji da蓷in ganina acikin yan'uwana domin kota'ina najuya sune basu kaunar ganin wata damuwa tattare da ni,
kowa yana iya bakin kokarin sa wajen ganin farin ciki ya samu gare ni.
Su Aunty Rafee'at da Aunty Jaleela kusan kullum sai sun zo gida sai dare su koma, Ya Mas'ud baya motsawa konan da can kullum muna tare idan ya dawo daga gurin ai kin sa, haka zai zauna muta hira.
yan'uwana suna matuqar qoqari wajen ganin sun sani farin ciki sun kuma 蓷ebe min kewa...
A hankali na fara sake wa, da muwar dake dankare cikin raina yana ta washe wa, yanzu kam alhmdllh na sake hankali na kuma nata kan da蓷a kwanciya..
Chapter 83 · 0% Book details