← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 79

Sashe 52

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

AKIN CIKI 2***14 Ya soja ya dubi Ya abdulrahman, yace je ka kawo mana ita nan! Ya miki cikin hanxari, ya nufi dakinta, tana kife bisa gado aikin kuka kawai takeyi. Ya sa hannu ya fisgota, ba karamin tsoro ya bata ba, ta kwala ihu, wani BAKIN CIKI ya kara turnuke shi, bai san tymda yasa hannu ya doke bakinta ba, yace rufe mana baki shashasha. Da sauri ta kame baki, wanda take kyautata xaton hakoranta xasu iya xaxxagow idan bata dafe shi ba. Ahaka ya ciga da jan ta har dakin abba. Gaban babban ya direta, ta xube har tana karo da guiwarsa. Ya xuro mata ido kamar zasu fado kasa. Yace matsa kdaga kusa dani, xan iya tokarinki, ki mutu idan baki matsa ba. Ta janye jikinta baya, ahankali hawaye na ambaliya, sunfi minti 5 babu wanda tanka saboda takaici, kafin Ya abdulkrm yace, gaba daya kin rusa rayuwarki Mama kin lalata cikar asalinki da martabar iyayenmu. Yanxu wa ya isa ya kankare bakin fetin da kika shafawa kanki? Wa ai daura miki aure da ciki? Wa kuma xai jagoranci kisan kai? Wannan cikin dole ki haife shi, domin yunkurin xubda shi, ya fi yinsa barna da tarin xunubi. Kin ga tun daga nan idan kinyi tunani cikin hankalinki, xaki gane babu soyayysa tsankaninki da Danliti. Burinsa dama ya ruguxa rayuwarki, burinsa kuma ya cika tare da hadin kanki. Saboda haka dabara ta rage wa mai shiga rijiya, sannan karki xargi Danliti, idan ya tsallake auranki, gaba daya abinda yake bukata ya samu, abinda yai saura shine ki haife masa wannan ckin, in ya ga dama ya karbi dan, idan bai yarda ba ya kyaleki da shi, ku wulaknta. Dama wannan shine karshen son xuciya. Babu uwar kudi balle riba ga mai cinikin son xuciya. Kuma duk wanda ya hau motar kwadayi da son xuciya, babu tantama tashar kunya da nadama xata kaishi ta aje. A koda yaushe karshen danasani, ina fatan wannan xai xama darasi gareki, ki gane cewa abinda Babba ya hango, yaro ko ya hau gwauron dutse ba xai hango ba. Ya goge 'ya kwallan da suka xubo bisa kuncinsa sannan ya sauke numfashi ya dubi sauran, yace yanxun mene abinyi? Abba yace abinyi babu shi abdulkrm, tunda maganar aure ta rushe a halin yanxun. Ya Soja yace duk da haka, dole ya san tana dauke da cikinsa, bayan ta haihu xa a daura musu aure, su tare da yaronsu! Su karata can da abin kunyarsu! Ya abdul rahman ya kara sanyaya muryarsa mai taushi, yace wannan dole ne, amma abu na farko shine, ina xata xauna? Ta kula da kanta? Umma dai ba xata jure ganinta a wannan yanayin ba, ya soja ya gyara zama yace, gaskiya ne, kuma waje na ya kamata ta xauna, sai dai ba xan iya daukarta ba saboda xan iya yi mata dukan mutuwa yadda nake jin na tsani ganinya. So a cikinku, wanda yake ganin xai iya hkr da ita, yana iya tafiya da ita Allah ya shiryeta, mu kuma kullum addu'a muke mata, idan ta dauki wannan mtsayin darasi a gareta, xamu fi kowa farin ciki. Ya Abdulrahman, yace ni xan tafi da ita, no ka bari ni in wuce da ita Minna. In ji Ya abdulkrm. Abba yace ba xata biki ba nan da xata xauna... ban ce mata yin ku za su yadda ta ba amman yau da gobe sai Allah. gara ta zauna anan, domin anan ne suke aikata abin kunyar u kun ga ganinta da juna biyu ba zai girgiza kowa ba sanin cewar daman can sakamkon da zai biyo baya kenan. in ba wani gyaran Allah ba. saboda haka ku kwantar da hankalinku kuci gaba da yi mata addua sannan ku kwantar da hankalinku ku tallafa wa mahaifiyar ku ta kowace fuska don ganin ciwon BAKIN CIKIN bai tagayyara ta ba, dukkan su suka jinjina kai alaman uban dawaki gaskia ne. yaya soja yace da yardar Allah umma ba za ta tagayyara ba, idan mama bata son ki mu bamu da wacce ta fi ki. bamu da wani buri. da ya wuce mu rayu tare da ke. kar bacin ran mama yasa mu dakatar da dukkan farin cikin mu. mu ukkun nan mun ishe ki kallo ki samu sanyi a ranki ko umma? hawaye na suka malalo mata yaya abdul yayi maza ya rungumota ya na share mata hawayen ki daina kuka umma in kina kuka mama ba zata taba ganin haske ba, duk adduar da zamu mata tace ba komai wallahi bana jayayya da ikon Allah amman ku sani BAKIN CIKIN ba zai goge cikin raina ba, domin FARin ciki da bakin ciki duk halitta ce cdaga Allah fata na kawai Allah ya bamu ikon cinye jarabawarnan Allah yayi maku albarka Kowa ya numfasa, yace amin, abba ya dubi mama da hawayenta yaki yankewa yace, ina fatan kin ji abubuwan da 'yan uwanki suka fadi, idan kinyi anfani da su, ki ga daidai, idan kuma kin ce ba haka ba, mu babu abinda xamu iya yi, sai mu kyale ki, ki ci gaba da rayuwar da kika xaba. Ko dama kin riga kin ruguza ta, karashe ne kawai. Allah ya shiryeki, ki na iya bamu wuri mu sha iska, ki jira dawowar Danliti, amma ki sani auran ku ba shi yuwuwa, sai bayan kin haihu. Tashi ki bamu wuri. Ta kara makurewa, kukanta ya karu, duk suka xubo mata ido. Ya soja yace wa yace kiyi kuka? Cewa akayi mun gaji da ganinki, ki koma dakinki. Ta yunkura kamar xata tashi, amma ta kasa, da sauri ta rarrafa jikin Ya abdulrahman, ta kudundune ta rushe da kuka. Nan da nan ta karya masa xuciya, ko dama shi akwai sanyi da saurin jin tausayin mutum. Idanuwansa suka cika taf da kwalla, tun baya son kulata har ya kai hannunsa, bisa knta muryarsa na rawa yake fadin, imani kawai xai sa akalleki Mama, amma ke ba abar tausayi bace, tunda baki tausaywa kanki ba...... Ya soja ya katse shi, pls abdulrahman, fita da ita, Umma tace sai ma ya fita da ita? Gata kenan, ya kyaleta, ta tashi da kanta ta wuce. Ya tarairayo ta suka mike tare, ya janyo ta xuwa dakinta ya xaunar da ita bakin gado. Ya tsugunna gabanta yace, dube ni Mama. Da kyar ta dube shi, hawayen ta na xuba, yace kukanki bai da wani anfani, muddin ba nayin nadama bane. Nadamar ma ta gaskiyya, tsakani da Allah. Saboda haka ina shwaratar ki da ki kama kanki, wannan ya xama na farko kuma na karshe. Ba soyyaya vace wannan, ki dauki jikinki ki ba da ga namiji, daga ranar da ya sanki a waje. Wlh kin gama yawo, duk wulaknci da ya ga dama xaiyi miki, ko da kinyi sa'a ya aureki, abanxa xai rika kallonki, sannan wulakanci ba xai daina shi ba, a karshe ki ga auran ya bantale, tun ba aje koina ba. Kuskure ne, kin riga kin yi Mama, irin wanda bamu taba xato ba, babu yadda xa muyi mu gyara shi, sai dai kiyi tuba wajen Allah, sannan ki nemi afuwarsu Abba, kin jini? Ta xura masa ido, hawaye na ta bulbula ta kasa fadin komai, domin ita kanta bata san ainihin abinda ke damunta ba, cikin ranta agame da samun ciki ba tare da aure ba. Saboda haka, sake fado masa tayi, ta kankame shi, kukan ta kamar xai fasa xuciyarta. Ba karamin rikita shi tayi ba, domin nan take ya goce da kukan shi ma. Da kyar ya banbare ta ya mike da sauri ya bar dakin, ya dawo falo ya cigaba da gugar kwalla, xuciyarsa na masa ciwo. Kai! Sun dandani BAKINCIKI, da akwai yadda xasuyi su goge wa Mama wannan bakin fentin da sun goge mata shi, ko da shi xasu rasa komai nasu. Sai dai kash! Babu hali, shi ya sa ko abinci tsakurarsa sukayi suka ci, ba don yayi musu dadi a baki ba. Haka suka juya bayan sallar la'asar makare da BAKIN CIKIN da baya misaltuwa. Haka zalika sun bar Mama cikin wani yanayi na kunci rayuwa, wanda ya wanxar mata da cututtuka masu dama ajikinta. Kafin yamma ta fadi, kamar ba ita ta dawo Legos dambasheshiya ba. Sati 2 kenan yau babu labarin Danliti, yayin da rashin lfyar mama ke cigaba da yaduwa tamkar yadda labarin samun cikinta ya gama baza gari, ta bakin Hajiya Gaje. Amma don tsabar yaudara su suka matsawa Mazajensu su akan su kai ta asibiti ko ta sami dan taimakon da xai rage mata larurar jikinta. Da kyar abba ya amince. Alh. Basir ya kaita babban asibiti da garin Kagara. Suka ga likita, yayi gwaje gwajen sa ya gano, lalurar shigar ciki ne ke wahalar da ita. Saboda haka ya bata 'yan taimakon da xasu rage abubuwan da take ji a jikinta, sauka dawo gida. Sun wuce kofar shagon Danliti shi kuma yana karasowa wajen. Yayi fakin ya fito tare da yin daguwar mika mai isar da sakon gajiya. Ayuba ya fito ya tarbe shi, sai dai fuskar sa babu fara'a ko alama. Yaya dai mutumina? Naga kamar kana ciwo? Ya numfasa, amma bai tanka ba har suka shige shagon. Ya dube shi da kyau, yace ina magana ka kyaleni, lfya nace? Ya kara sauke numfashi. Yace ina fa lfya, magana ta cika gari..... Ya katseshi Mama na da ciki ko? Gabansa ya fadi ya saki baki yana masa kallon Mamaki, Dan liti ya kece da dariya, kwalla na gangara bisa kuncinsa kafin yace, shiege ni, dan buzu mai shayi. Raina kama gaiyya, ka tabani ka ga tsiya. Watau labari har ya bazu ko? Kaga burina na farko ya cika, amma har yanxun akwai saura, don na san dan xagin kalilan za'ayi mata. Ido jajur! Ayuba yace, kaji tsoron Allah Danliti, ka kyale yarinyar nan haka. Tunda ba xaka aureta ba, ka barta taji da wannan bala'in! Ai ka gama ruguzamata rayuwa, babu sauran wulakanci da yafi wannan..... Ya ja Kujera ya xauna, yace haka kake gani, nasan akwai saura, sai dai ba xan shanye maka dadin labarin ba, idon ka nake son ka gani kamar yadda ka ga wannnan. Ya bishi da kallo, yana kada kai. Murmushin keta Danliti yayi, ya sake fadin, babu wani abu mutumina, kai kanka kasa
Chapter 52 · 0% Book details