← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 79

Sashe 23

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

BAKIN CIKI 1***12 Tace, Ita ma aunty ai ta bingire, dube ta aza zaune take yinsa. Ta so kayi breakfast dadin kana jiranka. Ta juya inda Mama ke xaune tana famanxuba mika, Yayan ki zai fita ne, ki fito ku gaisa. Tace,Gani nan. Suka fice da Malami, ita kuwa mama bayita shiga ta wanko Fuska ta fito. Suna bisa tebur ta same su fuska ba walwala, ta ja kujera ta xauna, inakwana yaya? Yace kalau, ya lazu Doktan ki?Murmushin bai kai ciki ba tace, ai ni ban shi ba Yaya.Yace a Yau kuma? Zamuyi waya ai, zan gaya masaabinda kikace. Tayi shiru Aunty amina tace, me yasami idanuwanki? Kamar sun kumbura? Ai ba sa min ciwo, tace, to meyasa? Da alama dai sun kumbura.Ta murje idon. Yayanta na cewa, ke me zai dameki?Ita da take tare da lazy Dr. Suka fara dariya, ita kuwayake takeyi. Ta sa abincin, sai juya masa cokalitakeyi, ta kasa ci, da alama tana son tayi matamagana ne. Amma ta kasa, aunty amina ta kare mata kallo, tace wai menene? Ta dago ido ta dubeta, tadubi yayanta, jim kafin tace, Fandagori nake sonxuwa. Fandagori? Me zakayi? Yayan ta ya tambaya.Idanuwan ta suka yi rau- rau! Da kwalla tace, ina sonxuwa ne kawai. Ya xura mata ido yace, xo nan bebi.Ta taso a hankali ta zo gaban sa ta tsaya. Ya kamo hannnayenta biyu yace, me zaki yi a can? Bayan yaukwanan mu bakwai da dawowa? Tace Umma na keson gani. Ya dubi Aunty amina, yace kinji shagwabarbanza! Ke kadai ke da Umman nan ne wai? To ba zaiki ba ki ba, nan zaki zauna sai karshen wata. Ta karamurtuke fuska. Don Allah yaya kayi hkr ka bari in tafi. Ni wlh ko a motar haya xan iya tafiya, ba sai direbaya kaini ba. Yace, motar haya? Baki a tunaninki bebi,banso in sake jin wannan maganar, karshen wata inada hutu zamu tafi tare. Is dat clear? Ya fadi tare damatse yatsunta da karfi. Tayi tayi ta kwace amma takasa. Ya kara girgiza ya, ya kara fadin Is dat clear? Ta kara cunno baki ta kauda kai. Ya saki hannun yace je ki ci abinci, ta juya da gudu ta haye sama.Aunty amina ta kwala mata kira, Mama! Ya dagamata hannu, a kyaleta! Iya shege takeji kwana biyu,ko baki lura ba? Tace haka ne fa, ni ma ban ganemata ba kwana biyu. Ya dubi malami yace, lazy man ayi sauri mana. Yace na gama Dadi. Mu tafi kenan?Ya ce eh. Suka bar tebur. Madam ta kwaso masajakar sa da hularsa. Malami ya goya, ta sa jakar suka fito tayi musu rakiya xuwa mota. Sai da suka fita,ta dawo cikin gida. Kai tsaye wajen mama ta nufa,tana xaune bakin gado ta kumbura suntum! Idanuwan ta sun kada jajur! Ta kare mata kallo, sannan taxauna gefenta, wai Mama me yake damunki ne? Komunyi miki laifi ne? Ta kada kai. To me zai sa ki tashihankalinki haka? Wajen Umma nake son inje. Ai bahana ki akayi ba, tunda yace ki bari karshen wata kutafi, sai kiyi hakr xuwa tym din. Tayi shiru ba tace komi ba. Ta rungumo kafadarta, wannan abu na banimamaki, kamar yau kika fara xuwa garin nan? Dabakinki fa kika ce kin fasa kara kwanankin da kikacexakiki, balle ace matsa miki akayi. Tace sai da na zokuma naji bana son zaman. To kiyi hkr, tundaYayanki yace ba xaki motar haya ba. Shikenan, yauwa autan Umma. Ni bari in je inyi wanka, in dankwanta kafin rana tayi. Tace to, auntyn ta bar dakin takoma nata. Ta aiwatar da duk abinda take son yidaganan tabi lfyr hafo. Bata jima ba, ta sunkuci jakarhannu ta rataya ta yafa mayafi ta debo takalman tarike a hannu ta sadado ta sauko kasa. Shigar ta falon ke da wuya, wayar Al-amen ta shigo falon, gabanta yayanke ya fadi, ta tsaya cak! Tana zare idanuwan.Tsoron ta Allah, tsoronta kar karar wayar ta tashi antyamina. Saboda haka tayi azama ta nufi wajen wayar,ta daga kan taaje gefe, ba tare da tayi magana ba,balle ta san waye akan layi. Ta dan kara tsayawa, jim shiru bata jin wani motsi ba, tayi hamdala ga Allah. Taaje takalmanta ta xura tayi waje abinta. Babufargaban komai ta doshi gate har tana gaida masugadi. Suka amsa tare da fadin a dawo lfya. Taceameen. Tayi waje cikin sauri ta bar sashin unguwar tafito a sarari a inda ta samu shatan tashi ta kai ta tasha. Tayi muguwar sa'a fasinja daya akejira motarta tashi xuwa Minna. Inda daga can zata sami MotarFandagori. Sha biyun Rana Aunty amina ta farkabarcinta, ta sauko falon kasa, tin daga nan ta faraganin abinda bata sa ba ba, kayan abinci na aje bisatebur yadda ta barsu. Mama ta bata kwashe ta gyara wurin ba. Cikin ranta take fadin, lallai yau Mama tsiyatakeji. Haushi ya isheta ta nemi kujera tsakar falo taxauna ta shiga kwala mata kira. Shiru bata amsa ba.Mamaki ya isheta, t yunkura zata tashi idanunwantasuka kai bisa waya, Ah ji wani sabon iya shege. Sumama! Ta nufi kan wayar ta dauka ta mayar yadda take. Tana jan tsaki. Ta hawo saman ta fada dakinmama cikin zafinta. Ganin babu kowa a dakin yasatayi turus! Cikin sanyin murya take kiranta, mama! Kokina toilet ne? Shiru? Wai malam yaci shirwa. Tabude bayin vata ciki. Hankalinta ya tashi ta sauko dasauri tana kiran Mama! Har waje. Daya daga cikin masu gadin yake gaya mata ai ta jima ta da fita.Al'amarin ya daure mata kai. Ta dawo falo..... Tana mamakin mama. Karar waya yadawomata da hankalinta, ta tashi taje ta dauka, hello! Muryar aunty Rabi taji ta amsa. Hello aunty amina,Rabi ce, tace nagane ai ya yara? Lfya lau wlh. Waime ya smu wayar ku ne? Al- ameen ya kirani, wai tunsafe yake neman layin, amma yana engage. Tace, uhm.... Ke dai bari, ina nan ina ganin abin mamaki.Kamar yaya? Tace, Mama ce daxun da safen tacewaYayanta ita gida zata koma, yace ta bari karshenwata ya kaita. Nima na rarrasheta, har fa ta amince,wai kuma na tashi barci yanzun, bata ba dalilinta cikingidan nan. Sannan ina zaton ita ta cire mana kan waya ta aje gefe. Cikin al-ajabi tace, to saboda me? Oho! Kuma ba ayi mata komai ba? Wai zai yi mataRabi? Ko da ma anyi matan ai be kamata tayi hakanba ko? Tace gaskiya ne ka, ah to, ita da yayanta ne.Ni ba babu ruwan. Tace, amma ai mama bata dawannan halin, me yasa za tafar shi yanxun? Wlh bakiji ba duk Al-ameen ya damu, nace masa ya barizanyi tryn inji. Tace watakila don taga kowa na rawarjiki ne da ita, shi yasa take son ta lallace. Zata kuwayiwa kanta sakiyar da ba ruwa, idan ta bari yaron nanya kubce mata. Aunty Rabi ta numfasa tace, to yanxumenene abinyi? Tace, yayan nata zan kira Yanxun in gaya masa ta gudu, Allah ya sawwake. To ameen. Taaje waya, sannan ta sake dauka ta lallatsa lambobinmaigidan na Ofis, jimawa kadan ya dauka, ta zayyanemasa kaf, abinda ke faruwa. Nan take haushi ya rufeshi. Ya mike cikin fushi ya fito daga Ofis, ya fadamota bai zame ko ina ba sai tasha, jami'an union ya samu ya bayyana masu kamaninnta, nan take sukabashi tabbacin ta zo tashar ta shiga motar xuwaMinna tun safe. Ran maza ya kara baci kwarai. Yafada motar sa yana tambayar kansa, dama mama taiya irin iskancin nan? Lallai zasu gauraya, zatayabawa aya zakinta... Karfe uku da rabi mota ta aje taabakin titi, ta fito ta gangagro saitin shagon danliti, saidai shagon a rufe yake. Babu kowa wajen. Ta tsayatana kallon kofar shagon kafin ta wuce, tana tafe tanawaige ko zata ga Danliti ya dawo, amma har ta dainahango shagon. Babu alamun kowa. Taci gaba da tafiya ranta bace na rashin ganin Danliti, xuciyartacike da tambayoyi, tana hasashen menenemusababbin rashin xuwan Dan liti shago? Tun dagakofar gida yara ke kwala ihun mama oyoyo! Shi yasaUmma ta fito har kofar sassan dauke da mamaki bisafuskar ta. Suna hada ido tace ke kuma dga ina haka? Ta kwaso da sauri ta rungume ta, Umma na! Tayisauri ta dago ta, ta xura mata ido, meya faru ne? Mekuwa Umma? Na dawo ne kawai. Ta wuce uwar tabiyo bayanta, bata yarda da ita ba. Cikin falo yara sunrufeta, tace, kuyi hkr ban siyo muku komai ba, gakudin nan kuje ku siyo biskit. Ta dauko Naira Hamsin ta basu., duk suka watse da murna. Har yanxunUmma kallonta takeyi, tayi dan murmushi tace, saikallona kike yi Umma? Tace dole in kalle ki, kin shgokamar an koro ki. Ni bawanda ya koroni, ke nake tamafarki Umma, nace gaskiyya ni xan dawo. To inajakar kayanki? Tana can, kamar yaya? Yaya ne yace baxan taho ba, ni kuma na silalo na gudo. Ta daukisalati ta sauke, kika yi me? Kanki na lfya kuwa?Mama ki gaya min gaskiyya dawa kuka yi fada? Taceumma ni ina fada ne? Da wan xanyi kuwa? Umma kiyarda da ni, wurinki nazo. Ba zan taba yarda dake baMama har sai Yayanki ya zo naji ta bakinsa. Kuma wlh naji akasin abinda kika fadam sai na bata miki raifiye da zatonki, kinji nagaya miki. Na yarda, shikenan,Ina abbana? Ya tafi kd, tayi 'yar dariya, Allah sarki inaango da amarya? Yau kwanan su uku da komawa.Kije ki zubo abinci ko sai kinyi sallah? Tace bari infara cin abincin, yunwa nakeji. Ta tashi ta shiga ta xubo abincin ta dauko ruwa ta dawo falon ta xauna.Bata wani ci sosai ba, saboda cikinta ya cushe dayunwa, don ko karin safe batayi ba, bayan ta gamatayi sallolinta tayi wanka, cikin kayayyakinta, dakegida ta dauko tasa. Ta fito tace zata shiga sasa tagaishe su, daga nan zata wajen Baraka. Umma tace daga xuwanki? Ba inda zakije sai Yayanki ya zo najidalilin dawowarki gida. Ta ya mutsa fuska, tace kaiUmma! Barakara kamar wata bare, kuma wlh damada xan tafi bamu sallama ba, na wuce, hkr zanje nabata. Tace, tazo nemanki kinbi 'yan abuja, amma bainda zaki, kinji na gaya miki. Ta bata rai sosai. Ta jefar da gyele bisa kujera ta koma dakinta. Ummatace, in kinso kiyi bindiga, ba fushi ba. Ta shige natadakin. Jimawa kadan mama ta fito cikin sanda ta lekafalon, daga nan tana jiyi sautin Umma tana karatunQur'ani. Tayo sanda takalmin ta a hannu, ta daukigyalan tayi waje. Bata
Chapter 23 · 0% Book details