← Book details Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 93

Sashe 37

Hamdah Part 4 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bana fita kullum ina 蓷aki in nafita kuwa to iyakata parlour'n sama, kamar yanda Hajiya Lubabatu tace bazan fita ko nan da can ba har sai ta gama aikin ta.
shiyasa ma na sami sa'ida daga gun wannan 蓷an anacen dan ko yazo iyakar sa parlour'n kasa yakaraci zaman sa yatafi dan bana sauka.
ana saura kwana uku bikin ranar tun da safe Hajiya Rahama da kawayen ta suka zo, Aunty Nusaiba matar Uncle Mahmoud itama da wasu kawayen ta sukazo, su Inna Wuro da Faty duk muna tare da su a side 蓷ina,
abin ka da taro ko babu yawane sai kaji hayaniyar nan ai ko parlour'n sama da kasa duk ya dauki hayaniyar jama'a.
wasuyan motoci guda biyar suka shigo gidan masu 蓷auke da tambarin sunan Company'n Ahmad Sabil.
duk kanin su shake suke tam-tam da kaya.
shigar su ke da wuya kira ta shigo wayata, koda na duba mai kiran ganin bakuwar lamba ce, kamar bazan daga ba sai da kiran takusa yanke wa kafin na 蓷aga da sallama, daga cikin wayar numfashi naji an sauke kana daga bisani a ka soma magana
"Kyakkyawa ta barka da safiya inad fata kina cikin koshin lafiya ke da yarana gaba 蓷aya."
Shiru nayi batare da na amsa shiba sai murgu蓷a bakin da nayi kamar yana kallo na. yacigaba da fa蓷in
"Ga ba'i a waje suna niman izinin shiga."
kashe wayar nayi ina kunkuni kasa-kasa "To ina ruwa da an hana ba'in shiga ne ko kuma wani sabon sai da hali ne."
Aunty Nusaiba dake kusa da ni tafube ni tana fa蓷in
"Wasu ba'i kuma?." baki na turo gaba nace "Wai wannan Ahmad 蓷in ne wai wani wai ga ba'i a waje ko da an hana su shiga ne da zai wani kira yana fa蓷a wa mitane."
tace "A'a kodai motocin da yanzu naji shigar sun nan ne naga mutane tsaye a jikin motar wata kila sune ba'in to ace su shigo mana."
Faty tashiga kwallawa kira Faty dake 蓷akin su Naseem tafito parlour da sauri tace
"Yi sauri kije kicewa mutanen da suke wajen nan su shigo sai ki sauke su a parlour'n kasa."
tace To,
jim ka蓷an ta dawo tace sun shigo suna parlour, Aunty Nusaiba ta sauka taje ta same su.
bajimawa ta dawo tace min
"Masu ai ki ne wai Ahmad Sabil ne ya turo su wai zasu fita da kayan cikin side 蓷in nan su shigo da wasu."
kafin nace wani abu Hajiya Rahama tace
"To bismilla su fara mana, sai su fara daga kasan idan suka gama sai a koma kasan a basu guri su gyara nan 蓷in."
tace "To haka ko za'ayi." ta juya ta koma domin sanar musu.
a raina nake fa蓷in
"Kamar wani an sashi ni shishshigi ne bana so."

Batare da 蓳ata lokaci ba ma'aikatan da suka kai wajen rai goma dukan su maza ne suka fara gudanar da ai kin su,
kan kace me sun gama kwashe kayan cikin parlour'n kasa, kama daga kujerun cikin parlour'n, bed and bedside drow dressing mirror wardrobe dake cikin bedrooms 蓷in parlour'n, zuwa kayan kitchen and dinning.
kaf sukayi waje dasu suka jibge su cikin 蓷aya side 蓷in cikin gidan da bakowa ciki.
nan suka rinka shiga da kayan da suka zo dasu a mota suna shirya komai yan da ya kamata.
zuwa karfe 1 sun kammala komai sun shirya komai a inda ya kamata.
nan suka bukaci haurawa sama domin cigaba da aikinsu, muka dawo kasan muka basu guri.
lokacin dana sauko kasa sai nazamo 拼ar kallo tamkar ba parlour na dana sani ba abun ba'a cewa komai tsaruwar sa ya wuci misali, kowa sai tabawa da sam barka yake....

Sai wajen yamma suka gama kammala komai sukayi mana sallama suka tafi.
abin kamar karya nake ganin shi sai da蓷a zamowa gaske yake,ana gobe 蓷aura aure Ahmad yaki rani lokacin ana yimin lalle, naki 蓷agawa sai da yayi min missed call biyar kafin na 蓷aga, yace
"Madam gani na shigo fito muje asibiti a bincika miki lafiya ta."
"Meye damuwa ta da lafiyar ka."
nafa蓷a tare da kashe wayar.
ina kallon wani kiran nasa na kuma shiga haka naki 蓷agawa, ga haushin lallen da aka bi aka dame ni da shi nifa in da anbi tanawa da duk wa蓷an nan fidda ficen da an barsu.
tsaki naja jin wani kiran ya kuma shigowa a fusace na 蓷ago wayar niyyata na gaya masa magana idan bai dai na dami na ba,
sai naga number Bappa ne ya bayyana kan Screen 蓷in wayar, da sauri na蓷aga wayar tare da yin sallama Bappa yace
"HAMDAH fito kuje asibiti ga Ahmad na jiran ki, kinsan yanzu ba ayin aure sai da gwajin lafiya kuje ku gwada lafiyar ku sabo da sai da shi
yanzu ake yin aure, kafin a 蓷aura aure gobe dole sai an bukaci takardar shaidar ingancin lafiyar ku wan da yafito daga hannun likita."
nace "Bappa lalle ake min kuma yanzu akayi bai bushe ba."
yace "To bari ace yatafi in yaso anjima sai ya dawo."
To na amsa da shi a takaice...

Sai bayan sallar la'asar kafin lallen yabushe aka wanke, duk nabi na gaji, a gabiye na fa蓷a cikin bedroom 蓷ina, nashige cikin bayi domin yin wanka nakuma gyara jiki na, dan naji alamar zuwan al'ada ta. shi yasa nace wa Hajiya Lubabatu zanje 蓷aki na na 蓷an watsa ruwa acan na huta dan nagaji da yawa,
ina gama kimsa jikina nafito, gaban mirror na zauna nasoma shafa ha蓷in mayuka masu da蓷in kamshi data ha蓷a min.
waya ta ce tashiga ruri ganin mai kiran yasa nayi banza, yayi ta kira yafi a kirga ban 蓷aga ba.
knocking akayi tare da yin
sallama daga bakin kofa, jin muryar Faty ce yasa nace tashigo.
tace "Adda HAMDAH wai kizo inji Yaya Ahmad."
fuska na 蓳ata nace "Kice bazan zo ba."
har takai bakin kofa nace "Bappa na gida ne?." tace "Eh." nace "Kice masa ina zuwa."
ta amsa da to tayi waje.
tsaki naja a fili nace
"Wlh badun kada Bappa yace naraina sa ba Allah da ba abin da zaisa naje."
sai da nagama iya yanga ta kafin nasaka kaya nafito ina gyara mayafin kaina, su Nasmah na ganina suka biyo ni da gudu suna fa蓷in "Mommy damu biki." Aunty Nasiba dake parlour'n kasa tana tare da masu aiki suna ta shirya abinci, nace mata zamuje asibiti tace "A dawo lafiya Allah ya tsare."
nace "Amin." nayi waje su Naseem suka biyo ni suna cigaba da fa蓷in zasu bini..

Yana zaune a mota yana ganin mu tun kan mukaro ya fito acikin motar.
ihun murna yaran suka sake sukayi gurin sa a guje suna fa蓷in
"Laa Daddy yazo oyoyo Daddy." ya bu蓷e hannun sa suka fa蓷o jikin sa ya rungume su yana dariya tare da bin ko wannen su da sumbata.
na karaso gurin fuska ta 蓷aure tamau, yasake yaran yana fa蓷in
"Kuzo mu bu蓷e wa Madam mota kada ta gaji da tsayu." yazaga 蓷aya barin ya bu蓷e yadube ni dakyau sannan yace
"Kyakkyawa ta bismilla taho ki shiga." yayi maganar tare da nuna min hanya da hannu yayin da 蓷aya hannun sa ke rike da marfin motar.
fuska na yamutsa namatso jikin marfin motar, ganin yana tsaye daf da in da zanbi nashiga cikin motar, sai na ja natsaya tare da na蓷e hannaye na a kirji.
murmushi ya yi kana ya蓷an ja da baya ka蓷an tare da fa蓷in "Bismillah Madam." baki na ta蓳e nashige cikin motar da bismilla. yamai da marfin ya rufe.
tuni su Naseem sun shige gidan baya sai tsalle-tsalle suke. yazaga gefen direba ya shiga ya ja motar a hankali yayi hon mai gadi ya bu蓷e get yasa kai yafita a hankali.

A hankali yake tukin kamar mai tautsayin kasa, yayin da su Nasmah keta zuba masa surutu yana biye musu, lokaci zuwa sai ya juyo ya kalle ni, niko na 蓳ata rai nayi kamar bana cikin motar.
sai da naji ya gyara parking kafin na 蓷ago, *HAM'NAS* International Hospital na ganmu ciki.
maganar sa najiyo yana fa蓷in
"Mushiga kyakkyawa ta ko na sauko na bu蓷e miki ne?."
tun kan yarufe baki nayi saurin 蓳alle marfin motar nafita ina jan karamar tsaki........!

Mommyn Twins ce
8/19/22, 10:56 - Ummi Tandama馃槆: *HMDH*

*WASA FARIN GIRKI*

*NA*
*RASHEEDAT S DIRECTOR

17
Chapter 37 · 0% Book details