← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 79

Sashe 35

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sanya tsananin kunci cikin ranta,ji take kamar ana hura wa zuciya ta wuta.Tsananin son ganin Dan-Lati da kewarsa suka hana ta sukuni. A yadda jiri ke dibar ta,sau uku tana fitowa waje ta tsaya wai ko zata ga lakwa-lakwa ta sulale ta gudu.Amma ina,ko fuska babu a wajen kuratan nan,balle ta sami hanyar fita.Don haka ta kifa ciki tsakar falo,tayi ta sharara kuka har azahar,bata san lokacin da barcin wuya ya sace ta ba. Anti Amina ta sauko tayi girki ta gama bata farka ba.Dawowar Malami ya kwarara sallama',shi ya tashe ta,tayi doguwar mika tare da hamma mai kunshi da yunwa da wahalar duniya. Ta tashi zaune taja jikin ta,ta zauna ta jingina da kujera,wucewar 'yan mintoci.sannan idanuwan ta suka kwalli agogo.karfe daya hard a rabi. Da kyar ta yunkura ta tashi ta haye sama a wahale,tana shiga dakin ta zube a kasa,sbd babu karfi a jikinta.Malami da ke cire kayan makaranta,ya zubo mata ido.yana so ya gaisheta yana jin tsoran mari. Ya sauya kaya,ya fice daga dakin,wajen Momin sa ya shiga idanuwan sa cike da damuwa. Ya zauna kusa da ita,tana kallon yadda ran sa ke bace,don hk ta rungumo kafadun sa tace, "Yaya dai,yunwa akeji? Ya kada kai yace, Momi Anti fa zaa mutu,ku maida ta asibiti.Allah bata warke ba. Ta zura masa ido,tace,Ba laifin mu bane Malami,a gaban ka ai kana kallo taki yarda asa mata Drip. To ya take so muyi?" Yace, kawai ku kira mata abba yayi mata fada. Wlh bana son Ant閾� ta mutu. Ina son ta Mom鐭�,me yasa take ta wannan ciwon ne? Ta kara rungume shi tace, kowa ma nason Antin ka Malami,kuma babu mai son mutuwar ta,Matsalar taki cin abinci ne,shi yasa ka ganta haka. To sbd me? Tace kaga ka yi shiru da bakin ka,kai yaro ne ba ruwanka da maganar manya.kai da鐭� idan ka yi sallah ka roki Allah ya bata lafiya. Yace, To Momi,tace. Maza kicin ka zuba abincin ka.'ya fice tana kallon sa. Zuwa karfe biyar Mama ta sake fadawa cikin mummunan hali,bata gane kowa. Anti Amina ta rasa inda zata sa ranta,domin ta rasa yadda zata yi da Mama don ta ceto ran ta. Ta sauko falo da nufin kiran wayar ofishin yallabai. Shigowar mota harabar gidan,shi ya dauki hnklnta ta zage labulan taga ta daga.Motar Abdulkareem ke fakin a harabar aje motoci,ta dawo da sauri ta nufi kofa cike da farin ciki da baya misaltuwa. Ta bude kofar tayi waje,farin cikin ta ya karu,ganin har da Abba acikin su. Sannun ku da zuwa! Ta isa wajen tana fadi. Duk suka amsa,sannan suka rankayo cikin gida. Malami ya rugo ya rungume Abba. Bayan gaishe gaishe suka tambayi Mama. Tace,tana daki babu kyan gani,nama fito ne,in kira dadin Malami ko za mu sake komawa asibitin ne,sai gaku. Wlhy Abba taki cin komai tunda suka zo garin. Ban jin tasa ruwa a bakinta,wannan masifa dame tayi kama? Duk suka yi shiru sbd takaici,babu wanda ya tanka har Anti Amina ta mike ta kawo musu abincin da ababen sha. Ruwa kawai suka sha Abba. Ya-ce, muje mu ganta. Duk suka rankaya saman. Yanayin da suka riski Mama,ba karamin daga hankulan su yayi ba. Abba ya zura mata ido,idan da zai hadu da ita a hanya,ba zai shaida ta ba,sbd sauya kamannin da tayi,sbd tsananin son cikawa al-ameen alkawari ko alama bai bar鐭� tausayinta ya rinjaye shi ba. Don hk ya dubi sauran yace,wannan ba shi zaisa mutuncin mu ya zube a idon duniya ba.sbd hk zamu koma da ita asibiti,ta farfado.sannan mu wuce da ita fandogari. Farin ciki na Mama ta mutu a dakin nauran al-ameen wanan shne kwanciyar hnkli na. Ku dauko ta mu tafi. gaskiya ne abba shi kuwa yaya abdul-rahman abin ne ya zame masa banbarakwai don bai taba zaton labarin da yakeji abin ya kai haka ba duk da yana jin zafin abinda mama tayi ,halin da idanuwansa suka gane masa mama a halin yanzu kwarai tausayinta ya kwanta a zuciyar sa shi ne ya fara kai hannu ya ciccubo ta suka taimaka suka sauko da ita kasa kamat matacciya,da kyar likita ya karbe ta sai da yan uwanta suka yita rarrshinsa sannan ya bata gado yayi mata duk abinda ya dace. Acan yaya abdul- kadeer ya same su bayan sallar magariba kafin ayi issha'I suka rankaya gida akabar anti amina tare da ita,kusan kwana sukayi shawarwari akan al'amarin,kwana daya da wuni mama na kwance magashiyan ledar ruwa goma sha tara ta shanye,ana shirin daura mata na ashirin sannan idanuwanta suka fara washewa ta gane inda take hada ido da abba tare da karkaf yan'uwanta bai haifar mata da wata nadama ba illa kuka da ta fasa wai don su tausaya mata babu wanda ya tanka mata wannan itace shawarar da suka yanke babu wanda zai sake bata bakinsa don yi mata fada amma zata sha mamaki ranar da Allah ya yasa al'ameen ya dawo kasar nan,babu wanda yace cikanki har ta gaji da shashekar kukanta. A zaton ta shirun na su alamma ce ta saduda ma'ana sun rasa yadda zasuyi da ita dole suu sa mata ido anti amina ta fara bata ruwan lipton tana kurba da kyar take iya hadiye shi gaba daya Makogwaronta ya farfashe kafin gari ya sake wayewa mama ta samo kanta misalin goma da rabi kawai ganin su tayi sun shigo suna gaya wa anti amina an sallame ta zasu wuce yanzu bata yi mamakin jin haka ba don haka ta amsa da to,Allah kara lafiya ita kuwa yar gigalar murna ce fal cikin ta jin za a wuce da ita fandogari nan da nan suka kwashe kaya,yaya abdul-kadeer ya dauki matarsa,mama kuma tabi ayarin komawa gida a minna suka yada zango suka ci abinci tare da yin sallolin azahar da la'asr in banda su ameera babu wanda mama tayi magana dashi domin anti rabi ma ta sauya fuska al'ameen dintama bai sami kulawa ba suna idar da la'asar yaya abdul-rahman ya jawo matarsa daga inda ya aje ta aka maida jakar mama ciki ita ma ta fito ta shige gidan baya abba na tare da karamin yaya a gaba Shi ya jasu a hankali xuwa fandagori. tun daga kan kwana hankalin mama ya soma kwantawa, domin dai idanuwan ta sun hango wanda take son gani. yana zaune bisa benci a kofar shagonsa, yayi murmushi itama ta sakar masa nata. har motar ta wuce, ba su daina leken juna ba. sai da ta daina hangensa, sannan ta zauna sosai kirjibta nata bugawa, ji take kamar ta balle murfin motar ta fice taje gunsa. ya mikawa ayuba hannu suka tafa. yace baka da kyau! Yace karya kak don ubanka, kalle ni sama da kasa! ba kyawun sura ba, ina nufin.... ya kai masa naushi a kafada, shi ya katse shi. zan ci..... kai! ka kiyaye ni fa wlh! me na gaya maka? yadda suka dauke ya ahaka za su dawo min da ita. wahalar banza sukeyi sakeena mallaka tace. yace ranar da Allah kuma zai kama. ayuba baya wajen, duk ka gama iskancin ka. ya ballo masa harara yace, to ko ka na wajen me zakyi? kai ma ka ji da naka, don ubanka. Menayi? ni nakai ka iskanci a garin nan? dama wane kai, amma sannu a habkali xzaka biyo ni mujera hanya watakila ma ka xarta ni. ya tabe baki yace Allah ya sawwake, kai din ma so nake na janyo ka baya. ka auri yarinyara nan, ka manta da kudinrinka na wulakantata. ya dafa shi yace ka dan kula da shagon, bari na je nemo gasasshiyar kaza. kasan dole anjima ta zo 鎷� ya xuba masa ido kawai, bai ce masa komai ba. yayi dan saurayin murmushin. ya mike ya fada motar sa yayi birnin gwarin tsinke. kai tsaye mama dakinta ta shige. umma bata gasganta idonta ba, irin yanayin da taga mama saboda haka tatashi tabi bayanta. Kallo daya tayi mata taji kanta ya ci gaba da sarawa, wani kululu ya daure xuciyarta, idanuwanta suka tara kwalla, saboda tsabar BAKIN CIKI. Ta jima kafin tace, Mama kina da hankali da tunani kuwa? Ji tayi an dafata ta biyu, muryar Yaya abdul rahma ke fadin, baki da lfya Umma, karki daga hankalinki, abba yace ki fito ki kyale ta. Ya kamo ta suka fito, jiri na dibarta, shi ya sa tace yawuce da ita dakinta. Abba ya taso ya biyo su, yayin da take kwanciya a gado. Gefen gadon ya xauna yace, bai kamata ki bar ciwon ki ya tashi ba halima, kin ji dai abinda Dr. Ya fada, jininki ne ke hawa saboda damuwar da kika sanya a ranki. Ki hrk kawai. Tace, ba alamun yin nadama a wajen Mama, ni kaina, nasan haka,amma shawarar da mu ka yanke da 'yan uwanta shine mu sanya mata ido tayi shirmen ta, sai ranar da Al-ameen ya dawo xata gane mu ma ba muyi nadama ba. Abdul yace saboda haka ki kwantar da hankalinki, ISA sai dai mama ta mutu a dakin Al-ameen, ba zamu ji kunya ba. Su Yaya babba da Iyalnsu duk sunce gaishe ki, sai sun xo. Tace ina amsawa, Allah ya taimake mu, suka amsa ameen. Abba ya dube shi ya cigaba, kai ma ya kamata ka hanxarta wucewa yamma tayi sosai. Umma ta amshe, ba xai bari xuwa gobe ba? Yace, akwai aiki Umma, yanxun nake so na lallaba. Ta dan kada kai. Tace, to Allah ya Tsare agaida min safiyya da kyau. Zata ji, ki daina damuwa Umma, komai xai wuce da yardar Allah. Ta amsa da kai, tana fadin shikenan abdul, Allah yayi maka albarka. Yace amin. Ya wuce cikin hanzari. A tsakar gida ya hadu da su Haj.Hajjo. Ashe da gaske ne kun dawo? Yara ke fada mana yanxun. Yace eh, nima xan wuce kd kenan. Gaba daya suke to Allah ya tsare! Ya amsa yayi gaba abinda, su kuwa ciki suka kutsa kai dakin mama. Kwakwazon surutun su ya sa Abba ya ta so fito. Sannuku da dawowa Yaya. Yace yauwa, ga haliman can a dakin ta. Haj. Hajjo tace, muna nan mun ganin ikon Allah. Mama ta dawo kashi ba rai? Yace haka take so, ai ku daina bata bakinku, kowa ya sa mata ido. Haj. Gaje tace, lallai kam wannan al'amarin sai ido. Allah ya kyauta. Ameen.
Chapter 35 · 0% Book details