← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 79

Sashe 30

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kuma kuyi mata addu'ar. Yace, na yarda da kai Ali, amma ban yarda auran kowa ba, sai wanda na aminta da shi. Zan gani idan ita zata daura wa kanta aure ko mune? Yace, haka ne Abba don Allah ina rokon 2mins in ishiga in dayi mata nasiha, koda bazata saurere ni. Ya suke numfashi yace, shiga Ali, Allah ya sa taji abinda zaka gaya mata. Ya aje jaka ya wuce cikin dakin. Tana kwance niyyar barci ma takeyi, kamar yadda Danliti ya umarceta. Yana shigowa ta runtse ido ta juya baya, ya tsya kanta yace, komai zakiyi, dole in gaya miki gaskiyya, tunda kunnuwanki naji..... Fadan hakan yasa tai sauri ta toshe kunnuwan nata da yatsunta. Yace aikin banza kike yi Mama, kuma rayuwar ki na cikin hatsari, muddin baki daina jefa su abba cikin BAKIN CIKI ba. Menene anfani abinda kika aikata yanxu? Ki kashe kanki a banza da wofi, ba asarar Danliti bane, don na tabbata duk tsananin son da yake mi, ba zai hallaka kansa ya biki ba. Ki nutsu kiyi tunani. Akwai abinda magabatan mu ke hangowa kan wannan ra'ayin naki. Ni zan koma kuma ina fatan zanji canji daga gareki? Ya juya ya fice bata re da ta daga kai ta dube shi ba. Wani dogon tsaki ta raka shi da shi, wanda ya tilasta masa juyowa ya dubeta ji, sannan ya karasa ficewa. Ya dauki jakarsa ya kara yiwa su Abba sallama, ya bar gidan ciki da Al'ajabin maras misaltuwa a zuciyarsa. Bayan tafiyarsa, su Umma suka shigo gunta ta tana kudundune ta dunkule wuri daya, ko 'ina jikinta ciwo. Umma ta zauna gefen gadon shi kuma Abba n atsaye kanta, yace Mama barazanar kashe kanki ba zai sauya abinda ke cikin raina ba, idan ma baki sani ba, ki sani gara ki mutu da mutunci na ya xube a idon duniya. Saboda haka fadowar ki a mota bata girgiza ni ba balle ta cire daidai da kwayar zarra na alkawarin da na daukarwa Al- ameen da iyayensa. Mu zuba ni dake, duk wani matakin rashin kunyar da kika hau, ni na fi ki hawa matakin karshe! Ya juya ya bar dakin. Umma ta kura mata ido, hawaye suka cika idanuwanta, tace Mama zaki iya tashi ki saurare ni? Ta shiru bata motsa ba, ta sake fadin, idan har ni na haifeki kuma na isa dake, to ki tashi zaune ki fuskance ni. Ta jima kafin ta yunkura ta tashi fuskar ta sharkaf da hawaye, kamanninta sun sauya, saboda fitinar da ta daukarwa kanta a tunanin iyayenta. Umma ta zura mata ido, kafin tace, nasiha xan miki, idan kiji ki dauka wahala ta kare miki, idan kuma kince ba haka ba to rayuwa zata cigaba da yi miki kunci, domin Allah ne ya wajabta miki yi mana biyayya, muddin ba mu sa ba masa. Ban jin akwai wani dalili ko hujja da xaki gayawa ubangiji da ace kin mutu sakamon bude murfin motar da kikayi, ki fado lasa. Wannan ya nuna muraran kin kashe kanki ne da gan-gan. Ma'ana kin mutu kafira. Me zai jawo miki wannan masifar da hankalinki da komai? Ko kuwa kina so ki nuna mana kin fi karfin mu cikin dan kankanin lokcine ne? Kina nufin mu sanya miki ido ki zubar da mutuncin ki da mu a garin nan? Ban taba tunanin Mama, ke din nan zaki zama kaza kici share baki a game da irin so da Kaunar da Al-ameen da iyayensa syka nuna miki. Haka kuma ban taba mafarkin ke din nan zaki iya hango wani da namiji ya rufe miki ido har kice kin fo sonsa akan Al-ameen. Kina nufin daman can yaudara sa kike yi ba tsakani da Allah kike sonsa ba? Har yanxun mafarki nakeyi Mama, don ba gaskanya abinda yake shirin fitowa daga gareki nake ba. Ki yiwa girman Allah kir ki bari wannan magana ta zama gaskiyya, ba ke kadai za'a zaga ba har damu iyayenki. Na mu ma zai fi yawa saboda mune muka isa dake. Yanxun abinda na rokonki shine, ki share hawayen ki ki gaya min, laifin me Al- ameen yayi miki kike son ki katse masa rayuwa? Gaya min daga ni sai ke ce a dakin nan kuma share hwayenki, muddin shi ne baida gaskiyya. Ta shre hawayneta wasu suka xubo mata, kalaman ummanta masu taushi ne dashiga xuciya, amma kash Danliti ya riga ya gama da ruhinta. Allah ya bashi sa'a ya kamata ahannu, idanuwanta ba sa ganin kowa sai shi, kunnuwanta ba sa sauraron kowa face kalaman yaudarsa da izgilanci. Dalilin da yasa kenan kalma daya bata tasiri a hrt dinta, a duk tsahon jawabin da Umma tayi, da ka dubi fuskarta, zaka gane bata yarda bane kawai. Murya cunkushe tace, ni babu abinda Al'ameen yayi min Umma, kawai raina yafi kwanciya da Danliti kuma shi nake so na aura. Haushi kamar ya kashe Umma ta mike tsaye. Tace, to baki isa ba! Mu dan Liti baiyi mana ba, idan kina da wasu iyayen da za su dauta miki auran to bismillah! Ya ci gaba da fadin, ai kuwa bata isa ba, ni zanje in dauko ta kuma dole ta auri wannan yaron tunda itace tace tana so tun farko! Yace, Yaya duk yadda kake tunanin al'amarin nan ya wuce nan, amma ka gwada ka gani, kilan kai tafi jin tsoronka, sai dai kafin nan xance Al-ameen din ya kira ka, kuyi magana, don ni gaskiyya ban san me xance masa ba. Yace ba wani abu xan rarrasheshi, ya kwantar da hankalinsa, kaima yaunxun nan ka kama hanya kaje ka yiwa Hajiyansa bayani, kace kar su damu ba wata matsala bace babba. Ya numfasa ya amsa da to kawai. Lallai babban yaya yana dau kara abin wasa ne. Suna aje waya Aunty amina ta nufo shi, me ya faru ne wai? Nan take ya labarta mata abinda ke faruwa. Tun kafin ya kare idanunwanta ke waje, wai kana nufin Mama ta fasa auran Dr? Yace gara da kikace wai, don bata ida ba. Ni xan je na dauko ta, cikin gidan nan zata zauna sai ya dawo. Ta kada kai cikin damuwa, tace amma mama ta ban mamaki, me Dr? Yayi mata? Babu abinda yayi mata, wani ta hango saboda rashin hankali irin naku na mata da butulci! Tace wlh na yadda sai dai matsalar banyi zaton haka ba daga wajen Mama ba ganin yadda take nunwa Dr. So mai tsanani, duk yaudara ce, kai gani kuma a zahiri ai ta nuna. Amma ai tayi kuskure ni zan gyara mata zama, don bata isa ta zubda mana mutunci ba! Tace gaskiyya ne. Allah yasa ta gane. Ya wuce tebur don cin abinci. Shi kuwa abdulkareem, bai sami zaman cin abincin ba gidansu Al-ameen ya nufa ba tare daya san wane irin bayani xai iya yi masu ba, don hankalinsu ya kwanta. A haka ya isa gidan. Nan da nan aka tarbe shi da girmamawa da abubuwan kusa da baka, marafa baya gari, saboda haka mami ce ke tare da shi, ina fatan dai kaci abinci? Yayi dan yake yace, Alhmdlh Hajiya, nagode. Tace amma dai ko Juice kasha ko? Haba, kamar wani bako? Yanata murmushin rashin nayi, yana kallo ta xuba masa ta mika masa, Ungo sha don Allah. Kuma maimakon kazo min da surukartwa, yau in riketa cikin gidan nan sai tayi min sati. Ya aje kofin lemo ya kara gyara zama, Yace Hajiya, hkr na zo in baki, domin ban sami dawowa da Mama ba,... Saboda me? Kodai maganar Al-ameen gaskiyya ce, sakeena na cikin wani hali? Bata da lfya ko? Ya karkada kai.... Tace karka bote min komai Baban ameer, duk tsananin da sakeena ke ciki, nasan yadda xan rarrashi Al-ameen don hankalinsa ya kwanta. Gaya min me ya faru da ita? Jikinsa ya kara sanyi, cikin taushin murya, yace Matsala ce babba Hajiya, wacce ni kaina ban da ita ba, sai da naje daxun. Ashe tun komawar ta gida, wani yaro ya hure mata kunne, shi ya hana ta dawowa. Su abba na ta fama da ita kuma suna kan kokarin su don ganin raba ta da shi. Na yi nayi ta biyo ni, taki hajiya, shine Abba yace in zo in baku hkr kafin yazo. Insha Allahu za'ayi maganin abin. Gaba daya hankulan mu atashe suke, al'amarin yana daure mana kai. Idanuwanta xuru akansa, hannunta bisa kunci. Tace, wyyo Allah! Wayyo Allah! Me xanji yau mai kama da almara? Ta goce da sallalami, yanxun baban ameera kana nufin sakeena tace amanar Al-ameen kenan? Idanuwanta suka cika da kwalla, yayi da yaya Abdul ya kara kasa da kansa. Yace, kiyi hkr Hajiya, a gaskiyya ban san yadda xan fassara wannan al'amarin ba, amma abinda nake so ki gane Abba ba xao rungume hannayensa ya sanya mata ido ba. Haka muma 'yan uwanta. Muddin kuwa tana son albarka dole tabi umarnin mahaifinta. Shi yasa ya fara turo ni kafin ya zo da kansa ya ga alhaji. Haka kuma ku rarrashi Al-ameen ya kwnatar da hankalinsa komai zai daidaita cikin hukuncin Allah da yardarsa. Ta cire tagumi. Tace, a gaskiyya ba zan iya fuskantar Al-ameen da wannan maganar ba, in katsa masa karatu. Na san ya damu kwarai ya san halin da sakeena ke ciki, amma ba xan iya gaya masa wannan mummunan labarin ba, kuma na rokr ku don Allah ku kyaleshi kawai. Gara abar shi cikin duhun da agaya masa sakeena ta sauke alkawarin da ta daukara masa. Na tabbata komai nasa zai tsaya jarabawar su gab take da xuwa. Ni da kaina xan iya xuwa na roketa, ta tausaya wa Al-ameen karta kashe masa zuciya. Kwalla masu zafi suka xubo bisa kuncinta bata re da saninta ba. Hankalin Abdul ya kara tashi, BAKIN CIKI ya dada lulluba shi. Don girman Allah Hajia karki xubda hawayenki akan maganar nan. Da yardar Allah komai zai gyaru. Kamar yadda kika ce kar agaya masa ba, ba za'a gaya masa ba. Gara ace masa bata da lfiya ne, xuwa lokacin da xa'a shawo kanta. Ta goge kwallah, tace ina ganin hakan zai fi sauki iyaka dai yayi tunanin jikinta, mu kuma nan mu rinka gaya masa tana samun sauki. Yace, to shkienan, Allah yasa mudace. Don girman Allah hajiya kuyi hkr, sakarci ne kawai
Chapter 30 · 0% Book details