Sashe 77
Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bai iya cewa komaiba.sai yayunta ke mata fada tareda sawa auren albarka.kamar wasa sai yazama dakyar aka banbareta daga jikin abba.takoma dakin ummanta takifa kai ciki.kukan rashin ummanta takeyi.jitayi anzauna kusa da ita muryar yaya ali taji yana fadin kiyi haquri kitaso mama!kowa yashiga mota ke kadai angonki ke jira!nanda nan tadago ta dubeshi duk idanuwa sun kode jajir!sun qara fitowa waje. 153.yasake fadin pls.ki kwantar da hankalinki ki taso a fita dake,,kin san hanya ba kyau ko?batace komaiba.ta tashi zaune ya miqa mata hankici yace share hawayenki!ta karba ta share ya gyara zaman mayafinta ya rufe mata fuska.sannan yakamo bakin mayafin yajawo ta falo.inda su anty amina ke tsaye cirko cirko.yace gatanan na fiddo da ita.ku muje nizan sata a mota.ya wuce anata musu dariya.wasu na guda.makekiyar jeep din sabuwa fil!itace angon ya tanada don amaryarsa.yaya ali yasanya ta aciki.inna saude da baraka tare da zainab da anty amina suka take mata baya cikin motar.gabadaya motoci suka tashi aka jera kamar an rako shugaban qasa.sun iso minna karfe biyar da rabi na yamma.akwai wasu kosassun dawakai guda goma dake jiran isowarsu.akan mahadar dazata shiga dasu anguwarsu..amarya da zainab suka hau biyu.sauran takwas din kuwa ango da abokansa cikinsu harda turawan da sukazo daga rasha.gaba daya sun daura alkyabba da rawani na alfarma.musamman alkyabbar amarya tafi kowacce ado.sai wanda ya gani suka tankaya makada da mabusan sarakunan lafai na gaba da bayansu suna qayata sha'anin.motoci na biye dasu ga jama'a suna tafiyar qasaita anata dauka da kamarori kala kala.tafiyar minti talatin takaisu get din gidansu.mami ta fito ta tarbi amarya da turarenta mai shegen qamshi.tana fesa mata anata rangada guda.sannan takamo hannunta suka wuce gida sauran ayari suka take musu baya.sashi na musamman aka warewa amarya da yan uwanta.babu abinda babu na nau'in abinci dasu kala kalar kayan sha.sun cika wani dan matsakai cin sito.sai abinda kake sha'awa zaka debo kaci. BAKIN CIKI 3***12 bayan anci abinci sallar la'asar aka gabatar data riskesu a hanya.bayan magrib da isha'i motoci suka sake kwashesu sai gidan amarya.wanda layi biyu kacal ne a tsakaninsu.dukiya taji jiki.irin dukiyar da aka zubawa mama agidan sai ka rantse da Allah baza a kwanta a kabariba.shikansa tsarin gidan abin kallo ne.bayan yan rakiya sungama bawa idonsu abinci.motoci suka sake dibansu suka maida wajen mami.amarya kawai aka bari dan bawa ango damar hutawa da amaryarsa.ganin basuda isashen lokaci suma gobe lahadi zasu koma zariya.karfe tara ya raka bakinsa hotel dindaya kama musu.shikuma yadawo gida cike da zumudi maras misaltawa..ita kuwa amarya tuni tayi wanka saboda zafin datakeji.tasake caba ado ta qame tana ta zuba qamshi.kawai sallamarsa taji cikin dakin gabanta yayi mugun faduwa.ta amsa masa tanajan mayafi.yatako a hankali yazo gaban gadon ya zuba mata ido.tsawon lokaci sannan ya sauqe numfashi..yazauna gefenta ya duqa sosai.yaleqo fuskarta suka hada ido.tayi murmushi tasadda kanta qasa yayi dariya yace amarya kenan.yadauke mayafin ya zura mata ido.yayin da yake juyo fuskarta gareshi.ta dubeshi tana murmushi kafin tace sannu da zuwa!yace kezanyiwa sannu kin iso lafiya?tadan murmusa lafiya lau.yace to alhamdulillahi.dukkan godiya ta tabbata ga Allah.daya nuna mana wannan rana dabamu taba mafarkin zatazoba.155.ya lalubo yatsanta ya runtse cikin nasa ya nisa sannan yaci gaba abinda nakeso dake shine ki kwantar da hankalinki muyi zama na amana wannan zama dazamuyi bana soyayya bane zalla a'a harda ibada.mudauka hanyar aljanna muke nema.ina fatan zaki zama mai bani hadin kai har qarshen rayuwarmu.ta dubeshi ido taf kwalla.tace insha Allahu zaka sameni mai sadauqar da rayuwata a gareka.tareda bin umarninka muddin bai sabawa shari'ah ba.kwalla suka sauqa bisa kuncinta ya zura mata ido sosai.yadan kada kai.meya kawo hawayen? yayi sauri yajawota jikinsa.no pls bansan dalilin wannan kukanba.murya shaqe tace farin ciki dokta! bantaba tsammanin zansamu nutsuwa kamar daba.azatona rayuwata tagama rushewa.amma sai gashi kanata hidima dani tamkar zaka auri.......yayi wuf ya rufe bakinta.bana sonji.kawai kiyi shiru idan bazaki fadi alheri ba.ta zuba mishi ido shima nasa sun fara kadawa.ya share mata hawaye.kinga tashi muje muyi alwala muyi sallah shine zaifi mana kyau.yaja hannunta yakai bayi fara yi ki fito.tayi ta fito.shida ya shiga sanda ya watsa ruwa tukun yayi alwar ya fito.ya jagoranci sallar raka'a biyu tareda miqa godiya ga Allah........ya juyo gareta tana miqe kafafunta saboda gajiya.yace in kwanta? tace kwanta mana waya hanaka?nazaci za a min irin na rannan ne a koreni inaji ina ganin abinda nakeso.tayi yar dariya.mesa baka mantuwa?yayi lum da ido!yace sharp brain.!ya qara bata dariya tace ai yanxu ban isaba,,,kayi kwanciyarka mai gida... .kawai taga ya yada kai bisa cinyoyinta kunya ta kamaata.ta kauda kai daga kallonsa.yasa yatsansa yamaida fuskarta.yace kalleni mana.mekike nufi da kauda kai?ta yamutsa fuska tace ina na kai shi? yayi dariya.wai naga har paracetamol kuka raba wai ku doctors ko?tace babu ruwana aikin baraka ne.tace alqawari ta dauka sama da shekaru biyar dole ta cika.gashi nima tasaka min ajaka dazu dazasu koma.yace kuma wlh ta birge har dr begas yasarawa basirarta.sai dai kun mance baku rubuta dose ba yakamata agayamana nawa nawa zamu sha?tayi dariya ai yawuce dokta.in,miqo maka kasha?.kawo min.tace to dagani.ya manne ido daya yace nanfa daya.ta watso masa harara.yayi murmushi.yace kinajin yunwa ko?takada kai.yace aikuwa ko bakiji yunwa dole kici tsarabata..tace dole?yace yazama wajibi ne yau inshayar dake madara inji manzon Allah.kinga kuwa dolene tayi shiru tana kallonsa kamar yadda ya zubamata ido.karfe biyar na asuba da kwata taji ana bubbugata a hankali tabude ido taga fuskarsa dafda tata.yasa mata ido za a iya tashi koda sauran gajiya?taja mayafi ta rufe fuskarta yayi dariya.yasa hannu ya yaye rufuwar.ta mulmula ta dirqa tadayan side din tafada bayi.yanata dariya sannan yanufi sallaya yatada kabbarar sallah.157.yayi nafila kana yakawo farali.kafin ya kammala tafito ta kintsa ta daura hijab.ta fara sallah.sai da ta kammala tsaf harda azkar din safe.sannan ta juyo ta dubi inda yake.yana kwance bisa shimfida.yasa hannu yayi kiranta.ta miqe ta nufi gunsa ta zauna gefe sannan tace ina kwana? yatashi zaune yabita da kallo yace qalau na kauna kefa?tace nima yace da kyau!kinsan wani abu?ta girgiza kai.to rufe idonki.tayi murmushi ta rufe.cike da annuri.ya tura hannu qasan filo ya zaro dan mukulli.yakamo hannun damarta ya damqa mata.bude ki gani.ta bude ta bishi da kallo dan mukulli nagani.yace hausawa sunce yaba kyauta tukuici.wannan shine tukwaicin kyautar kanki daki ban jiya.wata yar mota ce kiyi maneji.kanta yayi gingiri gin dokta shine......ya nuna mata alamun tayi shiru banson ji ok?ta wuce jikinsa ta qnqame.ban cancanci wannan ba dokta!don Allah kadaina wahalar da kanka akan......ya daka mata tsawa akanme? nace akanme? ta gigice cikin kuka ta kasa magana yace wallahi! wallahi!!wallahi!!!idan kikasake aibanta kanki ayau zan barmiki qasarnan.sai ranar da kikayi hankali zandawo.kina jina?haba!jiya jiya fa kika min alqawari? kina nufin abaki ne kawai?to wlh bazan dauka ba.bazan jure jin lBAKIN CIKIN Lafazinki susa min hawan jini ba.kin gane? tafada jikinsa ta qanqamesa sautin kukanta na ratsa kunnuwansa.shiyasa zuciyarsa taci gaba da tafarfasa..don baison jin kukanta sam.haka kuma bayaso taci gaba da aibata kanta.abinda yafii tsana da kyama kenan.dan haka ya kyaleta taci gaba da zubda hawayen.amma yadda ta qara qanqamesa kamar zata shige jikinsa.shiya tabbatar masa da lalle haquri take bashi dukda bata furta da bakintaba. hakan yasa fushinsa yadinga sauqa harya rabu da zuciyarsa.yabar masa tausayin amaryarsa kawai..ya tallafo kanta yasauqe numfashi ya sassauta murya.tun ranan da Allah ya hada ni dake ya manna min matsanancin sonki a zuciyata har rana mai kamar yau. Banji sassauci ba.duk wani abu dakikaga nayi a halin yanxu dama shiryayye ne.tunda mafarki nane kawai yazama gaskia.karkiyi mamakin irin tarairayar da zanmiki cikin zaman da zamuyi.kiga kamar shekaruna sun wuce hakan.ni a wajena dole inyiKARA'IN Soyayyarki.duk abinda na shirya mana a farko sai na nuna miki.tunda ubangiji ya nufeni da mallakarki.idan kuwa shekaru basu hanani dawowa yaroba.banga dalilin dazai hanani aiwatar da abunda nayi niyyaba.don faranta ran wacce ta faranta mini,,,,,ya dago fuskarta idanuwa sunyo jajuz.yaci gaba pls kidena kona zuciyata da zafin hawayenki.ta zura masa ido na tuba dokta!yayo dan murmushi amarya bata lefi. Kota kashe dan masu gida.tace gara da kace wai.ya goge hawayenta baki yarda ba? yanxu ki kamo waleed ki yanka ai babu abinda zanyi.illa in miqo miki waleeda itama ki yanka duk cikin nishadin amarci ne.159.tace Allah ya tsareni nazaama mahaukaciya kenan!ba amaryaba.karka sake min irin wannan misalin ya lakucr hancinta nima karki sake min asaran hawayenki.tace idan bakason hawayena kadaina min hidima..ya dubeta yace uhmm....to shikenan nadena.tamiqa masa yatsanta promise? yace bawani promise.karkiyi mini wayau maman waleen.ta watso masa harara.yafara dariya ai gaskia kisan nanda watanni tara zuwa goma zaki haifi ameer ko ameera.kinga kuwa hidima takama babab waleed da waleeda uba awajen ameer da ameera.ta shagwabe fuska takai masa duka a kirji.ya kece da dariya yakwanta a filo yana kallon shagwabar datake masa.zaka dace da roqo tace masa wannan irin kirari?yace eh bandeji haushiba..tayi dariya ta lallabo jikinsa nagode dokta Allah qara budi na halas!ya tallafota ameen bebina.abinda kawai nakeso ki rinqa fadi kenan kinji?tayi far da ido insha Allahu.good sai gari yawaye muje kiganta tana motor park.ta dada shigewa jikinsa double thank sir!sir sis!?babu sir a wannan gidan daga darling sai cweethrt sai honey. Sai sugar da mazarkwaila.ta fashe da dariya tana kada kai.yaci gaba da nishadantar da ita tuntana ji har bacci mai dadi ya saceta.shikuwa farin ciki ya hanashi bacci gani yake tamkar a mafarki.wai yau shine tare da sakeena?kana ya aje numfashi yace Allah nagode maka. I60.qarfe takwas da rabi wayarsa dake silent take hasko wa alamun ana kiransa.yasa hannu yadauka mami ce take kiransa..yayi sauri ya amsa sannan tagayamasa direba nanan zuwa da abinci safe.yayi godiya suka kashe wayar.ya dubi mama dake kokarin tashi zaune na tasheki koh?tayi lum da ido takada kai dama yakamata intashi.kiyi me?tace inyi wanka inshirya.kafin baqi su fara zuwa.yace gaskia ne mami ne takkira waya wai direba nanan zuwa da abinci kafin ya iso jekiyi wankan tace to.ta sauqa tashiga bayi ta tsalo wanka tadawo baya dakin.taci gaba da shirinta.kafin wani lokaci tahade kanar sarauniya.tafar a gyaran gado kenan taji sallamarsa shima yahade.da jar shadda mai duhu suka zubawa juna ido sannan tayi murmushi tajuya taci gaba da aikinta.ya matso yakama yana tayata.yana fadin kinkalleni ki dauke kai.banyi kyau bane? tace aidama kai mai kyau ne dokta!rudewa nayi nakasa magana.ko?kamar yadda nima na gigice? aida kika waigo kiris ya rage na zube qasa.sai kuma kika dauke kanki.tace ashe na taima keka?yayi yar dariya kintaimaki