← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 79

Sashe 41

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya kau. Al- ameen sakeena ta gudu tun jiya babu wanda yasan inda take saboda haka nake rokonka arziki da ka kwantar da hankalinka, kayi imani da furucin da kayi daxu, Allah ba xai bari kasha wuya ba. Ya Dubi Mami fuska kunshe da tashin hakali yace mami ban fahimci ta gudu ba? Me dady yake nufi? Tace iyakar kiyayya sakeena ta nuna maka, tunda ta xabi ta dauki akwatinta ta bar gidan iyayen ta ada ace ta aure ka. Ta xabi ta ci mutuncin mahaifanta akan auranka. Wulakanci ya kai makura Al-ameen, ya kamata ka nuna mana ka haihu dan halas, kace kai ma ka hkr da sakeena. Ya xura mata ido, du sun kadu, mami kina nufin an fasa daura auran gobe? Tace abinda Abbanta yayi sammakon xuwa shaida mana kenan, ia ske ba ku nan kun riga kun tafi gayyata, ni na bi dadynka Lafai na dakatar da shi. Kai ma ina so ka dauki waya ka kira abokin ka dr. Lawal ka gaya masa an fasa, don ya gaya wa saura kar su yi wahala. Ya kada kai yace, baxan iya ba mami, na rantse da Allah sakeena na so na, ina xata gudu taje? Ban yarda ba mami sace min ita kayi, don a raba mu.... Rufe min baki! Mami ta daka masa tasawa mai karfi, daga nan ta balle da masifa, kar ka yarda Al-ameen, amma ina son ka sani, babu maganar auranka gobe da sakeena! Idan kuma ka sake tak a wurin nan sai na tsinka mata mari, don ka gane ba wasa muke yi da kai ba! Yaya ana rarrashinka ana numaka gaskiyyar magana ka naso ka akrya ta mu? Sakeenar banxa sakeenan wofi? Ita kadaice mace a duniya? In sake jin xancen ta abakin ka sai na saba maka! Ku ma ka sani, daga daren yau ka fara shiri gobe xuwa jibi xaka koma sch! Kaji ko baka ji ni ba? Ya aje kai kasa. Dadi yasa hannu ya dago fuskarsa. Tuni hawaye suka wanke masa kunci, shi ya fara fadin, me yasa zata gudu ta barni Dady? Ko baxan hkr da ita ba, ai bai kamata ta gudu ba, hatsari ne babba ga diya mace, wa ya san hannu da take yanxun? Mami tayi caraf? Ta cafke, tana hannun wanda take so. Dama ka daina bata hawayenka a banxa. Sannan kama kunnunwanka da kyau ka ji ni, tun daga ranar da ka daina jin muryar sakeena awaya ta daina sonka, ta mance da kai, ta share ka a rayuwarta. Saboda kin da ta ke ma. Sakeena ta diro daga mota, da abin ya zo da karar kwana da yanxun an kusa mata sadakar arba'in. Sakeena tayi kwana da kwanaki tana yajin cin abinci, tayi ta suma ana mata karin ruwa a asibiti. Kai saboda kiyayyar ka, gabada dabi'iun sakeena suka sauya, bata gannin kowa da daraja, nballe ta saurari fada, da iayeynta da 'yanuwanta ke mata ba dare ba rana. A karshe sakeena ta aikata abinda yafi komi muni akan diya mace. Duk saboda bata sonka, ashe ya kamata ka hankalta kasan halin da kake ciki, don kai ba yaro bane, kuma ba alfahari ba, ilimi muhammadiya da boko sai dai a yiwa wani gori ba dai kai ba Al-ameen, duk kuma wanda yayi imani da kaddara, baya tabewa Al-ameen. Ka maida al-amarin ka wajen Allah shi xai maka magani. Ya dube su daidai tamkar karamin yaro, murya na rawa yace, gaskiyya ne Mami, duk abinda ki ka fadi na yarda, kuma na hkr da sakeena, sai dai son ta ba xan iya cire shi cikin raina ba, saboda ba ni na aje shi ba, kuyi hkr, ku yafe ni, idan furuncin danayi ya muku xafi, sannan ina rokon ku don Allah da son Manxonsa, kar ku kullaci sakeena cikin xukatan ku akan wannan maganar. Wlh har yanxu ina ji ajikna sakeenna tawace. Dady ya rungumo kafadunsa yace, shikenan,ya Isa, munji rokonka mun amsa. Zamu cigaba da taya ka addu'. Yanxun abinda nake sonka da shi shine, ka kira Dr. Lawal ka gaya masa, don su sani. Sai dai in baka lambobin ka kira shi dady, bakina ba xai iya furta mummunan labarin nan ba. Ya mike ya jao durowar dadi ya dauki biro da paper ya rubuta ya bashi, ya mike xai fice, ya kusan kaiwa kofa mamy ta kira shi, ya juyo tace kayi nafilfilu cikn dare. Allah zai saurareka, ya nisa kafin yace xanyi mami. Ya sa kai ya fice. Mami ta dubi dady ta hadiye hawayenta, tace gobe in Allah ya kaimu xan koma Lafai wajen baba liman in samo masa ruwan addu'a ya sha ya sami sanyi cikin ransa. Yace hakan ma yayi, Allah ya sa mu dace. Tace amin. Ta jawo wa dady kan waya ya nemi Dr. Lawal, ya sanar masa. Yace an fasa? Subhanallahi? Wannan abu baiyi dadi ba. Don girman Allah dady a samu a daidaita, wlh Al- ameen yana son yarinyar nan ba kadan ba. Ya ce ba sai ka rantse ba Lawal, ni kaina nasan hakan, amma fadan da ya fi karfinka dole ka maida shi wasa. Mu nan muna ta addu'a Allah ya zaba mafi alkhairi. Ya numfasa, yace amin. Ina Dr. Yake? Ai sai da ka neme shi xuwa gobe, yanxun kam babu sukuni yana dakinsa. Yayi dan jim, kafin yace Allah shi kyauta, amma ayi kokari Dadi idan xai yuwu a sasanta. Ba komai mun gode a gaida Iyali. Zasuji, ya aje wayar tare da tsananin mamakin wannan abu? Me ya faru haka da xafi? Haka ya kwana da tambayar kansa, don babu alamar wata mishkila a tattare da soyayyar abokinsa da sakeena, ko daya zo sanar da xancen auran ma babu alamat akwai matsala babba. Labarin barci dai babu shi a wajen Al- ameen kuma xuciyarsa bata daina karyata masa xancan ba. Ko alama ta ki amsar sakon, saboda tsabar shakkun da yake ciki, wai sakeena taci amanarsa? Har 8am yana kan sallaya, ba don wai yana sallah ba, a'a kasala ce ta hana masa tashi. Mami tayi sallama ta shigo da tiran kayan karin safe. Ya xubo mata ido. Mami tayi sallama ta shigo da tiran abinci, ya xubo mata ido, ta aje a agbnsa, ta xauna gefe, sannan yace, ina kwana mami? Lfya lau, ina fatan ba ka tsananta wa kan tunani ba? Ya kada kai, ya xanyi mami? Kin san ba yin kaina bane? Ta dafa shi a sanyaye, kllm ina kara gaya maka Al-ameen, kai kadai ne garemu, kuma ka zama tamkar dubu, ba gare mu kadai ba, gabadaya al'umma za su so rayuwarka ta daure cikin fciki da walwala, saboda muhimmancinta, ina so ka san wani abu yau. Wlh na yi maka rantsuwar da ba kaffara da rayuwarka ta salwanta, gara ni in mutu, don na..... Ya rufe bakinta, a hankali, idanuwansa taf, da hawaye yace, kiyi shiru mamina! Da ni dake zamu rayu da yardar Allah cikin farinciki da kwanciyar hankali. Har ga Allah na hkra da sakeena mami, kawai ciwon fitar son ta ke azabtar da ni. Ka kwantar da hankalinki mamina, a hankali zaki gan ni yadda kike so. Tayi dan murmushi tace, Allah yayi ma albarka! Da sauri ya kwanta a kafadarta yana fadin amin mamina. Zauna da kyau na hada maka brkfst. Kaga masa na sa iya ta shirya maka da sassafe, na san kana so kuma kana kewarta, don ba'a samu a Rasha. Ya bita da kallo dauke da tausayi. Yace nagode mamina, amma tare xamu ci ko? Ta jawo fileta tana fadi ah! Me zai hana? Bari ka gani. Ta loda waina a plate tana xuba miya ya ware ido, yace mami kin cika abincin nan! Ita ma ta ware idon tace injiwa? Ni da kaine fa? Sa hannu ka gani ko asa man shanu? Ya kada kai, a'a kinsa banso kayan karni. Ka bar dadi yaro. Yayi 'yar dariya yace Allah ko? Ta tura masa a baki tace, haba ai ba sai na fadi ba. Dady yai sallama dakin ya karaso da sauri yana cewa iye! Masa kuke ci kuka nuna min 'yan ubanci? Gaskiya ba ha akeyi ba, ai sai ku kira ni ko? Ya tambaya yana kallon al-ameen cikin ido. Ya gayara masa wwuri, yace laifin mami ne, xauna abinka Dadyna. Ya xauna yasa hannu ciki, yace ai mami akwai rowa, Allah dai ya tsaga da rabona. Suna dariya ta bashi amsa, ka san kuwa da na kawai, na aka yi ma. Kaji ko? Tafi son ka akaina. Yayi wuf ya rike hannu da yake kokarin kai loma yace, ba xaka ci ba sai ka fadi! Gaya min, mami ta hau dariya shima ita yake yi. Dady na ga dai da ta rikice kanka. Tace babu wani sai kai, sannan aka sameni, ko ba haka bane mami? Tace ni xaka tambaya? Dady ya karbe yanki wainar daga hannunsa ya tura masa baki, yace cinye dana, ka bani amsa daidai. Bai gama cinyewa ba ya dauko cinyar kaza ya tura msa, ka ra da wannan kayi brush! Duk suka sa dariya, ganin al-ameen na neman kwarewa, kan kace kwabo sun yaudari Al-ameen ya cinye wainar da mami ta zo da ita, domin dai shi suka yi ta turawa da wasa da dariya ya take cikinsa. Bayan sun kare, mami ta dube shi tace yanxun ka tashi ka shiga wanka ka kimtsa, muje asibiti ka gaida Umma.... Umma? Me ya sameta? Tashin hankali ya sa ta sami hawan jini tuntuni, maganar jiya kuma ta kara birkita ta jininta yayi mugun hawa. Tana nan asibitin sun bata gado. Jiyan abba ya taho da ita. Ya marairaice yace, Umma na asibiti tun jiya baku gaya min ba? Ban dadin hakan ba, dady yace kayi hrk, ganin kai ma baka da sukuni ya sa muka kyaleka, kaji da guda 1. Ya mike yace ba sai nayi wanka ba, yanxun xan tafi, idan na dawo nayi, bai saurara ba ya wuce ya jawo dirowa ya dauko key ya fice. Mami ta biyo shi tace Al-ameen, ya tsaya cak! yana dubanta, ta matsi sosai ta dafa shi, ka tafi a hankali, idan kaje kace ina gaishe ta, ni ma xan biyo in na dawo daga Lafai, ya dan lumshi ido, ya bude yace xan kula mami, amma
Chapter 41 · 0% Book details