← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 79

Sashe 32

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kan magana ta. idan kin canza ra'ayi ki koma minna zuwa gobe Alamin yaji ki hankalinsa ya kwanta kinji? yace in gaishe ki kuma yace inyi maki addu'a. Ta taimaka mata ta kwanta a hankali idanuwanta rufe suke yayin da mami ta dafa kanta tayi mata addu'oi da alamin yace tayi sannan ta kirata ta bude ido. nizan koma sai najiki a minna karki bari shaidan ya rinjayeki ki bar mai tsananin sonki cikin kunan zuciya nakasa zaiyi kinji? ta lumshe idon a natse mami ta wuce ta bar dakin umma ta shiga tare da sallama ta nemi wuri ta zauna yayin da baraka ta fice. ta basu wuri ta saurareki? tace to! bata dai tanka ba sai kuka da zan fito. ma nayi mata addua' kallo na ta dinga yi. da alamun za'a dace tace kwarai da gaske bari in lallaba hajia zan shiga wajen gwaggo sannan mu wuce . to a gaishe ta da kyau Allah ya kiyaye hanya Suka wuce suna fadin"Amin"har kofar gida tayi mata rakiya,motarsu ta daga ita kuma ta dawo gida dakin mama a koma suka taru da baraka suka ci gaba da yi mata nasihohi tana kudundune bata tanka ba,balle su gane me take nufi,Awa guda bayan tafiya mami yaya. Abdul- kadeer ya iso gidan daidai lokacin kuwa Abba ya dawo gidan,yayan tare yake da dakarun sojoji guda uku,duk suka fito,suka toge suna sarawa abba,sannan suka gaishe shi tare da yayan suka rankayo yana ruwan masifa, maganar banza yarinyar nan take yi,mu makace ta kawo shi ko mu muka hadasu wannan ai iskanci ne yanzun nan zan wuce da ita shiya na dauko kuratan nan su yi min gadinta a mota na ga ta inda zata fito,Nonsense kawai" Abba yace kayi daidai domin ni mama ta ginsheni ko ganinta bana sonyi cikin gidan nan,saboda "BAKIN CIKI",abu kamar al'mara yana so ya zama gaske yarinya ta bamu kunya ta zubar mana da mutunci basu ma san sun shigo falon ba sai da umma tace maraba da babban yaya yace sannu umma bamuyi sallama ba ko?raina bace yake ina mama?tana daki ina fatan tafiya kazo yi da ita sosai kuwa umma akwai kurata uku nazo dasu wadanda zasu gyara mata zama muddin tayi yunkurin bata mana lokaci tace yayi kyau wallhi yanzu ma hajiyar al-amin ta bar gidan nan bakaga uwar kunyar da ta lullubeniba na rasa inda zansa kaina Abba yace tazo kikace"tana ma cikin garin nan bata wuce ba"Abba ya nemi waje ya zauna ya kama kai,shi kuwa yaya babba dakin ya nufa kina jina baza ki fito ba"umma tace da wace kafar zata fito bayan ta kusan kashe kanta,yace kadan ta gani amma yau sai kin bar garin nan ko za ki mutu!Useless girl!kina nufin ki zubar mana da mutunci ko,baki. Kai wannan matsayinba,I swear,kin ji na rantse"yasa hannu ya fisgo ta da karfin sa yana fadin"stand up my friend"ta tsandara kara mai garfin gaske saboda gaba gabobain ta suka amsa suka kaiwa kwakwalwar ta zuwa falon dole gabobin suka loma aiki ashe dama wuri suka samu. Ya dankwafar da ita bisa kujera tace wayyo na shiga uku yace"No lokacin bai zoba tukuna sai kin ci gaba da bijire wasu umma I'am telling you! yau abuja zamu wuce ki zauna can, sai lazy doktan ki ya dawo ai ke ki ka zabe shi tun farko so now you have no reason ki ce kin fasa bayan kun kusa aure ya dubi umma yaci gaba karki ji tausayinta ta umma ki fidda ta a ranki har sai tayi biyayya a gareku, Ta kada kai tace tuni mama ta fice min a rai balle tausayinta ko alama babashi cikin raina ka tafi da ita duk abinda ya dace kuyi mata don ta gane kuskuranta yace wannan dole ne Abba bari mu wuce umma ta fara magana bari in hado mata kaya yayin da abba da babban yaya kamar zasu cinye mama a falo kuka take tamkar za a zare mata rayuwa umma ta fito da jakar kayan ta wurga mata gyale bisa jiki,yaya soja ya mike tashi karki bata min lokaci taki mikewa yasa hannu ya maketa sannan ya cafko. ta yana fadin zan iya karya ki u know dat! gara ki shiga hankalinki bai sake taba har kofar gida ita kuwa umma cikin sasa ta shiga ta gayo masu za a wuce da mama don haka suka yo waje ganin yadda za a yi saboda suji dadin karaars wa. A gaban su ya cilla wa kuratan daya zo da su ya ce kusa min ita a mota! kan kace kwabo mama na cikin mota, suka sanya ta tsakiya yayanta na gaba sanda ya jefa jakarta a but yaya ya juya da sauri ya zauna matsayin driver babu bata lokaci ya murza mukulli mota ta tashi ya bar wajen, idanuwan baraka suka cika da kwalla nan da nan ta fasa kuka ta koma cikin gida da gudu. sauran matan na ta fadin Allah ya kiyaye hanya ubangiji yasa a dace. umma ta juya ta shiga gida su suka biyo bayanta . ganin hankalin umma yayi mummunan tashi yasa hajia gaje ta janye hajia hajo cikin gida ta mika hannu suka tafa sannan ta tallafe haba ido waje tace Ashe abin har ya girman haka? wanan sojoji kamar an zo kama gagararren barawo? ta ce ai kamar hakan ne tunda ta gagari iyayenta. zamuga ikon Allah yarinya na neman tayi wa iyayenta bakin cikin daula, sun ga samu zasu ga rashi ai kinga haj halima kamar ranta zai fita sai kace dole suka sake tafawa haj hajo tace Hakki ne nake gaya miki kadan ma suka gani badai danliti ta jajibo masu ba? Allah dai ya kiyaye lalacewa! ta tabe baki Nayaushe kuma? wai ance wa kuturu Allah ya laance ka! shagonsa fa take zuwa tsinancewa ai ba sai an tambaya ba! hajia hajo tace Allah shi kyauta haj gaje ta amsa na gaba domin dai wannan ya riga ya faru anyi abin kunya maga yadda za ayi! sun jima suna yada labaran banza da karairayi kai duniya ina zaki da mu? rayuwa kenan uban dawaki da umma suna kallon ikon Allah suna fama da BAKIN CIKI sai fatan Allah ya musanya masu alkhairi Mama kuwa tun isowarsu Abuja take kudundune cikin daki duk hargagin yaya soja baisa ta dauki lomar abinci tasa wa bakinta ba,al'amari ya daure wa anti amina kai ta zauna ta siga yayyafa mata nasihohi da rarrashi ko Allah yasa ta gane amma ina Alla bai nufa ba tukuna shi kuwa soja babu abinda ya dame shi cewa yayi zai fi kyau da zata bari yunwa ta kasheta a yau hakan kuma shi zai tabbatar masa ta cika mai kunnen kashi,yasa kai ya bar gidan amma kuratan sojojinsa na nan tsare da gidan bayan masu gadi mutun biyu ke nan yanzu sun zama su biyar,kafin yamma mama taci kukan daya fidda ta daga hayyacinta bama ta jin tarin yunwar da ke cikin ta saboda tsananin tashin hankalin da take ciki domin ita kanta ta san ta shigo kurkuku zai yi wuya ta kara ganin dan liti sai dai tunanin ta bai yanke ba duk tsananin da zata shiga baza ta taba auren wani ba dan liti ba. BAKIN CIKI 2***5(TRUE LIFE STORY) Saboda haka taci gaba da zama cikin kunci da yunwa har bayan sallar isha'I yayanta ya shigo gida kamar shi alamin ke kira wayar sa ta hau bugawa falon kai tsaye kan wayar ya nufa ya dauka yayain da malami ya sheko da gudu don yi masa oyoyo.anti Amina ta biyo bayansa daga jin muryar al'ameen kasa yana cikin farin ciki da doki cike da zuciyarsa ina yini yaya,yace lazy dokta ya karatu?"Yana yar dariya ya amsa Alhamdulillahi ai na kira can minna don in tambayi jikin mutunniyar sai aka ce min ta sami sauki harma ka taho da ita, yace haka ne amma kasan yana yin rashin lafiyar sai a hankali cikin dan kankanin lokaci sai ta birkice bari in turo maka ita,koda kaji sauyi daga gare ta kar ka damu haka yanayinta ya sauya,jikin sa yayi mugun sanyi duk a lokaci guda gabansa ya ci gaba da faduwa murya dishe yace to yaya Allah dai ya bata lfy,ya amsa da amin ya aje kan wayar gefe ya amsa gaisuwar iyalinsa sannan ya haye sama ya fada dakin mama yana shiga ta kara kudundinewa cikin bargo yasa hannu ya kwashe bargon ya watsar gefr yace tashi zaune sai ga antin ta shigo ta matsa bisa shimfidar ta birkito ta tana fadin yi mata a hankali ke mama tashi kinji! Ta ciccibo ta ta tashi zaune kamar wacce ta shekara tana ciwo saboda tsabar fita hayyacin da tayi Tausayi ya lullube antyn a hankali tace kinaji na? Ga alamin cen ya kira waya don Allah ki fidda mu kunya ki tashi ki je ki saurare shi badon mu ba sai don girman Alkawarin da kika daukar masa kafin ya tafi tashi kije kudinsa na bin iska kinji? Tamkar antyn na magana da dutse don ko motsi batayi ba sai idanuwa ta ke ambaliyar ruwan hawaye . Haushi da takaici suka rufe yayanta ya daka mata tsawa mai tsanani sai ta zabura bazaki tashi ba? Alamarin ya kara kure su cikin mamaki sukaji wannan kalmar ta fito bakinta Nifa yaya ba zanyi magana da kowa ba Gaba daya suka ware ido baki sake sai dai shi soja baya tsayawa yana kallon raini don haka ya cira hannu ya tsnke ta da wawan marin da yayi sanadiyyar daukewar numfashinta karkaf,ta zube sumammiya ya nuna cikin zafi yace ni zakiyi wa rashin kunya ba na wasa da ke ni zan iya karya ki wallhy anti amina da tuni take kwasar salati tace ai maganar karyawa ta kare tafa suma yallabai yanzu me za a cewa Al'ameen din Yace ta mutu ni tayiwa rashin kunya bata isa ba wallahi!Mtsw"ya ja dogon tsaki ya bar dakin falon ya sauka ya dauki kan wayar ya kanga wa kunnensa hello al'ameen naji na ya amsa ina kinka yaya yace kayi hakuri da mama al'ameen ya katse shi me ya faru yaya ina take yace ta suma al'ameen kayi hakuri da ita domin mama ta riga ta sami matsala....". Ya sauke salati ya katse shi yaya bazan
Chapter 32 · 0% Book details