Sashe 36
Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suka fice tare suka koma dakin Umma, suka isheta da surutu. Duk iya kokarin mama na son fita a wannan daren abin ya faskara, domin dai Abba ya kasa ya tsare a falo har goman dare ya garkame kofar ya shige dakinsa barcinsa. Allah da ikon sa, abba bai xare mukulin ba, domin bai taba tunanin Mama xata iya aikata wani abu a wannan tym din ba lallai abba bai san Mama ta wuce tunaninsa ba. Yana bada baya, taji motsin rufe kofarsa ta yi wuf ta mike, takalmanta a hannu tare da mayafinta. Tayo sanda ta fito jim, tsakar falon bata ji mtsin kowa ba, sannan ta karasa kofar ta bude ta cikin nutsuwa ta sulale ta fice. Can ma kofar sassan hka ta bude ta, ta wuce zaurukan gidan, ta zare sakatun ta bude ta fita ta maida kofar ta sakaya. In bakayi bani wuri! Ta callah da gudu bata ko jin rashin karfin jikinta, sai da tayi rabin tafiya, sannan ta tsaya ta sa takalmanta ta yafa gyalen tana ta xuba haki, ta dau hanya babu jama'a sosai. Gata nan ga ta nan har kofar shagon dan gogan. Ya tare da dije a kofar shagon bisa banci, ta cukuikuye shi kamar na goye fadi yake, wai dan Ubanki dole ne? Kin fa matsa min da yawa, xan ci ubanki a daren nan, in ga mai kwatar ki! Kawai ganin mama yayi akan su. Ya banbare dije ya ture gefe, bai bata lokacin ya daga kanta ya shige, shagon yana jan tsaki. Mama ta daga itama ta bishi. Dije kuwa mikewa tayi ta kakkabe jikinta ta wuce tana kwafa. Ya hade rai a kujera, bai ko kalle ta ba. Ta matsa gare shi murya sanyaye tace, fushi kayi danliti? Ni ban yi fushi ba sai kai? Ina can naki ci na ki sha saboda kai. Ashe ka na nan ka tare da wata? Dubi yadda na rame na sauya kamanni, saboda tunanin ka Danliti. Bai kamata ka yi min haka ba. Ya dago idanuwansa farare sol! Sunji kwalli ya dubeta, ko mai nai miki ai kekika jawo, kinbi 'yan uwanki ki manta da ni, ba dole in sami wata ba! Tun yaushe kuka shigo garin nan? Nayi ta xuba ido, amma ban ganki ba, me kike tunanin xan dauka? Kafin tace wani abu ya fizgo hannunta xuwa daki, yana kara fadin, idan karya nake yi, xo muje ki gani! Ayuba dake kwance bisa katifa yayi firgigi ya tashi yana kallon ikon Allah. Ledar kaji ya janyo ya xaxxage su. Yace me kika gani nan? Saboda ke na tafi har birnin gwari na siyo miki gashin xamani kajin turawa. Dubi nan juice ne kala-kala har sanyi su ya fita, baki xo ba. Ba dole in yi fushi ba, in saurari mai so na! Ta sauke numfashi, idanuwan ta taf! Da kwallah, ba laifina bane Danliti, baka san irin bakar wahalar da na sha ba, don kawai su dawo da ni. Sau biyu ina kwanciya a ascibiti, dube ni da kyau, kai kanka kasan ba haka nake ba. Amma kayi hkr, tunda kana ganin kamar da gangan nayi, ka hkr? Ya xura mata ido jim, sannan yayi dan murmushi ya ware hannayensa yace, to oyoyo! Ta sa hannaeyanta ta rufe fuska. Yace kunya? Ashe baki so na, lallai na yarda ni kadai nake haukan sonki. Yana rufe baki ta matso da sauri ta rungunme shi. Ayuba, yayi gyaran murya. Mama tayi wuf ta rabu da jikinsa. Ya dubi Ayuba, yace malam ka fita ka bamu wuri! Yace, ai ku ya kamata ku koma daga waje anan nake so mu xauna, fita ka bamu wuri don Allah, shago fah abude yake, ya yankura ya tashi yana fadin, gaskiyya kuyi sauri ku gamacin kazaraku, barci nakeji. Ba ruwanka wannan. Ya fice yana waigen Danliti yana masa ishara da idanuwansa dauke da gargadu, wanda shi kansa ya gane nufinsa, shi yasa yake wani irin mur0ushin na iya shege. Yana fita ya dubi Mama suka hada ido dukkan su sukayi murmushi, sannan ya kamo kafadunta yace, gashi dare yayi, amma dole ki xauna ki cinye kajin nan, domin saboda ke na siyo su. Ba tace komai bam ya xaunar da ita gefen katifa, ya jawo kayan kwalama, ya baje mata kajin, yana bata abaki, tun tana jin kunya har ta saki jikinta, tana amssa sosai tana ci, suka ci suka sha suna hirar bayan rabuwa. Bayan sun kare. Danliti ya dubi agogonsa ya ce shadaya da kwata yanxu, ya kamata kije gida ko? Sai gobe, ina fatan xaki rika cin abinci don ki gyagije kyanki ya dawo kamar da. Kinji ni? Tace, naji kuma xan kiyaye, amma don Allah ka daina bari 'yan mata na xuwa gunka, watarana xamuyi dambe da su wlh, kaji na rantse. Ya kyalkyale da dariya son ransa kafin yace, xaki kuwa sha duka, don dai nasan sunfi karfinki. Wannan jikin naki rugu-rugu babu kwari. Ya fadi yana mammatsa hannayenta da kafafuwanta. Ta yankura ta tashi tana cewa, haka kake gani, ka maida abin wasa, zaka sha mamaki. Shima ya mike ya kamo yatsunta, yace karki damu, ke kadai nake so, ko da damben ya kama kuyi, xan shigar miki balle ma banda lokacinsu. Ke me xai dameki? Tayi murmushi, tace, to shikenan sai da safe. Ya sumbaceta yace, muje na rakaki. Suka fito yana rike da hannunta, tayi wa ayuba sallama suka wuce. A kofar gida suka fuskanci juna, tallafo kuncinta ya xura mata ido, yace karfa ki damu da ganin Dije tare da ni, wlh ba sonta nake ba, kawai ta matsa min ne dole muyi soyayya, amma xan dauki mataki akanta, tinda ta fara bata miki rai. Tayi murmushi, tace, nayarda da kai, ina fatam Allah ya yarda mana, ya bamu nasara abinda muka sa gaba. Da sauri ya amsa amin sakeena. To sai da safe nagode, wannan karon abin ya cigaba akan labbanta ya sumbace ta. Ta juya da sauri, ta tura gida ta shige ta maida sakatu. Danliti ya runtse ido ya jinjina hannayensa, shege ni! Ya juya yana takawa dda+dai kamar wani kasaitaccen basarake. Mama kuwa sanda takeyi, kamar barauniya ta turo kofar fa'aar dshigo ta mayar d hankali ta kuleta, ta fada gado. Tana jan mayafi, taji a; ttay bude kofa, tayi tsaye jim, sannan ya mayar ya rufe. Muryar umma taji tana fadin, menene alh.? Yace kamar motsin naji ana taba mukulli.. Tace Innalillahi an shi ne? Yace amma ban ga kowa ba. Ya dubi agogo, karfe sha biyu saura kwata, dare ma bai yi ba sosai, to Allah yai mana tsari da sharrin masu sharri. Yace amin, je ki kwanta. Cikin fargaba suka bar falon. Mama ta gyara kwanciya tana gyatsar naman kaxa. Dan kanta tace kwanta naman kaza. Tayi tunani Danliti har barci ya kwashe ta, shi take marfi yana sa mata naman kaza abaki. Da safe tayi wanka, duk 'yan ciwukan da suka rage ba su warke ba, ta goga musu mai, ta shafa hoda ta sa atamfah riga da xani, nan da nan ta dan yi fasali, duk da cewa akwai rama sosai a jikinta. Yau kam tayi dan kyan gani, ta fito falo wajen Umma cikin kicin inda take aikace aikacenta, tace sannu Umma ina kwna? Ta juyo da sauri ta dubeta sama da kasa, tace kalau na kwana. Ta kara matsowa tace, bari in gaida Abba, sai in xo in tayaki aikin. Bata amsa ba ta fice, ta bita da kallo sannan ta kada kai tace, Allah ya shirya. Dakin Abban tayi sallama, ya amsa ya bita da kallo, ta karaso gunsa ta tsugunna, ina kwana Abba? Yace Kalau, ta dan dube shi, amma bata kara komai ba, ta mike tayi waje ta koma kicin: Umma me xan tayaki? Tace ban so, koma dakinki kawai. Saboda me Umma? Ai ban isa na fadi ko saboda mene ba, tunda kin xama shafaffiya da mai. Je ki kawai ki sha xamanki. Kai tsaye kuwa ta wuce daki abinta. Tana fadi cikin ranta, kya gama girkawa, mu zo mu jajja (hmmm mama tayi nisa walle). Kan Umma ya sara ganin yadda mama ta wuce ko ajikinta, bata damu ba. Mamaki bai gama kashe Umma ba sai da ta hange ta kicin din tana diban abinda take son ci. Tana kallo ta koma dakinta ta cinye, ta maida kayan kitchen ta fito. Haushi ya kume Umma bata san tym din da tace, Uban wa kika ajewa kayan ya wanke miki? Tabbatacciya! Ta dan bata rai ta juya ta kwaso kayna ta wanke. Karfe 9 abba ya fita harkokinsa. 9:30 mama figi gyale tayi waje, Umma nace na wanka. Ta sha hirarta wajen Danliti har 12pm sannan ta tsallaka ta gangara wajen Baraka. Sosai taga sauyin fuska wajen Inna saude. Sam abin be dame ta ba. Suna kebewa da Baraka tace. Kawata ban gane ba, sai da nayi miki kallon kurulla. Yanxun saboda Allah dawowa kikayi? Tace ga ni kuma kina ganina. Matsala tace, babu ruwan kowa. Mutane masharanta ne kawai, saboda Allah yayi wa Danliti kyau da farin jini, ga shi ya Rufa masa asiri, shi ya sa ake masa hassada.... Ta katse ta, idan hassada ce, ai kuwa kem kinyi masa da. Menen baki fada ba akansa? Tace, Rashin sani ne, duk surutan da akeyi wai dan Iska ne dan guguwa. Dan wata tsiyace, ni har yanxun Danliti bai taba furta min maganar banxa ba balle ya nemi aikata wani shashanci. Rashin fahimta ne kawai yasa ake masa zargi, kisan mutum mai farin jinin 'yammata (Kuji fa wai bai taba mata komai ba?) baki ganin ko mace ce ta fiye samari sai arinka mata wani irin kallo? Baraka ta sauke fuska, tayi guntun tsaki, baki jin kira Mama. Allah ya shirye ki. Ameen, ni bari in koma gida, dama lekowa nayi mu gaisa kisan na dawo. Tabita da kallo, ki na san kin dawo wajenki xano? Menene anfani kawancen mu? Bayan ko na gaya miki gaskiyya bakyaji. Allah ko? To Allah ya bamu alkhairi ki gaida mohd dinki, in yazo. Yaushe xasu kawo gaisuwane? Ko bai shirya aure bane? Wlh ban masa zargin komai ba, amma sonsa bai rufe min ido ba, ina bukatar in gama sanin ko shi waye tunda ba gari daya muke ba. Ta tabe baki,