← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 79

Sashe 5

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a rai, nan da nan farin ciki ya rufeta, ta mike da gudu ta nufi dirowar kaynta, ta zuba ado ta rufa mayafi, ta fito ta doshi falon baki gabanta na harbawa, amma zuciyarta fara sol! Duk da cewar bata tabbatar da hukuncin da abbanta ya yanke ba. Sai dai tana da yakinin akwai alamun nasara, tnda aka ce taje da gaishe su . Tayi sallama ckn kunya ta shiga, ta sami wuri gefe ta tankwashe kafa, "sannunku da zuwa". Kai bakin marafa da kaninsa kamar gonar auduga, su kansu mama ta girgiza su, sun tabbatar da al'ameen ya darzo, fatan da suke yi Ubangiji yasa kyanta har ckn zuciyarta yake. Cikin ladabi da tsananin kunya ta gaishesu, su kuma suka amsa ckn farin ciki da nuna kauna a zahiri. Marafa ya taso yazo gabanta, ya tsuguna yace, "al'ameen ya zabe ki, nima haka. Sbd haka sai ku rike juna amana. Har Allah ya nuna mana lokacin da muke dakon zuwansa, kin ji?". Ta kara yin kasa da kai, sannan ta amsa da kai. Yace, "madalla, to mun gode". Yasa hannu a aljihu ya zaro sababbin bandir 'yan wazobia ya aje a gabnta, "wannan kyauta ce don nuna farin cikina gare ki, sbd zabar dana ya zama mijinki". Kunya kamar ta nutse, da kyar ta iya fadin, "na gode. Allah ya saka da alkhairi". Yace, "to me zan ce wa al'ameen idan mun koma?". Ta yunkura a guje ta bar falon, suna mata dariya. Shi kansa Uban dawaki yana mamakin kansa, irin farn ckn da ya tsinci kansa. Alh. Saifullahi ya mike, "to bari muyi harama, mun gode kwarai, Allah ya tabbatar mana da alkhairi". Suka yi musabaha, uban dawaki na fadin, "amin". Yayi musu rakiya, sai da yaga tashnsu sannan ya shigo gida. "Saboda Allah mama haka kuka yi da abbanki?" ummanta ke tambaya, ta kada kai, "wlh umma ba laifina bane. Babu abnda ban gaya masa ba, yaki yarda. Kinga wannan turowar ma ni bansan da ita ba, kawai ce min yayi shi yasan ynda zai bullowa al'amarin, don haka in sa masa ido". Tace, "ke din ma kina sonsa ne, ai nasan halinki sarai mama, ba don haka ba ko kallo bai isheki ba. Kin bani mamaki wlh, watau shi yasa jiya kika ce minna zaki hutu, ashe da manufarki....." Abbanta ya cafe, "tabbas haka ne....." ya karaso ciki ya zauna, yana dubanta yaynda gabanta ke ci gaba da harbawa da sauri. "ya aka yi haka mama na? Ki turo min babban mutum irin marafa, bayan kisan zai yi wuya ince a'a ko?". Hankalnta ya kara tashi, ido tam da hawaye tace, "wlh abba ba haka bane, hasali ma ni bansan shine mahaifnsa ba, domin ni bai gaya min ba, ka yarda dani abba, don bani da nufin saba maka. Duk hukuncn da ka yanke akan wannan al'amarin bazan bijire ba". Tasa hannu ta goge kwallan da suka zubo bisa kuncnta. Yace, "matso nan mamana". Da rarrafe ta isa gunsa, ya kamo kafadarta yace, "dubeni nan". Ta dago manyan idanuwnta da suka fara jirkita ta kalle shi, "na yarda da ke dari-bisa-dari mamana, sai dai abnda nake hangowa watakila ke ba zaki hango shi ba. Bayn aure mata sukan fuskanci 'yan matsaloli musamman idan Allah ya kawo rabo ckn gaggawa, wanda idan ba ayi sa'a ba sai ya jawo koma baya ga komai nata, ba ma karatu ba kadai. Amma bazan matsa ba mamana, ya kasance nayi jayayya da shirn Allah, don haka ina muku fatan alkhairi". Ta rufe fuska da tafin hannunta, fuskarta na bayyanar da murmushi. Jiknsa ta langwabe, dadi kamar ya kasheta. Yace, "ho 'yar nema! Watau kice kina son al'ameen ko?". Ta tashi a guje ta bar musu dakin. Uban Dwk ya numfasa sannan ya dubi Umma to ya kika ce? Kinga dai yanda al'amarin ya kasance. Fuska sake tace yaya kuwa za'ayi Alh? Tunda ka amince ai shikenan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, yace Ameen. Baki ma sani ba wai shima likita ne mun fito ina musu rakiya shi baban nasa ke gaya min. Nace itama abnd take son ta karanta din kenan. A hakikanin gsky ya tabbatar min babu damuwa I.S.A zataci gaba da karatunta, kinji inda muka tsaya dasu. Sauran maganar gaisuwa da baiko nace su bari mu zauna da yan'uwana. Ta numfasa gsky ne hakan kuma yayi kyau saidai kana ganin bazasy dora wani abu a zukatansu ba? Kasan fa su Ali sun so ta ka hana kace karatu zatayi. Yayi dan shiru jim, kafin yace kinyi magana amma ba komai nina san bayanin da zanyi musu. Tace shikenan sun dan jima suna maida zancen. Mama kuwa tana dakinta rayuwa ta zame mata sabuwa. Duk. Inda tajefa ido Al-Ameen din take gani kwarjininsa murmushinsa salon maganarsa da taushin murya mai dadi. Bayan sallar la'asar lokaci ne da kannen Uban dwk ke dawowa daga gonakinsu. Yaran nata daukar darasin Muhammadiyya kamar kullum. Uban Dwk ya tara kannensa a falonsa ya zayyane musu komai game da abnd ya faru, nan taje ransu ya sosu ba kadan ba kallon juna suke cikin al'ajabi suna tambayar zukatansu. Ina karatun da akace Mama zatayi? Ya kara gyara zama yace nasan zakuyi wa zukatanku wann tambayoyu a game da magana ta, sbd Aliyu da Sa'aeed dama sauran samarin da suka yo caa akan Mama, suna neman aurenta amma na hana, sbd dalilin zurfin karatunta. Wannan magana wllh haka take cikin zuciyata kuma shine buri na saidai marafan lafai ya cika min ido kwarai da gaske, banjin kuma zaku goyi bayan na bada masa kasa a ido ba, alhalin da kansa yayi tattaki neman alfarmar da bata fi karfina ba. Abnd nakeso in rokeku shine donAllah don son Manzon Allah SAW kuyi min uziri akan wann hukunci dana yanke karku zargi komai sai alkhairi, ina fatan zaku bani hadin kai dari bisa dari. Alh Basiru mahaifin su Aliyu kuma yafi kowa yaya a gidan ya gyara zama yace Alh ai wann al'amari na Allah ne kuma abin alfaharinmu ne ace Mama ta sami cigaba domin cigaba ne samun irin wann hamshakin zuriya ta marafan lafai. Mama yar mu ce kuma muna farin ciki tare da fatan Allah ya tabbatar da wann abu kome kace Adamu? Alh Adamu karamin cikinsu ubansu Sa'eed yace wann magana haka take Alh mu munsan cewa Mama bazata auri kowa ba sai wanda Allah yace shine mijinta sbd haka muna murnar samun wann babban rabo daga Allah. Cikin jin dadi Uban Dwk ke magana "godiya ta tabbata ga Allah da yasa na sami hadin kanku cikin sauki nayi godiya sosai, abu na gaba shine sunyi maganar gaisuwa da baiko nace su dan saurara min muyi shawara da yan'uwana. Me zaku ce akai? Alh Basiru yace hakan shi ma yayi kyau sai ta gama sakandiran ne ko kuwa yanzu suke so? Yace a'a sai ta gama tukunna. Idan haka ne zaifi kyau a bari ta gama din sai ayi baiko a sa rana ko kuwa? Alh Adamu yace haka yayi daidai. Allah ya nuna mana lokacin lfy. Kowa ya amsa da ameen. Uban dwk ya shaida musu kyautar kudin da Marafan yayiwa Mama na tsabar kudi naira dubu hamsin. Aha! Gsky ta bayyana abnd Uban Dwk yake so kenan ruwan kudi. Haka zuciyoyinsu suka saka musu, ya fiddo kudi ya nuna musu kafin yace saidai maganata gsky wann kudi ko sisi bazan taba a cikinsu ba zanci gaba da ajiyarsu cikin banki da dukkan wata kyauta dazata zo daga baya har sai wann abu ya tabbara iidan kuma an sami akasi ba fata muke ba sai a mayar musu kayansu. Ko yaya kuka gani? Sasan alh. Basiru suka tasu da matansu suka kwnce musu abnda ya wakana a falon uban dawaki. H. Hajo matar alh. Basiru ita ta fara tsoma baki, "amma kuwa idan baka mutu ba zaka ga abin mamaki kala-kala. Ynzu da gske alh. Babba ne ya iya tararku da wannan maganar? Ko ya mance abnda yayi a kan su ali ne?" Alh. Adamu yace, "ya manta? Babu abnda ya manta. Hasali ma sai da ya kara maimaita zancn su". "tafdi!" inji h. Gaje, matar alh. Adamu. "kai dai kaga dan-uwa kawai, ai dama tun farko na fada, ba wani karatn da ake so tayi, burnsu mai kudi ko basarake, sbd su ganin mama tafi kowa kyau a duniya. Shi yasa suka dauketa a matsayn wani jari gare su. Ai shikenan, Allah ya bamu lfya. Muma namu 'ya'yan bamu fidda ran Allah zai azurta su ba. Ba Dai kowannensu ya kama aiki ba? To muje zuwa wai mahaukaci ya hau kura. Harda wani za'a tara kudi a banki, don kawai kar ya baku wani abu ne a ciki, shine yake muku 'yan dabaru" "ni dama bance a bani ba, me zanci da su?" inji alh. Basiru. Alh. Adamu yace, "balle kuma ni, ai tuni na haramtawa kaina komai na alh, tnda ya nuna mana kiyayya a fili". Ya tashi yayi waje, alh. Basiru yabi baynsa. Yaynda h. Gaje ke fadin, "sai musa ido mu gani, da wane bakin h. Halima zata gaya mana zancan". H. Hajo tace, "kema dai da son jin baki kike. Tnda mijnta ya furta, ai ba sai ta maimaita ba, tana nan tasa ido muje mata murna 'yarta tayi farin jin". Tayi 'yar shewa, "Allah mai iko, kiri-kiri an raina mana wayau?". H. Hajo ta ja tsaki, "mtsww! Kina mamaki kenan, dama kin daina wlh, domin an jima ana ruwa kasa na shnyewa. Ba girin-girin ba dai, tayi mai. Ba auran gidan kudin ba, kwancyar hnkali!" Tana rufe baki tare da sallamar umma, suka amsa suna wani yatsina suna yarfarwa. Ta zauna tana fadin, "na shiga sasanki yara suka ce kina nan" "uhm! Ina nan" "dama maganar 'yarku ce, ban sani ba ko su alh. Sun gaya muku halin da ake ciki?". H. Hajo tace, "sun gaya mana, yanzu haka ma shirn zuwa sasan naki muke, sai kuma gaki. Ashe kuma mama an fasa karatu aure za'ayi?" Tace, "to yaya zamu yi, mutane sun cikawa alh. ido, sannan da alama ita ma maman tana son yaron. 'ya mace kuwa idan ta nuna tana son aure, to yi mata auran shine mafi alkhairi ga iyaynta". H. Gaje tace, "gaskya kuwa, gidan hutu ai dole a so shi.
Chapter 5 · 0% Book details