Sashe 72
Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
zubdahawaye.bansan lokacin dana goce da sumbatu ba,fadinake haba ruqayya,meyasa zakimin haka?saidanafara sonki zaki tafi ki barni? kinmin adalci kenan? yanxu ya kikeso nayi da raina?dady ya dafani yacekayi shiru da bakinka al'amin.taso haka ya isa!nadubeshi hawaye na sauqa nace haba dady wannanwani irin abune? narasa sakeena sannan narasaruqayya ma kenan?ku tausayamin mana.118Baice komaiba yadauke kanta daga jikina yanadeta waje daya,sannan yakamoni ya fiddo niwaje,yatura aka fito da gawar.mutane maqil!sukasallaceta nadauketa da hannuna nasa akabari akabinne abinda nakasa mantawa kenan.ya rinqa firgitaniidan natuna dasafe munyi waya da ita.nakasa kallon jinjirar data bari ga waleed naqara raunana min xuciyada tambayoyinsa.su nanta aka maidawa bebin danhaka muke kiranta waleeda.babu inda tabarmahaifiyarta.tananan yanxu shekararta daya darabi,nikuwa tun lokacin nakoma rasha nabar waleedwajen mami.ita kuwa waleeda tana hannun umman ruqayya.idan kinganni nigeria to gayyotani akayi waniaikin dabazan wuce sati biyu ko wata guda ba.gabadaya nasamu rauni acikin xuciyata agame damaganar aure ko soyayya.dukda nasan nafaramanyanta yakamata nasake aje mata.amma banatunanin hakan.abisa dalilin dani kaina nasan ba hujjabace a wajen ubangiji,119Amma Allah yagani na jarabtu wajen kewarruqayya.da kayan sonki danakasa sauqewa shekarada shekaru.kuma inayin addua ina rokon Allah idanyasake bani mata yabani wacce zuciyata zatasotakarna sake tafka kuskuren danayiwa ruqayya.saibayan ta mutu nake gayamata kalmar so.kwatsam! Nasami takardar gayyata indawo inyi aikin wata shidaanan asibitin zariya.musamman saboda ku yan koyonaikin dakuma yawan samun matsaloli lalurar datashafi kwakwalwar yara.bantaba tsammanin zansakehaduwa dakeba sakena.saigashi cikin satin farkodana shiga office.Allah yahadani dake.nayi murna da farincikin dana manta rabon da inyi irinsa.don azatonaAllah yakarbi adduata.saboda yasan babu macendanakeso tamkarki..ya numfasa tareda shafa zufardata karyo masa,yaci gaba da fadin.koda yake nayiimanin bakomai kakeso yake zama alheriba.wata qilaakwai abunda Allah yaboye agame damu shisa nakasa samun aurenki.nagode Allah tunda ya tsamoki daga qangin sharri.ubangiji yadada tsaremu dagasharrin masu sharri. Ya dubeta tana share kwalla yace kukan me kikeyi?tace mutuwar ruqayya naji tamkar nasanta.Allahyajikanta.yace amin summa amin! tace haryanxuwaleeda tana suleja?yace tana can waleed ma yanazuwa hutu yadade acan har hutun yaqare.ta numfasatace Allah amfanasu yace ameen.sukayi shiru suna ratsa tsakiyar zariya haryakawo gida.yayi fakin.tadubeshi daidai lokacin dashima ya dubeta.tacenagode ina fatan zaka yafemin.yace me kika min?tace shikenan saida safe.ta bude murfin motar tafitoyana kallonta bai iya tankawa ba.yabude nasa murfinyafito yasake dubanta yace dazaki ban numbarki dakin taimakamin ko gaisuwa mudinga yi.tagyaratsayuwa tace kada muyi hakadakai babanwaleed.alfarma biyu ka nema.kakuma gayamin naamince.toyanxu zaka karya alqawari.ya kada kai yacesakeena.....ta katse shi saida safe baban waleed tajajakarta ta tura get ta shiga ta nufi bangarenta tana budewa zainab ta tura qofar ta shigo.sakeena kindawone?tadub eta da murmushi bake kika turamin dr ba?yana iya daku!ta tura qofa tashige,120.zainab tana dariya to ko kefa? saboda Allahakanme zaki bar karatunki?ta jefar da jaka tazaunagefen gado bazaki gane bane zainab.medaki shiyasaninda yake masa yoyo.nisanta ta da dr shine zamanlafiyata.tazauna kusa da ita ta sanyaya murya tacedon Allah intambayeki?tace tambaya naji.tace tsakani da Allah bakison dokta?ta zura mata ido jim kadantace meyasa zakimin tambayar kurilla?kiban amsakai tsaye zan fahimta sakeena.tace to aikobangayamiki ba kinsan amsar tambayar zainab shinaso afarko kuma shine a qarshe.idan kuwa hakanebaikamata ki cutar da kanki ba.kimanta da komai ki amince masa adaura muku aure.tace zainab kenan tona gode da kulawarki.tamiqe tana fadin don Allah kiyitunani karki bari dr yaqara kubucemiki.Ta juya ta bar dakin mama tayi shiru kanta sun kuyeduk gabobinta suka mutu,zainab ta sake fadowadakin. Ta firgita sakeena haba sakeena ki taimakibawan Allah nan koya sami natsuwa ko kin san haryanzu yana waje ta kara zaro ido banganeba doktayana waje kin kuwa san zai iya kwana a nan don hankalinsa ba a jikinsa yake ba ta sauke numfashitace na shiga uku ta mike da sauri ta fita zainab tabita kansa na kife bisa sitiyari ji kawai yayi an budemurfin motar ya dago kai ya dube ta ya zura mata idobaki sake ya kasa fadin komai ta gyara tsayuwa tacebaka san dare ke kara yi ba Ta juya tabar dakin,mama tayi shiru kantasunkuye.duk gabobinta sun mutu.zainab tasakefadowa dakin harta firgitata,sakeena!haba sakeena!kitaimaki bawan Allah nan kozai samu nutsuwakinsan haryanxu yana waje.ta qara zaro idobanganeba? dokta yana waje.kinkuwa san zai iya kwana anan,don hankalinsa baya jikinsa.tasauqenumfashi tace na shiga uku!ta miqe da sauri tafita.zainab tabita.kansa na kife kan sitiyeri ,ji kawaiyayi anbude murfin motar.yadago kai ya dubeta yazura mata ido baki sake,yakasa fadin komai.tagyaratsayuwa tace bakasan dare ke qarayiba?ya sauqe numfashi yace zantafi.tace yakamata kasan yanayingarin ko?yace hakane saida safe.tace Allah yatashemu.ta rufe masa murfin mota ya tayar yasakedubanta kamar yagayamata sirrin zuciyarsa ya tunamata baya,amma yariga ya dauki alqawari dan hakayadake kawai.yadaga mata hannu ya wuce.itama tana daga masa saida yabar haraban wajenm tadawo dakiba kwari ajikinta.batama san tawuce zainab tsayeba.Ta maida kofar ta rufe ganin haka yasa zainab itamata wuce nata bangaren ta kyaleta tayi tinani akanabinda take shirin aikatawa.kwanciya tayi bisa gadotunani ya isheta labarin daya bata kawai yakanta cikinranta.ta tausaya masa ta lalubo hotonsa ta zura masaido bata lokacin da kwalla ya zuba mata ba daren nan bata runtsa ba saboda tsabar tausayin al'ameen dayaransa.haka zalika lamarin yake ga al'ameen tundaya koma gida yakira wayar mami yasheda mata dukyadda sukayi da mama.ita kanta ta girgiza.sai daibatada abinyi illa tabashi haquri ya dangana..tundayace bayaso abbanta yasani dan karya takuramata.wanda hakan baisan abunda zaijanyoba.haka yakwana yana juyi da tinanetinane.kamar yabar garin yakeji.dasafe a ofis ya iskemutumin dr lawal.yazauna shiru yana kallonsa.drlawal yakada kai yace ai mukam mun shiga uku!tundasakeena ta dawo mana!yanxu shikenan haka zamu kasance a susuce?dafa ba yanxubane kasanalameen din yanxu ba yaro bane.122Yaja tsaki ina ruwan so da shekaru? yace waitsaya baku daidaita bane?ko tana da aurene?yacelabari ne mai tsawo ashe yaron nan asiri yamatasaboda taqi yarda dashi ya lalata mata rayuwartayakuma qi aurenta.ya rabata da iyayenta.ya ajiyetakamar dadiro.cikin wahala da kazantatciyar rayuwa abin babu dadin ji sai dai Allah yakawo qarshenabin.asirin ya karye.ance yananan yana hauka afandogari.amma ingaya maka har haihuwa sukayidashi saida yaron yashekara goma sha biyu yamutu.da wannn fa take ganin ita abar kyamace.tagaggaya min maganganu masu qona zuciya.wai harda tarkata kayanta ta gudu tabar karatun.tagudu harkaduna nabita na lallasota nace indan tanine tayihakuri na haqura.ya ce haba!bai kamata kayi hakabaai ita abar tausayi ce kuma dakai yadace ku zaunazaman aure.don wancan BAKIN CIKIN Yazama tarihi! HAUSA Novels BOOK BAKIN CIKI 3***10 Yace ita batayi wannan nazarin ba.amma tunda hakane sai mu mutu gwaraye!dr lawal yace a a Allahyasauqa kamutu gwaro nizanje nasameta.da sauriyace karka je dr lawal alqawari nadauka mata koabbanta bazaijiba.to saboda me?bayan kana sonta?yace bana so tabar karatunta dr lawal.kaga tunfarko abbanta karatu yaso tayi nazo na tusa matasoyayyata har wancan shirin ya russhe.yanxu kumatayi nisa sai inqara rusa shi? ka kyaleta kawai zandaure har zuwa lokacin dazan koma abina.daga nanbazata sake ganinaba.ina ganin hankalinta zai kwantataji dadin karatunta.ya numfasa yace Allah yazaba mana mafi alheri.yace amin zan qarasa ofis.tosai kafito yamiqe yafita yabar dr lawal yana girgizakai.kwana 7 suncika litinin tazagayo wa al'ameen adaddafe.domin gani yake kamar yashekara da zuwayanda nigeria tamasa zafi.komai akan qarfin haliyakeyi.amma hankalinsa nakan mama.ko yau da wuri yazo ofis dan ya ganta kozaiji dadi aransa.kowa yazoya tarar dashi ne azaune a ofis yanata fama da (laptop),A hankali masu jinya suka cika wuri masu raba(folder)suka rarraba kamar kullun sababbin zuwa susuke ganin baban likita kuma mutun hudu ake bokinko wane wata saboda dadewar da ake wajan bincikeakan kwashe sama da awa biyu ana ganin mutumdaya, dalibai suka iso cikin ayari kaman yadda suka saba suka kutsa kai ofishinsa. Bai iya dauke idon saga kallon mama ba hasalima wani banzan kyau tayimasa ga rigar likitocin ta kara mata kwarjini bayansun gama sa hannu kowa ya zauna aka fara karatugaba daya ya tasa mama da tambayoyi kuma idonsabaya daukewa akan na ta koda bada ita yake magana ba ma'ana dole ne duk bayan yan sakwanni ya dubiinda take zaune anan suka kai karfe daya kamaryadda suka saba suka sallame shi kowa ya ficemama na tsaye rungume da wani (file) a hannunta yazuro mata ido jim kafin yace yaya dai ta matso ahankali ta dora masa file din hannunta akan tebur ta juya da sauri tabar ofis din ya bita da kallo ya rasa mezaice har ta fice ya jawo file din ya bude ya daddagetakardun dake ciki daya bayan daya ya karanta kafdin su sakamakon gwaje gwajen da aka yi mata ne aegypt kansa ya daure mene ne nufinta na kawo masafile din yakasa warware dalilin... -Amma a hakikanin gaskiya kai zan kawo mawa don ka gani a matsayinka na mijin da na yanke shawarar mika wa amanta Allah ya tsare ni dokta ba'a sami cutar komai ba a jiki na zaka iya hakuri dani a matsayin matarka ba tare da tunanin na taba haihuwa a waje ba tsawon sakwan biyar yayi zuru yana kallon a idanuwanta jajur taf da kwalla murya dishe ya ce idan zolayata ki keyi ki bari sakeena please kar ki yi wasa da rayuwa ta kwalla suka zubo bisa kuncinta tace ba wasa bane dokta zainab tayi kokarinta ta gaya min gaskiya haka abokin ka dr lawal zuwansa uku gidan nan yana jawo hankalina akan abinda ya sameni ba hujja bace ta kin yin aure na kuma tabba ta ko abba yaji wannan maganar zai so mucika wa juna alkawari shi yasa na hakura na yi niyya cikin raina da yardar Allah baza mu mutu gwauraye ba muddin zaka kare min mutuncina wajen danginka kayi min alkawari ya dafe kirji idanuwansa sama yake fadin Alhamdulillahi Allah na gode maka da ka nuna min wanna rana dana dade ina mafarkin zuwanta kawai gani tayi ya zaro waya ya nemo wasau lambobi ya kara wa kunnensa tayi zuru tana kallon sa dukkansu kwalla ke bin kuncin su jimawa kadan ya fara fadin wa'alaikumus salam mamina albishirinki sakeena ta amince mami sakeena ta yarda zata aure ni tace godiya ta tabbata ga Allah ka gaya mata muna godiya yace zan gaya mata mami zan kira dadi in gaya masa ya fara shiri tayi yar dariya tace Allah sarki dan gidan dadi to shi ke nan sai mun ganka ya kashe waya ya dubeta sukayi wa juna kuri na tsawon lokaci yai dan murmushi yace sakeena har,126Yace sakeena har abada asirinki a rufe yake.kuma zaici gaba da zama a rufe har qarshen rayuwarki.duk wanda ya nemi ya tona miki sai naga iyakarsa.ina mai tabbatar miki qarshen sa zai zama tamkar na danliti.karkiyi kokanto ko kadan tunda ga fuska har zuciyaata alameen dinki