Sashe 9
Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
ba. Babban gida ne masu mutnci. So u hv 2 b very carefl, ke ma ki nuna wa duniya kin fito daga babban gida mai cike da tarbiyya, OK?" Tace, "insha Allahu yaya zanyi iya kokari na". Yace, "to da kyau likita matar likita. Abba kasan wani abu? Ai mu juma munyi bye-bye da rashn lfya". Suna ta drya, anti rabi ta shigo itama. Sun jima suna hira, sannan uban dawaki ya bar garin minna tare da yarnsa kalla.! Anyi sallar magriba lokacn da suka shigo Fandogari, don haka a guje uban dawaki ya nemi bada farali. Bai wani ci abnci sosai ba, sbd abncn da ya ci da yammacin dazu a minna. Umma ya aika ta tattaro masa kaf kannensa da 'ya'yan gidan tare da ali. Duk suka hallara a falnsa, ya dubesu ya fara magana ckn rashn jin dadi, "abnda yasa nace a kira min ku, a gskya abnda ya biyo baya sakamakn maganar da muka yi da ku jiya, sam banji dadnsa ba. Basiru da amamu kar ku manta gaba daynmu ciki daya muka fito, babu bare. Kar ku bari tsegunguman mata su raba kawunan mu, domin da halima da hajo da gaje tare suka same mu. Bai kamata in gaya muku uzuri na ba, ku kuma ku koma kuna min yankn baya wajn mataynku, har su sami damar yada maganganu marasa dadi akai ba. Ko ban haifi daya daga cknku ba, ina zatn ni uba ne a gareku, kuma daidai gwargwado ban shiga hakkn kowa ba. Ali da sa'eed a wancn lokaci sun yunkuro, kowannensu yana son auren mama, a gabnku yaran nan suka rika rigima a junansu, gaba ta kullu, babu mai kalln dan uwnsa. Sbd Allah idan ban ynke wancan hukunci ba me ya kamata inyi? Shi za'a tsaga mama gida 2 ne, ali ya auri rabi sa'eed ya auri rabi? A gani na idn aka hana kowa zai fi mana alkhairi. Ko da bani da ra'ayn mama tayi zurfn karatu, ballantana ina da shi. Wlh bani da wani buri akan mama da ya wuce tayi zurfn karatu ta zama likita gabana. Amma da Allah ya sauya al'amarinsa, ba zan iya jayayya ba. Sai dai a cknku laf din nan na bar muku zabi, idn akwai mai iya yin wani abu bayn wnda Allah ya zartar bismilla, ina saurarnsa. Ni kam na yarda nayi gmanin al'ameen Allah ne ya turo shi, ban isa in koreshi ba. Kuna iya kirana kuda sbd kwadayi, ba zai sauya komai a jikina ba, don nasan har ga Allah bana bukatar sisin kwabo daga al'ameen ko mahaifnsa. Na kare maganata, idan akwai mai abin cewa yana da damar fadi". Gaba daya ka rasa mai yin koda motsi, sbd dogn jawabn uban dawaki ya tattaro musu kunya ckn idanuwnsu, musamman matan. Jin sunyi shiru, uban dawaki ya kara da cewa, "idan babu mai magana kuna iya tfya, shikenan magana ta kare" Har matan sun mike, alh. Basiru yace, "ku zauna. A gskya munyi kuskure, amma ynzu mun gane bamu kyauta ba ko kadan. Kayi hakuri alh. Da yardar Allah wata magana ba zata sake bullowa akan mama ba. Ku kuma hajo da gaje ku ba alh. hakuri, har ma da h. Halima" Da ganin fuskoknsu kowacce ba akan son ranta take magana ba. Sun dai bada hakurin, kuma abba da umma sun yafe, sun maida komai ba komai ba, a matsaynsu na manyan gida, sun nada gammo sun dauki girman kamar ynda hausawa ke fadin Babba juji ne. Aik. Adamu ma yayi nasa dan guntun jawabin na neman afuwa. Kowa ya tashi aka bar Ali a zaune, ba tare da yace wani abu ba. Abba ya dube shi yace, "akwai magana ne ali?" ya karkada kansa da ke sunkuye, sai hawaye shar-shar! Suka hau zuba. Uban dawaki ya sauke numfashi, gaba daya jiknsa ya mutu. Harga Allah bai taba tunanin soyayyar mama tayi zurfi ckn zcyar ali haka ba, wa ke ganin hawayn ali? Da yarntarsa ma ba karamar azaba ke sanyashi kuka ba, shi yasa yaci sunansa Gadanga! Domin kaf tsaransa babu mai nuna masa yatsa. "zo nan ali!" yayi kirnsa yana nuna masa waje bisa kujera kusa da shi, "zauna kaji". Ya zauna yana goge kwalla. "abnda nake sonka dashi ali kayi wa girman Allah ka dauki imani ckn ranka. Wlh a zatona tuni kun share maganar mama a zuktnku, ganin na jima da soke maganar. Amma kayi hakuri, ka dauki dangana kasa wa ranka, duk abnda Allah ya hukunta daidai ne" Ya dan gnge kwalla ya dube shi, "abba sa'eed ne ya hakura, amma ni burina inyi ta jiran mama har zuwa lokacn da zata gama karatnta. Kullum addu'a nake yi Allah yasa a tsayn shekarun nan zcyr mama ta aminta da ni". Ya numfasa ya kada kai, sannan ya ci gaba, "bansan yanda zanyi ba abba". Abba ya rungumo kafadarsa, "hakuri magani ne ali, ban son ka tashi hnkalnka. Mama 'yar uwarka ce, ka taimaka ka bata goyn baya tare da addu'ar fatan alkhairi, kaji? Ka kwntar da hnkalnka, nayi rantsuwa da mama tana da kanwa da na baka ita. Amma tnda babu, ina son kasa natsuwa ckn ranka, ka ji ni?" Yace, "naji abba, kuma na gode". Umma tace, "nima dai hakurn nan shi zan baka ali, gaba daya hawaynka sun kashe min jiki. Amma babu abnda zamu iya yi, sai dai ince Allah ya musnya maka da alkhairi" yace, "amin umma". Abba yace, "to tashi kaje ka kwnta, ka ci gaba da addu'a, komai zai wuce". Ya mike babu kuzari ya bar falon. Shiru su umma suka yi tsawn lokaci, kafn abba yace, "Allah ya kyauta!". Ta cire tagumi tace, "amin. Da gaske ali yake yi" "mtsw!" yayi dan tsaki ya tashi ya shige daknsa dauke da tausayn ali, ya bar umma zugum! Tana tunanin iska. Gidan yayi tsit! Ko da tasa damuwar. Washe gari da wuri ali ya koma birnin gwari don kara samun natsuwa. Idan bakwa comments sai inga kamar littafin ne baiyi muku dadi ba, na kuma sai inji bana son turowa din.