← Book details Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 93

Sashe 69

Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bappa ya soma da addu'a bayan addu'a ya 蓷aura da fa蓷in
"Alhamdulillah muna godiya wa tabakara ma蓷aukaki mabuwayi mai izza, wan da ya nuna mana wannan rana, muna niman tsari da sharrin masu sharri Allah ya ka蓷e mana fitina, muna godiya wa Allah da ya nuna mana wannan rana, Allah ya da蓷a ka蓷e mana fitina duniya da kiyama."
kowa ya amsa da amin amin,
Bappa ya gyara zama tare da ci gaba da fa蓷in
"Abubuwa sun faru da dama bama fatan hakan ta kuma faruwa Allah ya ka蓷e fitina, ya iyar mana abun da baza mu iya ba, Allah yayi mana maganin makiya da masu hassada kamar yadda ya nuna musu karshen sharrin su,
hakika addu'a makarin Mumini ne, a na son musulmi a duk in da yake a duk halin da yake ya kasan ce mai ruko da addu'a, domin addu'a takwabi ne mai kaifi ya kan tsare fitina da sharri da kaifin sa, hakika wannan abu da ya faru ya nuna 蓷an dakacin addu'a ka蓷an duk da Allah yayi taimako an farga da wuri, Allah ya da 蓷a tsare mu ya yi mana katangar karfe da azzalumai."
Abbu ya jinjina kai cike da gamsuwa yace "Amin ya rabbil izzati, hakika addu'a takwabi ne mai kaifi hakika lamarinnan ya jijjiga mu ba ka蓷an ba duk da bakin mu baya iya
furta wa amma zuciyoyin mu tana kuna."
ya 蓷an sakai ta maganar tare da duba na kana yaci gaba da fa蓷in
"Kiyi hakuri HAMDAH duk da bamu kuma yunkurin niman ki ba amma zuciyoyin mu suna tare da ke a ko da yaushe."
kai Bappa ya jinjina dan ya san cewa ai kin sihiri kenan shi yasa ake so a koda yaushe mutum ya zamana yana cikin sarki da addu'a idan aka jefe ka da shi bazai yi wani tasiri a tattare da kai ba...
Abbu yace "Muna mai ci gaba da baki hakuri hakika mun ai kata rashin kyautawa wa rayuwar ki, a matsayin mu na iyayen ki da kike da hakki a kanmu da muka gaza sauke shi na wasu shekaru mu na ruko da ki yafe mana."
da sauri na shiga girgiza kai yayin da hawaye ke zuba a ido na
kwalla na share nace "Abbu bakuyi min komai ba, Abbu ka rokar min Abba ya yafe min dan naga kamar har yanzu bai yafe min ba amma wlh ni ban ta蓳a ai kata zina ba."
wani kuka ne ya tsu蓳uce min na fashe da kukan, Aunty Rafee'at ta rungume ni itama ta fashe da kuka.
cikin matu茩ar nadama Abba yake fa蓷in
"Ki gafarce ni HAMDAH tsananin kunyar ki ce ta hanani iya furta komai, tabbas nayi danasanin yanke hukunci cikin fushi, ki gafarce ni ki gafarce ni HAMDAH ina mai da na sanin yanke hukunci cikin fushi,
dana kore ki HAMDAH ina kika shiga ina kika shiga HAMDAH nayi da na sani nayi na dama HAMDAH ina kika je wani rayuwa kika yi?."
Abba yayi maganar cikin nuna nadama sosai kamar zai zubda kwalla.
in da yake na rarrafo tare da rike hannunsa gam kana a hankali nashiga basu labarin abun da ya faru, tun ranar da na sa kafa na bar gida da
rayuwar da na fara fuskanta,
da rayuwar da mukayi cikin daji ni da su Naseem da,
irin gwagwarmayar da na sha a rayuwa har na kai matsayin da na ke a yanzu.
tun da na fara bada labarin
gaba 蓷aya parlour'n ya kacame da koke-koke su Aunty Rafee'at har da jan shassheka, Ummi Mamie gaba 蓷ayan su kuka suke wei-wei kamar kananun yara,
Abba Abbu Bappa Ahmad duk kanin su sai sharar kwalla suke.
Abba yana sharan kwalla yana fa蓷in na yafe masa,
kai na shiga girgiza wa
nace "Baka yi min komai ba Abba."
Mamie tana kuka ta rungume su Naseem da tun 蓷azu take jin wani yanayi a kansu a kasan ranta take fa蓷in a she dai jinin ta ne su shiyasa tun da ta sanya idanunta kan su take jin su a cikin jikin ta.

su Abbu suka shiga yiwa Bappa godiya da irin kokari da jajirce wa kan lamari na da yayi yake kuma kan yi shi da matar sa wato Inna Wuro.
Bappa yace ai yiwa kaine, da 蓷a da dukiya bana mutum 蓷aya bane kuma ba'a yi musu keta.
sun yaba kwarai da gaske da irin kokarin da Mama mai awara ta yi a kaina suka kuma 蓷au alkawarin niman ta suyi mata godiya.
Ahmad ma godiya suka yi ta masa suka kuma yi jinjina ga Rasheedat matar da ba kasafai ake samun irin su a duniyar mu ba....

A 蓷aya side 蓷in da babu kowa ciki wan da yanzu su Talatu suke kwana ciki, nasa su Talatu suka fita suka koma side 蓷in su Inna Wuro suka shiga 蓷aya daga cikin 蓷akunan side 蓷in wan da ba kowa ciki,
wannan side 蓷in kuma nayi wa su Abbu da Abba Ya Masa'ud Fauzan masauki ciki.
蓷aya daga cikin
蓷akunan kasa kuma aka shigar wa Mamie kayan ta ciki, 蓷aya 蓷akin kuma Aunty Jaleela da Aunty Rafee'at da Nusaiba.
a ranar raba dare mukayi muna hirar bayan rabo da ahlina abu mafi soyuwa a rayuwa ta, Ahmad kuwa gidan sa ya tafi yace ya barni na gana da 拼an uwa na, bayan ya gama zolaya ta wai na share shi na nuna masa wariya...
kwanan su Abbu uku suka soma shirin komawa gida bayan na kaisu na nuna musu duk kanin kadarori na da suke cikin garinnan,
sauran na wasu gararruwan kuma a computer na nuna musu..
ranar da suka cika kwana biyar suka juyo Bauchi, amma banda Ummi dan ta ce ita tana nan sai ta yimin zaman arba'in tukun.
Abba ko da wasa bai yi yunkurin hana ta ba, sai dai ma karfafawa zaman nata da yayi, yace ta zauna tayi min wankan arba'in kamar yadda ake yiwa mai haihuwar fari dan na cancanci haka, duk da na sami ingantaccen kulawa gun Mama mai awara a haihuwa ta ta farko wan da ya kamata ace uwata ce ta bani wannan kulawar,
to amma guri bai kure ba, ta zauna nakuma kara samu agurin mahaifiya ta...
Ahmad yayi musu goma na arziki dan mota guda ce ta raka su da kayan tsaraba, bayan wan da nima nayi musu..
lokacin da suka iso gida Masa'ud ya shiga 蓷akin sa, yayi matukar mamaki ha蓷e da razana ganin SALEEM cikin 蓷akin a kwance ya dukunkune cikin bargo sai rawar sanyi yayi, lokaci zuwa lokaci kuma sai yayi wasu tagwayen tari ya dafe kirjin sa da karfi yana matse idanunsa.
a bin da ya da蓷a bashi mamaki shine kayan jikin sa, kayan da yazo da shi gidan ranar da zasu tafi Abuja gurin HAMDAH, "Kenan tun ranar yana 蓷akin nan?."
Masa'ud yayi maganar a ransa, da sauri ya karaso bakin gadon yana fa蓷in
"Subhanalla Ya SALEEM baka da lafiya ne?."
da ido kawai ya bishi barate da yayi magana ba.
ganin yan da ya kuma rumtse idanunsa yana da蓷a damke kirjinsa,
da sauri Masa'ud ya fito dan yaje ya sanar wa Mamie halin da SALEEM 蓷in yake ciki.
a sakiyar gidan ya ha蓷u da su Abbu da alama masallaci zasu tafi,
da sauri ya karaso in da suke yace
"Abbu Ya SALEEM bashi da lafiya yana kwance a 蓷aki na."
da sauri Abba yace "Subhanalla me ya same shi?."
ya juya da sauri ya nufi 蓷akin nasa Masa'ud ya rufa masa baya.
Abbu kam tsayuwa yayi ya蓷an yi dimm kana ya girgiza kai yawucw masallaci abin sa..
Abba na shiga 蓷akin ganin halin da yake ciki yashiga tambayar sa abin da ke damun sa,
ba wani kwakkwaran amsa ya samu a gurin sa ba dan tun da ya tambaye sa, me ke damun sa ya nuna masa kirjin sa bai kuma cewa komai ba duk tambayar da yake masa.
Abba ya 蓷aga waya ya kira Dr Farooq yace ya zo yanzu.
batare da 蓳ata lokaci ba Dr Farooq ya iso.
bayan sudduba shi da yayi ya rubuta masa magani, Abba ya bawa Masa'ud ku蓷i yaje ya siyo maganin ya kawo masa....
Chapter 69 · 0% Book details