← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 79

Sashe 26

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

nan ya bata umarnin taje ta bincika,ai bata bata lokaci ba,cikin tsakar ranar nan ta kama hanya ta nufi gidan uban dawaki.Umma na daki tare da abban shi ma shigowarsa kenan gidan aka gabatar masa da abincin sa yana ci.-Inna ta shiga suka gaisa sannan suka koma dakin umman.Bayan sun gaisa da en hirarrakin zumunci kafin tace.magana ce tafe dani yaya amma ki duba ko alhaji ya gama cin abincinsa zan so in fade ta a gabansa."Nan take jikinta ya mutu,tace me ya faru saude?"To magana ce data shafi mama na rashin jindadi shiayasa nace ba zan bari ta kwana ba dole in zo in bincika,sai dai alhaji shi yafi dacewa ya sani,tunda nayi sa'a yana nan.Tayi dan tagumi......Subhanalillahi!Bari in yi masa magana.Ta mike jiki a salube ta shiga dakin abba ta iske ya kammala tace,wai magana ce tafe da saude idan ka gama ka taso muje,To muje gani nan".Ta gyara zama ta maida musu abinda baraka ta gaya mata umma ta shiga tafa hannu,abba kuwa sai daya mike."Kar dai ace shi ne yazo jiya da daddare?Lallai biri yayi kama da mutum,ina maman take? Umma ta dube shi ido taf da kwalla,tana daki. Kira min ita!Ta mike ta fita,har suka dawo tare babu wanda ya tanka sbda tsabar mutuwar jinin jikinta,a darare ta karaso dakin tana fadin,inna sannu da zuwa."Ta zuba mata ido,ke ma sannu."Ta gaishe da abba da umma na mata kallon mamaki,ta dube shi suka hada ido,tace abba ga-ni" yace,wanene yazo gun ki jiya?Ta sunkuyar da kai,tayi shiru,ya daka mata tsawa,ko baki ji ne?Nace waya zo gun ki jiya? Tana rawar lebe tace dan- liti?"Kin kuwa san ko waye danliti a garin nan? Tayi shiru,mama ni kike so ki mayar tsohon bnza,ki tozarta?jiya me na gaya miki?To ni ba hayaniya na kira ki mu yi ba domin a iya sani na ke mai hankali ce,kin san abinda ya dace,kin fi kowa sanin cewa saura 'yan watanni suka rage bikin ki.Sannan idan kika nutsu kika yi tunani ba mutuncin mu bane daga ke har mu ace an gan ki,kina karakaina a shagon wani ma,balle danliti sbda haka nake umurtar ki daga rana mai kamar ta yau,bana son in sake jin wani labari makamancin wannan!Ina fatan kin fahimce ni?Ta kara sunkuyar da kai yayin da idanuwanta suka fara tsiyayar ruwan hawaye,umma ta muskuta ta karbe "kin bani mamaki ba kadan ba mama,wai ma in tambaye ki,me kike nufi da bin sa har shagonsa? Shiru babu amasa,umma ta cigaba,wannan katon sakarci da me yayi kama? A zaton ki abin birgewa ne yadda 'yan mata ke tsayuwa kofar shagon samari suna amsar abin hannun su?Ban taba zaton hakan zai fito daga gareki ba mama kuma mun saurara miki ne kawai sbda wannan shine karo na farko da irin haka ta faru!" Inna tace,kin ga gidan nan da dukkan jama'ar gidan dake cikin sa ana ganin girma da mutuncin su musamman mahaifnki,don girman Allah kar ki bari wani ya rusa wannan ginin,ya hure miki kunne ya kai ki ya baro,kin ji mam? Ta goge kwalla bata ce uffan ba,abba yace,to mun ci mun rufe anan bana son ki sake aikata wani abinda zai sa ayi miki zama irin wannan,kin ji ni? Ta amsa da kai tana goge kwalla.umma tace tashi maza muje ki dauko min ledar kayan da aka ce ya baki,a iya sani na dai baki da yunwar su,maza tashi muje!Ta mike da kyar umma ta tasa ta suka je dakin ta dauko ledar.Umma ta fizge cikin zafi tace,Allah yasa in sake gani ko ji sai kin sha mamaki!" Ta fice ta bar dakin,ta bar mama cikin tashin hankalin da bata taba jin irinsa ba,har inna ta gama zamanta ta bar gidan mama na aikin kuka a daki domin dai tamkar sun kara debo soyayyar danliti ne sun kara antayawa cikin zuciyarta.Ita wannan ranar da suke kwakwazon an sanya mata ta jima da manta saurayin ma balle ranar,ba shi a idon ta ko birnin zuciyarta.Al'amarin ya daurewa iyayenta kai,shin wai me mama take nufi da kukan ta? Tambayar zukatan su kawai suke yi amma basu da tabbacin amsa.Karfe takwas da rabi cif! Lokaci ne da motar danliti ke fakin a kofar gidan uban dawaki,kai tsaya ya aiko yaro a kira masa mama,abba na nan a falo yana gadin zuwansa don haka yace da yaron yaje yace tana zuwa. Umma ta fito masa da kullin ledar kayan kwalamar da ya ba mama Abba ya karba ya bi bayan yaro kamar jiya,yau ma yana harde jikin motarsa yana kada mukullai sai dai yau kananan kaya ke jikinsa,gaba daya ya firgita kofar gidan da kamshin turare.Yana hango uban dawaki tilasa ya gyara tsayuwa yana 'yan kame kamen gulma ko kafin ya karaso ya tsugunna yana fadin,sannu alhaji,yace yauwa sannu,ya sake fadin ina wuni? Lafiya kalau,mike abin ka,magana zamu yi,ya mike a hankali yana sunkuyar da kai kamar muminin gaske.Abba yace magana guda daya ce nake so zan gaya maka danliti,'ya ta sakeena na riga nayi mata miji,tuni aka sa musu rana har ma lokacin ya kusan zuwa da yardar Allah sbda haka ina rokon ka da girman Allah kayi hakuri ka nemi wata,daga yau kar ka sake zuwa gun mama don tana da miji,ina fatan ka ji ni? Ya dan yi shiru jim kafin yace naji alhaji amma nima ina roqon arziki ka bar ni in rinka zuwa muna gaisawa,tnda ba'a daura ba.Wlh..."Abba ya katse shi,ba zai yiwu ba danliti domin koda babu alkawarin wani akan mama kai kanka ka sani zai yi wuya ka sami auranta,sanin kanka ne kaf garin nan babu wanda ya san tushenka,kaje kayi tunani mana.Ya saki baki yana kallon abba ran sa a bace,abba ya mika masa keda yace ungo nan,yasa hannu ya karba kafin ya cigaba da fadin,abubuwan daka bata ne dazu tunda ba auranka zata yi ba bai kamata ta amshi kayan ka ba.Don Allah kayi hakuri ka nemi daidai kai,sai da safe.Ya juya ya shige gida abinsa ya bar danliti a tsaye. )Ya kara harde kafafuwansa yana irin murmushin mugunta,sannan yace ko banzo ba ita zata zo wajena,koda kuwa kasheta zaku yi ta dawo.Dama ai zuwan nawa na hure kunne ne ba wai neman nake da gaske ba."Yayi er budurwar dariya ya bude motar sa ya shiga ya sake fadin,sai ni dan gidan buzu mai shayi taba ni kaga tsiya da bala'I!Ya ba mota wuta yaja ya bar harabar gidan hankalinsa kwance.Sabanin mama da take ji kamar ta saci jiki cikin daren nan taje wajen danliti shiyasa tayi ta leken falo,amma kash!Abba da umma sun ki tashi har dare yayi sosai suna tattauna zancenta.Daren nan bata yi barcin kirki ba sbda bakin cikin an hana ta fita ganin danliti.Gari ya waye ko alama umma ta ki sakar mata fuska,sam abin bai dameta ba Allah- Allah take yi kowa ya kama gabansa,itama ta samu ta sulale,ai kuwa abba na fita karfe goma umma ta gama abnda take yi,ta dare gado kamar yadda ta saba barcin safe,mama ta gama caba kwalliyarta ta sadada ta bar gidan.Ta kwarara sallama kofar shagon danliti,ya taso cike da fara'a yana amsawa kafin yace,a zatona ke ma zaki juya min baya ne,har na fara shiga damuwa,jiya sam ban yi barci ba.Ta dube shi cike da tausayi tace nima haka danliti ko gyangyadi ban runtsa ba,me zai sa na juya maka baya alhalin na san cewa nima zan cutu? Ya zura mata ido a marairece yace,abbanki ya nuna baya so na ban san yadda zanyi da rayuwata ba sakeena,kar ki bari ciwon zuciya ya kama ni.Kwalla suka taru cikin idanuwanta tace ka daina fadar wannan maganar don Allah,in ka ga na rabu da kai to sai dai su kashe ni in daina numfashi,zuciya ta kai take so kuma bana ra'ayin auran kowa face kai." Kwalla suka zubo bisa kuncinta.Da sauri ya tauko sabuwar t鐭泂hu kware ta ya yago ya miko mata,"share hawayenki, ki daina kuka.Na yarda dake sakeena,amma mece ce mafitar mu? Ta dan kada kai tace, "zanyi tunani,ka ban dan lokaci kadan,zan samo mana mafita.'ya daga kanta ya fito ya gyara zaman benci.Yace zauna kiji Ta zauna gefe shi ma ya zauna ya fuskanceta sosai yace,me zai hana ba zaki gaya musu ni kike so ynzu ba?Ta daga ido ta dube shi,jim,amma ba tace komai ba,yace "kar kiji tsoron komai kai tsaye ki gaya musu ke kin sauya ra'ayi ni kike so,za'a yi miki tilas ne?Dole a baki wanda kike so,don babu wanda zai zauna miki da shi,idan kuma kina son in rasa raina ne shikke nan........Ta kada kai tace,"nace ka daina fadar rasa rai danliti idan ka mutu nima mutuwar zan yi.Ka kwantar da hankalinka insha Allahu a yau zan gaya musu na sami sauyi wanda hankalina yafi kwanciya."Ya dafe kirji,ya lumshe ido yace,kin sa naji sanyi cikin raina sakeena.Ya bude ido ya bi ta da kallo ya cigaba,idan kika yi min haka kin gama min komai sarauniya ta,ba zan cika baki ba sai mun yi aure zaki ga tsantsar son da nake miki,bana jin akwai wata 'ya mace a fadin duniyar nana da zata sami irin gatan da zan nuna miki." Tayi dan murmushi tace,Allah ya nuna mana,yace amin.Ya dan gyara zama ya sake gadin,"wai sakeena kin san cewa kin fi kowa kyau a duniyar nan?Ta saki baki,ido waje tace,duk duniya? Wlh duk duniya babu mace mai kyau irin naki,ta kada kai tana murmushi tace,"ka daina fasa min kai danliti,ni na san ban kai ka ba,ya washe baki ya nuna kansa ya9e "ni kuma? A'a ni dai kike son ki fasawa kan,ina ni ina ke? kin gan ki kuwa?kin ga wannan dan bakin naki dagwas ba karamin kashe min jiki yake ba."Ta sunkuyar da kai tana 'yar dariya ya bita da kallo yana shafo habarsa."Mama!" Muryar kawai taji anyi mata wani gigitaccen kira,gaba dayan su suka kalli mai magana,ta bi shi da kallo babu tsoro ko wata fargaba tace,ah! yaya ali! saukar yaushe?"Ya kara tsuke fusk,yace me kike yi anan?"Tace me kuwa?Ba komai,taso muje gida,kaje ina zuwa,"ina wasa dake ne? nace ki taso mu wuce." "Ta dubi danliti suka hada ido yace,tashi ku tafi sai wani lokaci ko?Ta dan numfasa ta mike ta wuce,yaya alin dake tsaye,ya bi ta da sauri ya sameta,"mama,wai mafarki nake yi ko kuwa gaske ne?Ta yamutsa fuska "da aka yi me?" Zaune na gan ki kofar shago
Chapter 26 · 0% Book details