← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 79

Sashe 34

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a dauka ba malami ya shigo gidan dawo war sa ke nan daga maka ranta,kicin ya wuce kai tsaye saboda yunwa ce ta koro shi ya debo abinci ya zauna ya fara ci waya ta sake daukar ruri ya mike da filet din a hannunsa yana kara lomar shinkafa da salad ya dauki waya baki cike da abinci ya ce hello hello malami al'ameen ne ba kowa ne a gidan yace eh nima yanzu na dawo school mai gadi ya gaya min sun tafi kai anti mama asibiti wai ta suma. Jikin al ameen Ya kara mutuwa ya ce gaskiya Uncle duk ta rame kamar ba ita ba bata magana sai kuka Tunda suka dawo da dadi ba ta ci komai ba ko ni bata. Yi min magana ba sai yau ta ce za ta mare ni idan na sake gaishe ta wane irin ciwo take yi uncle hawaye suka tsunke wa Al Ameen. Bai san lokacin da ya kife kan wayar ba malami yabi ta hannunsa da kallo. Bai gane komai ba dan haka shima ya aje ya dauki abincinsa ya cigaba da ci yayi sallar magariba dadinsa ya shigo yayi masa sannu da zuwa ya amsa ya haye sama ya cire kaki yasa kana nan kaya jaket da wando ya sauko ya shiga kicin ya hada kayan abinci cikin dan matsakaicin kwando ya kira malami yace kai mota ya jirashi can su tafi asibitin,yace dadi yauwa uncle al'ameen ya kira waya dazun me kagaya masa na gaya masa anti ta sume kunje kai ta asibit to ke ka kirani a mota ya dauki kwando yayi waje jim kadan dadinsa ya fito suka tafi har zuwa lokacin mama bata gane kowa yayan ta ya zauna nan zuwa goman dare sannan suka koma gida da malami Anti amina ta kwana tare da ita kiran asubahin farko ta dawo hayyacinta ido ta zurawa anti amina kafin ta fasa kuka anti amina ta matsa gare ta ta dafa ta saman goshinta tace me yasa kike wahalar da kanki bayan ki na sane da cewa aure tsakaninki da al'ameen babu fashi,ta goge hawaye wallahi wallahi anti bazan. Taba cin abinci ba har sai yaya ya maida ni inda ya dauko ni kinji kuma na rantse bazan kaffara ba,baki sake take kallonta tama rasa ta cewa mama ke ci gaba da fadin na gwammace na mutu da a raba ni da dan liti sabo da haka mu zuba nida yaya idan jan idonsa zai sa in daina son dan'liti anti amina tace gadkiya ne kuma yanzu kika tabbatar min kinyi nisa ka kya jin kira To abinda zan gaya miki shine ki guji bacin ran iyaye rayuwa ki ba zatayi kyau ba muddin kika bar mahaifanki da BAKIN CIKI sannan dole ki fuskanci kalubale tunda kika ci amanar dokta bazan rufe miki ba mama koda nan gaba in ta Allah ta kasance zaki tuna dani kice na gaya miki a asibitin nan wallahi yadda kika sanya al'ameen kuka da radadin zuciya kema sai dan liti ya dandana miki fiye da hakan Da namiji ne fa ki bari ya gama shanye romon da yake hange a jikin ki kisha mamaki daidaiku ke da rikon amana su ajiye ki ke kadai suna girmamaki a matsayin matar sunna mai tsananin kamanta gaskiya shi ne zai ce kik zai kara aur amma sauran shagalinsu suke sha a waje su barki hoto a gida balle wannan Dan'liti daya sami shaidar banza don haka kibi a hankali mama so ba hauka bane tace na ji kin fada amman yarda ba dole bane ko ashe kin gane domin ni duk abinda mutun zai fadi akan Dan'liti ina daukar sa a matsayin hassada ina abin hassadar ga Dan'liti koda ban san shiba labarinsa ya gamsar dani kuma na tsane shi idan kin tsane shi ki daina maganar sa don zai sanima in tsane ki Ta ware ido sosai tana kallon ta ban yi mamakin jin kalamanki ba tunda kika iya shafawa idanuwanki toka ba kya ganin mahaifanki ki balle ki saurari nasihohinsu gareki kin ban kunya mama ban taba zaton wata rana mai kamar wannan zata zoba in sha Allahu zan rarrashin dadin malami ya kyale ki duniya ta koya miki hankali,ido cikin ido ta bata amsa zaifi kyau idan kika yimin wannan kokarin haushi yasa anti amina ta mikie ta fito babban falon asibitin tayi zaune har aka kira asalatu tayi alwala tayi sallah ta je ro addu'o'I tare da rokon Allah ya sanya wa al'ameen dangana idan har ya rasa mama Cikin shigar kakinsa tsaf ya shigo asibitin tare da malami shi ma sanye da kayan makaranta kuratan sojoji biyu na take masa baya dauke da kwandon kayan karin kumallon safe a babban falo ya same ta zaune bisa dardumar sallah,malami ya fara isa gun ta ya gaisheta ta amsa sojojin dake biye suka kwashi gaishuwa yayin da ta miki ta tarbi yallabai amma fuskarta babu walwala sannu da zuwa tace dashi ya amsa yauwa ya dai jikin na ta, tana ciki shiga ka ganta ai ta farfado tun asuba,ko?suka jera zuwa dakin tana gaishe shi jin muryarsa yasa mama ta runtse ido ya tsaya kanta yace ki daina matsr ido nasan kina ji na ina fatan amina ta gaya miki sako na saboda haka ina son ki gane wannan sakarcin bazai firgitani ba abinda na sani kawai al'ameen ya dawo a daura maku aure middin kina numfashi sauran shawara ta rage gare ki, Anti amina dake ta kallon ledar ruwa tasa hannu ta dago igiyar tabbas abinda take zato shine din. Ruwan ba a jikin mama yake ba cirewa kikayi mama, ta juya kan yallabai tayi masa kuri ka gani ko ta cire ruwan yaya ya kawo iya wuya kamar ya nannausheta yake. Ji cikin fushi ya juya ya fita anti amina tace da kanki ki ka kama drip din ki ka tuge,sau dubu aka samin sau dubu zan cire me ruwanku dani tunda baku kauna ta tana rufe baki yayan na shigowa da wasu nosis biyu amma abin karin haushin mama taki yarda su mai da mata ledar ruwan nan basu san lokacin da yayanta ya cire hannu ya tsinka mata mari ba,sai da bakinta ya tsatso jini saboda haushi da takaici kafin ayi haka ya bar dakin anti amina ta biyo bayan sa ta bar nosis na rarrashin mama yana shiga mota ita ma ta fada ciki tace kayi wa girman Allah yallabai karkayi fushi ka tsaya ka saurareni kar ki min magana akan wannan wawayar yarinya," I have finish with her, dama munyi waya da abdul- kareem sun ce za su zo harda abdul-rahman so suna zuwa zasu wuce da ita daga can su bata kudin mota ta wuce fandogari zan iya kashe yarinyar nan idan ina ganinta, tace wallahi ni ma shawarar dana ke son in ba ka ke nan idan kaji maganganun da mama ke fadi zaka tabbatar da tayi nisa bata jin kira sai addu'a kawai zamu zauna ne tana bamu wahala koda yaushe mu ma asibiti a aikin banza?ba zai yuwu ba a irin take taken ta tana gab da fara sufa mana zagi ku kyale ta da dan-litin shi ne zai koya mata hankali,yace ai an gama dokta zuwa kice ya sallame ku kawai zan sake kiran abdul- kareem din in ce su dame mi gida ta numfasa don murna kafin tace,"!58,naji dadi yallabai Allah shi taimake ka ita kuma ya shiryar da ita amin ga break fast can kije kici ki kyale ta bari mu kai malami school gada can zan shiga ofis to a dawo lafiya amin,ta fito sannan sojojin suka taso daga. Inda suke tsaye tare da malami suna jiran su babu bata lokaci suka bar harabar asibitin anti amina ta koma ciki tace wa nosis su kyale ta su tafi abinsu guda tace oga zaiyi fada madam idan ya shigo. ni nace ku tafi kawai abin ku ba mu muka kawota ba,kuma mu zamu biya bill ku wuce kwai ba wani abu"nosis suka wuce da mamaki anti amina ta hada abin kari ta hau ci bata sake komawa ta kan mama ba har likita ya shigo misalin takwas da rabi na safiya anti amina ta maida masa bayanini yallabai likita yace a'a baza ayi haka ba nan ya ja kujera yayi ta rarrashin mama,tayi shiru kamar da gaske sauraronsa takeyi da kansa ya nemo jijiya ya maida mata ruwan amman me yana gamawa bai ko bar dakin ba ta sa hannu ta zare ta aje masa robobin sa haushi ya shake likita ya jima yana kallon ta sannan ya dauki (file)din ta yayi rubutu,ya dubi anti amina yace kuna iya tafiya gida madam da alama ba zamu shirya da sakeena ba tace ai dama na gaya maka kayi hakuri dokta kan ta tayi mawa tace ba wani abu shawa ta kawai ia ce ku kyale ta ta auri wanda ta zaba may be rabon wahala ke kiranta,tace sosai kuwa dokta mun gode ji suka yi mama taja wani shegen tsaki duk suka bita da kallo likita yace I'am sorry for yau,a tunaninki kinyi abu Mai kyau ke-nan? NO,ba hk rayuwa take ba. Ya kamata ki rinka kulaw. Ya sa kai ya fice.Nosis din sa suka take masa baya,kowanne su babu wanda bai shak鐭� taikacin Mama ba. Tana hada kaya direba na shigowa, yaya ya turo shi,idan anyi sallamar ya kaisu gida. Shi ke nan kaya sun tsunke karkashin kaba. Ya kwashe kaya,ta dubi Mama tace, ki na iya tasowa muje gida,idan kin so.Ta yunkura ta tashi,Anti Amina bata saurareta ba ta wuce abin ta. Da kyar ta sauko daga gadon,wani mugun jiri yayi tafiyar ruwa da ita,ta koma dabas! Ta zauna.(maganin mara jin magana,yarinyar nan tana ban haush鐭�! Mts!) Tafi minti uku dafe da kai,sannan ta sake mikewa ta daddafa bango ta fito tana layi. Kowa kallon ta yakeyi,musamman Noisis din da komai ya faru a gaban su,ai nan take aka shiga maida labari. A mota ta same su. Anti Amina na gidan baya,duk ta kulle sakatun kofofin biyu,saboda haka dole Mama ta bude murfin gaba ta zauna tare da direba. Ko a cikin gidan ma,babu mai kula wani,hasalima Anti Amina kwanciyar ta tayi tasha barci,bayan ta yi wanka ta sauya kaya.Ita kuwa Mama taci gaba da
Chapter 34 · 0% Book details