Sashe 53
Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ramuwar gayya, tafi gayya xafi. Dadin abin a gabanka mama ta xageni, ta xagi Mahaifina, ka manta kawai! Yace wannan ba hujja bace Danliti, ina gaya maka barnar da kakeyi tayi yawa. Allah ba xai kyaleka ba. Ya ja dogon tsaki ya mike tsaye, kai wannan ya dameka, ni yanxun gidan ma xani kuma lfy lau xaka ga na dawo, see you! Ya juya ya daga kanta ya fice abinsa, ayuba ya koma a hankali, ya xauna ya dora tagumin mamaki da takaici. Danliti ya sake gani ya dire masa bakar leda tare da kwalin juice kato bisa kanta. Yace ga sauran kazar da na ci a mota nan, idan ka gama laulayin, ka ci. Ya juya ya wuce mota, yayi tafiya sa ya bar shi da tagumi. Kansa tsaye yayi fakin kofar gidan Uban dawaki, akwai yara gidan suna wasa, don haka bai yi wahalat neman yaro ba, take nan ya aika yana kiran Mama. Yarinyar ta shiga, jim kadan ta fito ta gaya masa tana xuwa. Yana nan jingine da mota yana kada makullai. Abba ya fito. Nan da nan ya tsuguna kai sunkuye, mummunin kare kenan. Yace, ah! Sannu abba, ina yini? Abba ya bishi da kallo, amma kash, ya kasa ganin bakinsa balle ya gaya masa bakaken maganganu. Ya amsa gaisuwasa, sannan yace mike ka biyoni. Ya wuce kofar falon bakinsa, ya murda ta bude suka shiga, xauna, ya nemi waje ya tankwashe kafafuwa. Abba ya xauna ya dube shi da kyau yace, yanxun saboda Allah Danliti abinda kayi, ka kyauta kenan? Me ya sa duk abinda xakuyi baku sa tsoron Allah a xukatanku? Ya xa kace kana son yarinya da aure, sannan ka aikata mata abinda ba shine ba? Danliti ya kara sunkuyar da kai, kamar xai tsaga kafet din falon ya shige don gulma, abba ya ciga da cewa, to ta faru takare, ahalin Yanuxn Mama juna 2 gareta, kaga xancen auranku ya rushe kenan dole tayi zaman istibra'i xuwa tym da xata haihu. Wannan abu ya bani kunya kuma kun xubar min da mutunci da kima a garin nan. Hannaye 2 Danliti ysa ya rufe fuskarsa yayi xugum, ko mtsi ba yayi. Abba ya numfasa ya kada kai ya cigaba, ni bani da abinda da xan iyayi, tunda kaddara ta riga fata, abinda kawai nake soka sni, shari'a ce ta tsara haka, saboda haka dole ku kauracewa juna, don gudun karku kara maida hannun agogo baya. Ina fatan kaji? Sai ka koma jira ranar da xata haifamaka danka, kaga kun sami dan aike, ba sai kun nema ba. Kana iya tfiya, mu jira abinda Allah xaiyi. Shawara da xan baka kawai, ka nemi tuba wajen Allah, domin ka saba masa, ka keta rigar mutuncin yarainya. Shiru yayi ya kasa tashi, abba yace tashi mana, ni nakare magana, ya dago kai da kyar, amma bai kalli fuskar abba ba, cikin sanyin murya yace, abba kayi hkr ka yafe min? Wlh sharrin shaidan ne. Ya goge kwalla, abba na kallonsa kafin yace, haka ne, amma wani tym har da son xuciya. Si yasa nace ka nemi tuba wajen Allah, don ta ni mai sauki ne. Ya kara rankwafawa yace, je ka kawai. Ya tashi simi simi ya fice babu ko waige. Abba ya raka shi da ido, sannan ya numfasa ya kada kai, yace Allah ya shirya mana. Shi kuwa Danliti yana fita yayiwata 'yar girgiza ta jin dadi, ya wuce motarsa cike da farin ciki ya koma shagonsa. Ledar kazar da ya ajewa ayuba suna nan bisa kantar bai taba ba. Wai don ya ba ayuba haushi sai ya dage kantar kayan suka watse kasa. Ayuba ya bishi da kallon kafin ya ce ni baka ban haushi ba don ka xubar kudinka ne, ba nwa ba, gaskiyya ce dai ba xan daina gaya maka ba, watakila ma baiji shi ba, domin bai tsaya ya saurare shi ba, cikin daki ya shigr. Yayi kwance yana tunanin shirinsa na gaba akan mama. Abba kuwa ys jima falon xaune yana tunani rayuwa kawai. Sannan ya mike da kyar ya koma cikin gida, ya maida wa Umma yadda sukayi da Danliti ta kada kai tace , shikenan, Allah yasa ta nutsu ta xauna gidan. Yace amin, amma ina mai tabbatar miki muddin tace ba xata nutsu cikin gida ba, xan bata mamaki, domin, dole ta xaba ko mu ko shi. Umma tace gaskiyya ne, ace wannan abu ya sameka, baka yi nadama, ai kuwa sai a sallama mutum asa masa ido. Allah yasa mu dace. Ya amsa da amin. Tunanin uwar gayyar ba anan yake ba, domin kuwa jin ga Danliti yana kiranta, ya tabbatar mata da cewar ya dawo kuma taso ta ganshi, su Abba suka taka mata birki. Duk da haka taji karfi a jikinta kwarai da gaske, har wasu daga cikin cuttuttukan da ke damunta suka yaye nan take. Sai dai tana ganin babu adalci a hukuncin dasu abba suka yanke. A zaton su zan iya zama tsahon tym banga masoyina ba???????? Ta tabe baki tana daga kwancw tace, ba xan iya ba gaskiyya, sai dai suyi hkr wlh. Ai dai maga juna, ya san halin da nake ciki, ya tausaya min. Ta goge kwalla ta cigaba da sakar xuci. Ana ta sallar magriba, tym ne da ita mama ta sami damar satar jiki ta sulale ta isa shagon danliti. Shi kuma kaida ke xaune cikin shagon. Ayuba ya shiga sallah. Yana ganinta ya dafe kirji ya wani lumshe ido. Yace wayyo Allah na gode maka! Ta daga kanta ta shiga, ta nemi t barma ta zauna, saboda bata jure tsayuwa. Tana xama ta hade kai da guiwa ta fasa kuka ya kare mata kallo, a dage yana dan murmushi, sannan ya taso ya dawo gunta yace haba bebina! Meye abin kuka? Ya xauna gefenta ya rungumota jikinsa, bana son kukan hakan nan....... Ta cira kai da sauri ta dube shi, ba xanyi kuka ba? Ciki fah gareni, kowa ya tsaneni ana ta zagina. Shine xaka ce ba xanyi kuka ba? Yayi dan murmushi yace, bebi kenan, to don kowa ya tsaneki shine me? Bayanni ina son ki kuma ina son ciki na! Kina so yi kukan ne, wata kila kuma na dadi ne yayi miki yawa. Ta mako masa harara tace, jin dadi? A zageni, a tsaneni shine jin dadi? Son ka ne kawai yake sawa bana damuwa, amma kai ina ganin abin baya damunka, daya dame ka, da baka wanke kafarka ka bar garin ba, tsawon sati 2, alhalin an ce ka turo a daura mana aure. Da ka maida hankali ka turo din, ai da duk hakan bata kasance ba, koda cikin xai bayyana adakinka xai fito. Tunda ni ban ma taba nuna wa akwai wani abu tskanin mu ba. Sannann.... Ya da ka mata tsawa, ya ida don Allah! Haba! Wannan maida xancen na menene? Ko kuwa turo ki akayi ki zo ki batan rai? Ko dan kinga ina ta rarrashinki? Babu fah dole, kin ganne? Abban ki cewa yayi ba dole bane ya bani ke, ko bayan kin haihu. So pls ki daina damu na da irin wadannnan surutun banxan, ban son jinsu, idan har kin son mu shirya! Kin gane? Ta xura masa ido hawaye na xuba, ta ma rasa me zata ce? Ayuba yayo sallama ya shigo ya riske su cikin wannan halin. Shi ma yayi tsaye yana kallon su, jim kadan Danliti ya buga tsaki ya tashi ya shige daki ta goge hawayen itama ta tashi ta bishi, ayuba yaa kada kai ya ja kujera ya xauna yana fadin Allah ya kwaci yarinyar nan. Tana shiga ido ya xubo mata. Yace au biyo ni kikayi? To ranki xai baci kuwa, gara ki koma. Ta marairaice tace, kayi hrk Danliti, ba don ranka ya baci bane ya sa na gaya maka abinda ke damuna. A xatona xaka tausaya min a halin da nake ciki. Bani da wani gata wajen iyayena. Tun ranar da na nuna kainake so Danliti, ka tausaya min. Yayi lum da ido ya bude, ya cigaba da kallonta tana tsiyayar hawaye kusan 3mins sannnan ya yafito ta da hannu, yace xo nan! Da sauri ta isa gunsa, ta fada jikinsa ta kara fashe da kuka. A'a, kinga ni fa kukan ne bana so. Yanxu menene damuwarki? Ta goge hawaye, tace kullum in rinka samun kulawarka, hakan shi xai tabbatar min da kana sona kana son abinda ke cikina. Yayi dan murmushin nan nasa, ya kara janyo ta jikinsa, yace, kin samu bebi, karewa ma da kewarki na dawo. Kin ci abinci? Ta kada kai, saboda me? Bana iyawa ne, jikina gaba daya ya canza, sai amai kamar xai kasheni. Yace ayya sorry ko? Amma duk da haka ba za a rasa abinda kike sha-awa ba, gaya min in nemo shi, na kosa in kore kishirwata. Ta mako masa harara, ya kyalkyale da dariya, meye na harara ta? Ko ke ma xaki min BAKIN CIKI ne, irin na 'yan sa ido? Masu shiga tsakanin masoya suna son suga bayansu. Haushi su nake ji wlh. Tace ai ko ni din ma haushin su nake ji, ah haba? Wlh kaji na rantse. Ya cacume ta tana dariya tana fadin, ban da lfya Danliti, bai saurare ta balle ya tuna ya nemo mata abinda take son ci. Karfe 8 ya fito ya barta can kwance tana murkukusun ciwon ciki, ya wuce waje wani mai suyan nama, ya karbi danyan naman da yasa ya aje masa. Ya dawo ya bade shi da magani, ya maida cikin leda ya nade. Yana xaune bakin shgo bisa benci, yana tunanin tafiya yayi wanka ko ya samu yayi sallah. Mama ta fito tana yafa mayafinta, ya bita da kallo yana murmushin keta, ya cikin? Tace yayi sauki ni xan koma gida sai gobe. Haba haka da wuri? Yanxun fa 8 ta wuce? Kar a neme ni ne. Wa xai neme ki? Don Allah xaumna muyi hira, ba wanda xai nemeki, bayan sun san kina nan. Bata da xabi, don haka ta xauna kusa dashi, ya shiga bata labaran banxa. Jimawa kadan wani kare ya xo gilmawa nan take ya hau kiransa, tace me xakayi da kare kake kiransa. Kasan karen okundiri fada gareshi ko? Yace bai sami nama bane don ubansa okundiiri, ya kece