← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 79

Sashe 74

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

gidan kowa na kokarin kare kansa yayi horn mai gadi yabude suka gaisa ya ajiye motar a wajen ajiye motoci.suna tsaye kofar gidan dr al'ameen yana kwankwasawa yana mata dariya ganin yadda ta tsaya tamkar marar gaskia.jimawa kadan aka bude.ah! oyoyo dadin waleed yana murmushi yace anti niima sauqar yaushe?tace dazu dazu tafe kake da baquwa? yace wlh kuwa wai tanaso tazo taga waleeda.bakinta har kunne tajawo hannunta suka wuce ciki.tana mata sannu da zuwa.har kujera takaita.tace zauna inkira umma.suka zauna dr alameen yace antin ruqayya ce tana aure a kano.tace akwai fara'a sai gasu sundawo.anty ni'ima na riqe da hannun waleeda tana taka qasa dabas dabas.saboda kiba,rugu rugu!da ita.ga gashi kamar buzaye.mama ta zura mata ido ai batasan lokacin data tashi ta runguma yarinyarba saboda sha'awa data bata.bayan angaisa anty ni'ima takawo musu ababen sha.hajiyar ke tambaya hala wannan itace sabuwar mominsu waleeda?Yana yar dariya yace itace hajiya munje makaranta taga waleed shine tace sai na kawota 135-wajen waleeda hajiya tace madalla ya ya kyau Allah ya sanya alkairi yace amin yayin da mama ta kara sunkuyar da kai tanayi wa waleeda wasa ita kuwa tamkar ta taba ganin ta fariya kawai takeyi mata ya sunanta anti ni'ima ta tambaya yace sakeena sunanta tace sakeena ta dan yi shiru ka na ta kara fadin dadin waleeda ko dai sakeenar da marigayiya ta taba ban labari ne duk suka kalli juna sannan ya tambaya ta taba. Baki labarin wata sakeena ce tace ya dade da ta gaya min ka so wata yarinya sakeena amma Allah bai yi auren ba ta auri wani itama iya ce ta bata labarin irin son da kake mata haka ne? Yayi murmushi yace haka ne anti ni'ima ga ta kuma mun sake haduwa hajiya tace haka shirin ubangiji yake matar mutun aka ce kabarinsa ina fatan dai yanzu babu wani sai da na ko sakeena taja mayafi ta rufe fuska suna ta mata dariya kunya ta hana mama sakewa sha biyu rana suka bar gidan da alheri mai yawa da hajiyar taba mama waleeda kuwa harda kukanta da taga sun shige mota sun tafi sun barta, suna tafe suna labarin gidan irin kyakkyawar tarbar da akayi mata abin ya faranta mata rai kwarai da gaske bayan wucewa awa daya. Suka iso maitama gab daza su shiga gidan take cewa kasan wani abu ban fa gaya wa abba komai a kanka ba kamar yaya tace kawai gaya masa nayi zan zo weekend so na ke abba ya sha mamaki yace ai kuwa zai sha mamaki na bazata ma kuwa ba shi kadai ba kowa ma ya ganni zai saki baki yau , kin kyauta da baki fadi yayi horn aka bude musu get suka sulala ciki tace munyi sa'a yaya na gida ga motocinsa nan a jiye yace good al-ameen sa'a ke nan... mu je ciki asa mana rana yarinya balarabiya ta bakin waleed" ta ballo masa harara tace wace ce yarinyar yayi yar dariya ya bude murfin yana fadin Allah na tuba duka kwaya nawa kike ita ma ta fito gara dai da kace Allah ka tuba ta wuce yabi bayanta yana dariya suka tsaya bakin kofa tace ka tsaya anan zan dawo in shigo da kai yace ba laifi ina jira ta shige tana kwarara sallama duk suka amsa mata daga babban falo can ta wuce da sauri suna mata oyayo ta fada jikin abba da murna sanna ta juya. Wajen yayanta da anti amina duk ta gaishesu kana ta mike tsaye tace kun san wani abu duk suka zuba mata ido abba ya bata amsa sai kin fadi mama na tace duk ku rufe idanuwanku akwai abin mamaki dana taho muku da shi yayanta ya aje jarida yace idan kin ka nuna mana shirme sai na balla kafarki tana dariya tace na yarda to kun shirya mun shirya a rufe ido ina zuwa ta fice suna mata dariya abba yace ai sai mu rufe mu bude muga abin mamaki duk suka rufe suna dariya jimawa kadan suka shigo tare da al-ameen ya tsaya saitin daza su ganshi sosai yana ta murmushi tace kuna iya budewa duk suka bude kowa ya yi ido hudu da al-ameen dif yake dauke wuta ya zubo masa ido anti amina ce ta fara magana dokta ko ba shi bane mama tace gashi nan dai abba wanene a tsaye yaya ka gane shi yaya yace al-ameen abba ya miko hannayensa biyu yace zo nan al-ameen zo in taba ka in tabbatar da ba mafarki na ke yi ba ya tako da sauri bakinsa har kunne ya zube,137- gaban abba ya rungume shi yana fadin 鈥渢sarki ya tabbata ga allah ashe zan sake ganinka al- amin?鈥� Ya jima yana rungume da shi.sanna ya dago shi suka duba juna. abba ya numfasa ya sake fadin 鈥渉aba al- amin kuma sai zumunci ya yanke? Babu kai babu labarin dadinka?鈥� Ya-ce 鈥渒a yi hakuri abba. Tunda na ba kasar nan ban dawo ba. Sai da na kusan shekara biyar. Duk abubuwan da suka faru ban dawo ba. Sake haduwarmu da sakeena take gaya min har umma Allah yayi mata rasuwa kai kuma ga lalurar da ta same ka banji dadi ba Abba ubangiji Allah ya jikanta yayi mata rahama hannayensa biyu bisa kafadarsa ya amsa amin summa amin ina fatan su alhaji duk suna nan lafiya ya juya suka gaisa da yaya soja da anti amina yayi masu. Gaisuwar umma nan da nan aka baibayeshi da kayan ciye ciye dana sha kala kala ya jika mako shinsa da ruwan sanyi yace ashe haka al'amura suka faru abba wannan wane irin zaluncine da rashin imani, Abba ya kada kai yace ka bari al-ameen ai munga tashin hankali yarinyar nan ta dawo tamkar mahaukaciya a gari kowa yana ganin kamar rashin biyayya ce ta jawo mata lalacewa da kaskanci ashe ba haka bane ka ganta nan Allah ne yasa tana da sauran shan ruwa a duniya hankalin al-ameen ya kara tashi yace subahanallah Allah karabamu da sharrin shadan suka amsa da amin yace shine wannan zai zama dalilin da* tace ba zatayi aure ba sati uku muna artabu abba da kyar abokin na ya shawi kanta. Inda harna ce na hakura suka zuba mata ido kafin abba yace haka ne kuma nima na kyale ta ta zaba abinda tafiso dan hankalinta ya kwanta sai dai tun lokacin na sani dole wannan kudirin na ta ya tashi domin bani da wani buri da ya wuce in cika maka alkawarin dana daukar maka to Alhamdulilahi,138.tunda itama ta gane gaskia,nakuma tabbatar batada wanda takeso face kai.saboda haka duk lokacin daka shirya kazo adaura auren dafatan bazaka samu matsala da iyalinka dake gidaba.yayi murmushi yace ai babu iyalin abba banganeba.ta rasu abba shekara daya da rabi kenan.yace ayya Allah yamata rahma yasa duk musulmi suna kyakkyawar matsayi.yace amin abba.kowa yayi masa gaisuwa,,,,,suna suka ci gaba da tattaunawa.mama tace abba bakaga yaronsaba.yakusa tsawona.al'amee n yasaki baki yana kallonta,,yayinda abba ke fadin ah lalle ba shakka,su nawa ne?tace su biyu ne,abdulrasheed da ruqayya.sunan mamanta aka samata.abin tausayi abba tana haihuwarta ta rasu.tausayi yakama kowa sunata mata addu'a.al'ameen na amsawa haka suka wuni hira salloli kawai ke tadasu.dare yayi aka kai al'ameen masauqi.farin ciki kamar ya kashesa.shine mutumin dazai iya sharewa mama hawayenta.cikakken labarin abinda yasameta dayaji ya qara masa tsantsar sonta.bashida wani buri daya wuce ya mallaketa ta hanyar sunna.don ya tabbatar mata da cewa Allah baya zalunci kuma bayason mai yinsa.washegari qarfe tara suka bar abuja dauke da albarka mai tarin yawa daga wajen abba.suna shigowa suleja mama ta tunada waleeda.tadan dafa qirji Allah sarki waleeda kamar mu koma mu daukota.yace kinsan rigimar waleeda kuwa? bazaki iyaba nake gayamiki kukanta sai hajiya.139.Tace haka kake gani,badon karatu ba dana daukota.Allah taban sha'awa,jiya saidanayi mafarkinta.kukan da take lokacin dazamu tafi.yace ba waleeda kika gani ba ameera ce.ta ballo masa harara yasan hararar yakesha shiyasa yaqi waigowa ya rinqa yar dariya.ya qirqiro waka.yana rerawa idan da rai da rabo!.......al'ameen zaisamu ameer da ameera! mai harararsa yadena!...takada kai tana dariya Allah ya shiryeka!yace ameen.sannan yace na fahimci kinfison waleeda akan waleed,lalle zakuyi rigima dashi dan kishiyarsa ce.tace naga alama komai saiya tambaya yaji ko anyi mata shi ba a yimasaba? tace ba komai nasan yadda zanbi dasu yace ko? kana shakk ne?uwace fa! yayi murmushi yace uhm....naqosa inganki mama.tace bari gatse dama sunan kenan! yace godiya nake!dai dai lokacin daya dauki hanyar minna.idanuwa waje tace yaya haka?yace haka dinne.dan Allah ina zamu?yace yanda kika nuna ni suprise haka zan nuna ki mamakiyos!ta langume kai amma bakada kirki mesa zakamin haka?yace mesa? tambaya kike?any way....kinma riga kinba kanki amsa tunda kikace banda kirki.rashin kirkin ne yasa zan nunawa kowa cewa alqawarin Allah baya tashi.fuska yamutse tace wayyo Allah na!yace ke yasu!?ta numfasa bata bashi amsaba.yafara mata dariya yana karawa don a gaskia tanajin kunyan su mami balle kuma dady. Ganin abin yadameta sosai yace to miye abun damuwar keda zaku zauna nan bada dadewa ba.kinsan cewa ko bajima ko ba dade zaku zauna tare.tace ai da sai a bari na dolen yazo saboda Allah fa! Yace gaskia bazan iyaba kiyi haquri kawai muje kisha kunyar a yau.kinji ko bebina?tace naji sir! yayi dan murmushi yace thank you mah!suka ci gaba da hira kala kala.har suka isa minna.kai tsaye yadauki hanyar anguwarsu.tace tsaya bansaya wa mami komai ba.gayamin abinda tafi so?yace idan kinaso ki burge mami kisaya mata carrot.cucumba,da kankana.to muje insaya mata.yace karki damu munayin kwanar can akwai masu fruit.yana maganar suna shiga kwanar sai gasu birjik!yayi parking duk suka fito mama ta kwasa kamar banxa gaba daya akace dubu daya.alameen yazaro zai miqa tace anyi ba ayiba kenan.nice zansaya mata bakaiba kokai kace?yakama kunnuwansa tuba nake wannan jan idon?tayi murmushi harmai fruits na tayata.ta zaro dari biyar biyar sabbi dal ta miqa masa akasa a boot.suka wuce alameen na tsokanarta hajiya mama kenan kinfara raina min wayau!tun jiya kike kashe min kudi,karfa ki maidani mijin hajia?tace sai me? yace sai ni baban ameer da ameera.tayi dan tsaki ta kyaleshi yana mata dariya.sunyi fakin harabar ajiye motoci,suka fito shima ya ajeta waje kamar yadda tamasa.yashiga ciki tare da sallama.maminsa na dakin dady.daga can ta amsa sallamarsa.ya qarasa ciki da fara'a maraba da bokan turai!.inji mami yace mamina!ya tsugunna gabanta yadafa guiwowinta.ta dafashi tace ya aiki?yace
Chapter 74 · 0% Book details