Sashe 18
Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
BAKIN CIKI 1***10 Wannan soyayya ta su Al- ameen dasakeenar sa ko a film ba'a taba nuna irinta ba. Sannua hankali bikin abdulrahman yana ta kara matsowa, a'yan tsakanin ne jarabwar su Mama ta fito. Allah daikon sa sakamakon ta yayi kyau matuka, domin tanadaya daga cikin ajin farko. Tsalle da murna wajen Mama abin ba'a cewa komai, ba ita kadai ba, kowa yataya ta murna musamman dan gaban goshin nata,daga can yake gaya mata a halin yanxun yana tare daabokan karatunsa, suna liyafar taya ta murna. Donhaka kowannen su dai tayi magana da shi, tayi masagodiya. Babu bata lokacu Abba ya fara bincikar mata makaranta a zariya, amma aka ce ba'a fara siyar daform ba tukunna, jin haka yasa hankalin Al-ameen yatashi, sam baya so Abba yayi wahalar karatun mamakuma, ai cewa akayi a gidan sa xatayi karatunta. Nantake ya kira wayar gidansu, ya kuma yi sa'a dadinsana gida, saboda haka ya marairaice ya bayyana masalarsa, Dady yace, wai me ke damun ka neAminu? Haba Aminullah! Menene a ciki, idan ta farakaratun? Yace, ni dai Dady nafi so ta fara bayan aure,kamar yadda aka shirya tun farko. Yace, wanan yarorigimarka tayi yawa, saboda Allah ya kake so inyi?Kaje wajen Abban, kui magana. Kai tsaye ya bashi amsa, ba xan iya ba, gaskiyya sai dai ka hk, bakasan nauyin da nake ji na uban dawaki ba. Sabodahaka ba inda xani, wannan karon dole ka hkr. Kuma niban ga wani abin xafi ba, idan sakeena ta fara karatuyanxi. Cewa xatayi ta fasa auranka? Kamar zaiyikuka yake fadin, ba haka bane, Dadyi amma ina tsoron mata a jami'a, yace, ban son shirmen ka, kayarda Da Allah shi daya ne mai xartar da komai,sannan ka rike sakeena da xuciya daya, na tabbataba xa ta ci amanar ka ba. Ya numfasa yace, shikenanDady, na gode. Sukayi sallama ya aje waya. Dukjawabin da dady yayi masa, hanlainsa bai kwanta ba, don haka yake sake kiran waya gidan Yaya Abdul.Mama ce kuma ta dauka. Bayan sun gaisa, ya faratambayarta, yaya maganar makaranta? Tace, tananan, form din ne har yanxun ba su saki ba, yace,saboda Allah menene na wahalar da Abba, yanayawon neman makai makaranta? Hakki na ne sakeena, don Allah ki taimake ni, ki gaya wa Abba yabari in dawo, bayan auranmu, sai ki tsundumamakaranta. Tayi 'yar dariya tace na tsunduma kamarwani kogi? To menene idan na fara yanxu? Gaskiyyaban so my princess, pls ki rushe maganar nan sai nadawo. Ta yaya? Ki na cewa sai na dawo. Babu mai tilasta miki, tace wa xan gayawa? To sai dai in gaywaAunty Rabi, tunda ka nace da alama kana da watamanufa. Yayi murmushi yace, manufar kenan gudadaya, xallar kishinki, bana so wani ya san cewa bakida aure, ya lallabo yace xai miki magana. Aikomuryarki yaji, wlh ya cuce ni. Ta kama baki tanamasa dariya, a gaisheka. Dariya kike yi? Dagaskenakeyi, kina da kyau sakeena, ba karamin jarumi bane xai kalle ki ya dauke kai. So pls kic gaba daxama gida har na dawo, in maida ki tawa, ni kadai, aikin gane? Tace, ba dole ba, ya na iya da Maigida? Yafara dariya yana fadin iye! Dan sake fadi inko? Tace,Maigida takobi. Kaina xai fashe uwargida, in dainafadi? Yace, a'a ci gaba madam. Idan kan nawa ya fashe, kin san yadda xakiyi. Tace ya xan yi? Hakanan xa'a sha bikin. Kina fa dada tunxura ni. Ji nakenakfi kowa awajen nan. Tace, sa ranka a inuwaAmeer da Ameera suna tafe.... Me kikace? Me nacekuwa? Don Allah ki maimiata. Allah na manta. Yamarairaice, gaskiyya ba haka akeyi ba, ba haka akeyi ba sakeena. Ai dai banji ba sai ki maimaita ko? Tanata masa dariya tace, sai da safe. Yace, a'a rufeidonki. Kin rufe? Ta rufe tana fadin, uhm. Yace, kingansu? Su wa? Ameer da ameera. Suna tsakiyar mu.Ameer ya cire min hula ya sanya a kansa. KingaAmeera? Wayyo, kamar ku daya my princess, shagwaban ta kawai takeyi a ajiki na. Oh ma Godmwhat a lovely family. I lobe U sakeena, I really meantit. Murya sanyaye ta amsa, me too dokta. Tayi saurita kife wayar ta ruga dakin ta, tayi sufa bisa shimfida,ta datse ciki ta rasa duniyar da xa ta sa ranta tajisanyi. Haka ta raba dare tana juyi, bata san lokacin da barawon ya sace ta ba. Kamar yadda ya tsaramata haka ta aikta, domin bata bata lokci ba, ta samiAunty Rabi ta gaya mata, abinda dokta ke bukta. Taxura mata ido jim, kafin tace, wannan dan nawa yafiye rikici wlh, menene banbancin fara karatunkiyanxun da kuma lokacin da ya bukta? Kar fa yayi miki sakiyar da ba ruwa, ki shiga gidan yayi mirsisi!Da saurinta tambaya, kamar yaya aunty? Tace, ayiauran ya ce bai san maganar karatu ba. Tayimumushi da bai kai ciki ba tace, Haba anti kamarwani jahili, ai dokta baiyi xubin irin wadannan mutanenba. Tace, oh haka ne? Idonki ya rufe kina son sa ko? Ai shikenan, ni 'yar sako ce kuma ko an tambaye nishawara ba xance a'a ba. Tace, kinyi daidai antina,kin kuma san Yaya na ji dake, idan kika ce eh dinnan, babu sauyi. Tace, banson zakin baki, inda yakexuwa neman 'yan matansa sani zakiyi? Ya ya mutsfuska tace, wannan kuma sharrin kine. Ta dada mata duka. Ai gaskiyya ne anti, dan Abba sadauki ne,bawan Allah bai yi xubin shaidanu ba. Ke da kanki, kikace idab bashi ba, sai rijiya. Tace, a'a sai masai barijiya ba, meye ajikin Yayan naki da za'a fada rijiya? Ta gwalalo mata idanuwa tace, ayi kurumaunty, kar ayi 'yan tone-tone, don ni har na hango ki agidan Zoo! Tace, kan biki! Lallai yarinyar na ki gagadon barcina, to ko ke din suke kwakwaxo a kanki,ma zaki gwada min? Ta kece da daroya tana fadin, aidama ni ban fadi ba. Aunty ke ce xaki raina min yaya, alhalin koda mai kwado, ya dara gaya. Tace, naji saikije wajen kwadon ki gaya masa da kan ki, a kyalegaya agefe. Ta rungumo ta, ayya my Aunty ba ma'yar haka dake surukuta ta kaina! My lovely wife! Tatabe baki tace, haka naji masu kyau ke da Al-ameendin naki hakane? Tace ban so surutu, sai in fasa ta kara kankakme ta, yauwa my swthrt, ke kadai ce harabada. Tace, ko baki fadi ba. Haka ta lallaba ta sukasasanta, don ta san halin Aunty Rabo, da wasa xatace ba xatayi abu ba, amma sai sai ki sha mamaki,taki ai watarwar da gaske. Ba yaya Abdulkareemakadai, su Abba kan su sun sha mamaki da wannan sako da yazo kunnuwansu, sai dai Abba baiyi jayayyaba, du da yana shakku cikin ransa, yana jin kamar Al-ameen ba zai bar ta yin karatun bane. To amma idanya dubi iyayensa, sai yayi saurin kauda wannantunanin. Yanxun bikin abdulrahman shi suka gaba,sun kyale fafutukar makarantar mama. Shi dai dadi bai san yadda akayi ba kawai an masa ne makarantarce bata samu ba, sai wata shekara. Tun sati biyun sasuka wuce aka fara gabatar da shirye-shiryen biki tahanyar kai kayan lefe kaduna. Tun daga lokacin sumama babu xama, kusan kullum fita sukeyi xuwakasuwa, domin yawancin abubuwan bukata, daga nan minnar xa su taho da su. Satin daya shigo shine yakama kwana shida biki, don haka a gobe su mama damutan gidan za su wuce Fandagori. A daran ranarraba dare sukayi suna hira da Al-ameen, saboda xasukwana biyu basu motsin juna ba. Washegari dasassafe yaske bugowa. Sai da kalamansa suka sa Mama kuka, don kalamai ne masu ratsa xuciya, suhana ta sukuni, shi ya sa bakinta gum! Tana tunanitare da kewar Doktan ta, ji take kmar tace su sauketa koma gida. Ta dai ya daurewa sannu a hankali tatattaro nutsuwarta wuri daya, ta dauki dangana. Sunisa kuma, ganin Ummanta ya debe mata kewar masoyinta. Bayan sun ci abinci, sunyi sallolin su,sannan suka ci gaba da tattaunawa akan shirye-shiryen biki. Karfe biyar dai-dai lokacin ne rana tayisanyi. Mama ta sheko wanka tayi shafe- shafe, bayaga hoda bata karawa fuskar ta komai ba, ta daukowata atamafa 'yar ingila ruwan bula ta sanya, ta daura dan kwalin ta, ta ziro bakaken takalma, ta yafo bakingale ta rataya jaka. Duk wannan shirin na tafiya wajenBaraka ne, wai nan ma ba kwalliyya tayi ba, kawaiyanayin jikinta ne baya boye kyan da kaya ke mata.Ta sallami Umma ta kama hannun Ameera suka fitotare A kofar gida suka ci karo da Ameer, yanaganin gari shi ma yace zaije. Tace yaje ya fadi a gida,don kar a neme shi. Daga nan ya kwaso takalman sa.Ya sheka a guje cikin 'yan dakikai ya fito suka wuce.Suna gaba tana biye da su, suna xuba mata labari,iya ko jinsu bata yi, don tayi nisa a tunanin Doktan ta, kalamansa ke shiga suna fita a kunnuwanta, "kwanakigoma banji muryarki ba sakeena? Ai yayi yawa, kitaimake ni kar ki sa asiri na ya tonu a makarantarnan. Xauntuwa xanyi cikin aji in kasa gane komai".Idanuwan ta suka tara kwalla, tayi sauri ta shanye su,tana fada aranta, ba xan xauna ba, ana gama biki xan koma...... Sannu 'yam mata! Muryar ta fito. Samaribiyu ke xaune bisa benci a kaofar wani katon shagodaf da bakin titi. Daya fai sol! Ga dogon hanci damatsakaitan idanuwa, duk da cewa a xaune yake, kana kallon sa zaka gane dogon gaske ne. Gashinkansa kuwa mai santsin gaske ne, har yana nannadewa duk da cewa bai da yawa akansa, watauyayi aski. Kwalli ram! Ya xauna a idanuwan kamarmace. Ga kuma alamar gashin baki baki wulik! Akwance, guda kuwa wankan tarwada ne kuma zamansa kusa da na farkon, ya dushe gaba daya kyan sa.Gaba dayansu, ta san su, amma tuni suka bace a kwakwalwarta, domin shekaru masu yawa rabon ta dasu. Sannan ko a wancan lokacin babu wata alakantsakanin su. Shi yasa a yanxu take masu kallonmamaki, yayin da farin yake kara fadada murmushinsa, sannu ko? Ya sake fadi. Wani guntun tsaki tayi,ta wuce abinta, sukayi sa'a babu wata mota mai xuwa, don haka ta rike hannun yaran suka tsallakatitin. Ka gani ko? Na gaya maka karka yi matamagana, ba zata saurare ka ba. Yayi murmushi yace,ko bata suarare ni ba, dole ne ma ta so ni, domin irinwadannan su ne ke nema kuma ban taba daga ido nadubi yarinya nace ina son ta ba, tayi min kallon banza ta xubar ba. Yace yau ka samu, saboda haka dukabinda kake takamar ka na dashi, yau