← Book details Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 93

Sashe 72

Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Kamar yadda Ahmad ya fa蓷a bayan kwana uku motocin mu suka haura hanyan zuwa Bauchin Yakubu.
motan mu daban ni da Ahmad da su Naseem duk muna baya in da direban sa ke janmu.
motan su Bappa daban, Bappa na gaba shida direba Inna Wuro da Mama da Faty suna baya.
har da su Uncle Mahmoud motan su daban shi yake jan motar sa da kansa shi da matarsa da 拼a拼an su ne ciki dan shima yace ba za'a barsu a baya ba.
sai motar security motar su guda, a hanya muka ha蓷u da su na fahimci biyo mu suke.
a jere motocin suke tafiya, motan su Uncle Mahmoud ne a gaba na su Bappa na biye da su in da moton security ne ke biye da mu......
da misalin karfe uku muka iso cikin garin Bauchi,
wani irin lumshe idanuna nayi tare da kuma hu蓷e wa a cikin garina mahaifata,
na shaki iskar dake ka蓷a wa ina mai farin ciki da jin da蓷in gani na cikin garin.
murmushi Ahmad yayi tare da jan kumatu na yace
"Yarinya tana murna tazo kauyen su."
dariya nayi nace "Nan 蓷in ne kauyen me Abuja yafi shi da shi."
yace "Lalala birnin tarayya ne fa babu ha蓷i ai."
nace "Ba wanin nan."
yace "To dai nuna mana hanya ina zamu karmuje mu 蓳ata."
dariya nayi tare da soma yi masa kwatance ya kira Uncle Mahmoud ya ha蓷a mu da shi narika yi masa kwatance har muka shigo unguwar mu.
a bakin get Uncle Mahmood yayi hon mai gadi ya bu蓷e ya shiga muka bisa a bayan sa, a farfajiyar gidan motocin mu suka faka.
numfashi mai karfi na sauke gani na a cikin gidan mu.
su Aunty Rafee'at ne da su Mamie da Goggo Hauwa suka fito daga sashin Mamie da sauri suka nufo gurin motocin,
da saauri na malle marfin motar na fito da sauri muka rungume juna cikin matukar farin cikin ganin junan mu,
su Abbu suka iso gurin suna yi wa su Bappa sannu da hanya, kana a ka 蓷unguma aka shiga side 蓷in Mamie, security kuma aka shinfi蓷a musu babban tabarma a gindin bishiyar anbulera dake gefe da tsakar gidan.
muna zazzaune a parlour sai gaisawa ake, tuni Mamie ta sa su Aunty Rafee'at suka cike mu da kayan ci da sha wan da aka tanadar domin mu, aka 蓷ibi wasu aka kaiwa security.
niko ina tsakiyar su Aunty Rafee'at da Aunty Jaleela da Ya Masa'ud, da 拼an kanne na Nusaiba da Fauzan.
Naseem da Nasmah suna like a jikin Ya Masa'ud wai har sun gane shi kenan sai surutu suke zuba masa, wannan yace Uncle kaza wannan yace Uncle.
Ahmad karami kuwa yana hannun Mamie tana yi masa wasa yana dariya.
ana ta hira cike da jin da蓷i da nisha蓷i.
nan suka yi ta yiwa Mama mai awara godiya da irin kokarin da tayi a kaina...

Acan gidan SALEEM kuwa labarin zuwan su HAMDAH ne ya iske Na'ima,
a bujajan ta taso dan gane wa idon ta karya ne ko gaskiya, dan yau tayiwa boka alkawarin kawo masa cikon ku蓷in sa, dan wan da suka shirya zai sace Ameer baya nan shine aminiyar ta Raliya ta bata aron cikiton ku蓷in da zata bawa boka, idan aka kar蓳i ku蓷in fansar Ameer ta biya ta,
shikuma yayi mata alkawarin yau 蓷annan da daddare zai tura aljanu su kashe HAMDAH...

Sallama muka jiyo daga sama, duk kanin mu muka mai da hankali bakin kofa,
kamar an jefo ta haka ta fa蓷o cikin parlour'n, wani irin kallon-kallo muke yi da Na'ima da tayi mutuwar tsaye bakin kofa.
dogon tsaki Aunty Rafee'at ta ja kana tace
"HAMDAH kalli wannan hoton ki gani."
tayi maganar tana nuna min hotunan mu da ta sa Fauzan ya 蓷ibo a side 蓷in Ummi.
dariya nayi ganin hoton tun ina Dass wani lokaci Inna ta bani ku蓷i naje na 蓷au hoton,
kai na girgiza tare da fa蓷in
"Allah sarki Inna ta."
Ahmad da hankalin sa ke kanmu yana binmu kallon cike da sha'awa da burge wa ganin yan da muke da junan mu yace
"Madam muga hoton."
蓳oye sa nayi a baya na ina dariya, Aunty Jaleela ne ta fizge hoton tana fa蓷in
"Bashi yaga munin kawai." ta mika masa hoton.
nace "Allah Aunty Jaleela ko a da ma na fiki kyau."
Ya Masa'ud yace "Bare kuma yanzu har girma kin fita 拼ar gidan Inna."
dariya na fashe da shi nace "Yau wa Ya Masa'ud fa蓷a mata dai."
Aunty Rafee'at tace
"Oh Masa'ud zaka fara ha蓷in naka ko."
tayi maganar tana dariya cike da kewar fa蓷ar mu da Aunty Jaleela da muka saba.
Aunty Jaleela kuwa hararar sa tayi tace "Ni sa'ar ka ce Masa'ud?."
Ya Masa'ud yace
"Aunty Rafee'at matsa na mari bakin yarin yar nan."
dariya muka yi dukan mu har da Ahmad da hankalin sa ke kanmu,
yana kallon hoton yana dariya, idan muka ha蓷a ido da shi sai ya nuna min hoton yayi dariya,
baki na rika murgu蓷a masa nima ina dariyar...
Na'ima tana tsaye kamar wacce a ka kafata idanunta a kaina, kamar a mafarki haka take ganin komao.
Ummi ce ta dube ta tace
"Shigo mana Na'ima ya kika tsaya a gurin."
ta janyo 蓷an da ke rike a hannunta suka karaso cikin parlour'n hankali a mugun hargitse....
Chapter 72 · 0% Book details