← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 79

Sashe 37

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baraka ke nan, Miss kakale! Ba kakale bane, gaskiyya ce kawai, daga kinta sai bata. Shi ya sa nake nuna mikita, don banson ki bata. Ta mike hannu daya kame da kugu, tace, nagode, ni nayi gida, kar Umma ta neme ni. Tasa kai tafice. Baraka ta biyota, ta sallami Inna ta rako ta iya zaure ta juya. Ta shige gida, tabar mama dauke da mamaki. Tai kwafa tace, kiyi da gwana yarinya. Ta kama hanya ta koma wajen Danliti, wasa-wasa sai da ta bata mini talatin anan, sannan ta karasa gida. Umma na zaune tskar falo ta sha tagumi, ta gaji Mama ta shigo babu ko tsoro ko fargaba tace, sannu da gida Umma. Inna saude na gaisheki. Ta zura mata ido ba tare da cire tagumin ba, jima kafin tace, da izinin wa ki ka bar gidan nan Mama? Ta mimmike kafa sosai akujera. Tace ai kinshifa wanka ne Umma shi yasa banyi miki magana ba. Umma ta numfasa, tayi hucin BAKIN CIKi tace, lallai kin isa mama, duk son danliti ne yasa kika zama maras kunya? To kibi a hankali, duniya zata koya miki hankali, muddin kika dauke ta kika goya. Ta figi gyalenta, ta mike cikin sauri tana fadin, Uhm.....! Ta wuce ta fada dakinta, tayi kwanciyarta. Umma ta kada kai, kwallah suka xubo mata, ta share tace, Allah kana kallo, munyi iya yinmu, amma shiriya na wajenka, kayi mana gaji Ya Allah. Nan Umma taci gaba da zama tana shan BAKIN CIKI tare da takaici mai tarin yawa har aka kira azhar, ta tashi tayi sallah. Abba ya dawo ta labarta masa, hannaye biyi ya kama kai, takaici kamar ya kashe shi, bai niyyara kara yiwa Mama wata magana ba akan Danliti, amma dole tasa ya kira tazo dakinsa ta xauna. Yayi mata kaca-kaca, sannan ya sa mata dokar fita ko'ina, duk da yasan ba dole bane tabi umarninsa. Tabbas hakan ne, yadda Mama ta fito dakin bakin nan nata ya kai wani gari wai shi ZUNTU. Shi kasna ya san rashin kunyta Mama ta kai wani mataki na kololuwa kwatance, ta xauna bakin gadon ta tana fadin a fili, wannan shine bature ke kira Impossible! Tunda kuka hana shi xuwa guna, dole inje gunsa mu ga juna. Ta saki wani lafiyayyen tsaki, ta yada kai bisa filo......... Maganar mama dutse. 7days kenan babu abinda ta fasa, muna iya cewa al'amarin kara haukata yayi. Domin a halin yanxun Mama bata shayi, agaban Umma zata dauki mayafinta, ta fice. Umma na kira, tana fadin tana xuwa yanxu xata dawo. Sau uku Umma na xuwa da kanta kofar shagon Danlinti, tana taso keyarta. Jama'a na kallon su, gwanin ban kunya. Sai da Abba ya hanata xuwa. Yace tasa mata ido, tunda ta zama gagararriya. Wannan abin kunya ya zama abin yayatawa awajen su hajjo, duk inda suka xauna xancan kenan. Babu abinda bai dawowa kunnen Umma ba, sai dai tayi kuka ta share hawayenta ta barwa Allah komai. Mama fa ta gagari kowa, suna ji suna gani mummunan labari na ta yaduwa har gidan Gwaggo Hausi. Daga can labarin ya mika gidan Marafa. Nana take mami ta tsani auran mama da Al-ameen. Shi kuwa Marafa nuna mata yake su daina kama jita-jita. Aure dai nufi ne na Allah, idan sakeena matar Al- ameen ce, bbu makawa xai aureta, idan kuwa ba matar sa bace si barwa Allah yayi masa zabin alkhairi. Duk da haka al'amarin yana jefa Mamai cikin tunani ba kadan ba, kuma da Al-ameen zai ji shawarar ta, da ta umarace shi daya hakura da sakeena, tunda shasahnci tasa gaba. Sallar la'asar ta kammala, amma bata bar sallayar ba, saboda gabatar da lazimi takeyi. Wata tasi tayi fakin kofar gidan, direban ya fito ya bude but, yana fido jakar kaya. Yana rufe but din, idanuwa na suka nuna min Al-ameen a tsaye ya cusa hannu gaban riga ya zaro kudi ya mikawa direban, yace, ka rike chanji. Ya sunkuci jakarsa ya wuce. Direba na xuba gdoiya. Ya tura karamin gate ya shiga, bakin mai gida har kunne ya taso da gudu ya amshi jakar yana fadin Maraba da oga! Fuskarsa babu walwala sosai, yace ya kuke? Lafiya lau oga. Ya shige masa da kaya falo. Al-ameen yayi sallama, muryar sa ta dauki hankalin duk wanda ke cikin gidan. Iya ta riga kowa fitowa, wa nakehi kamar dan Iya? Ya nufo ta fuska sake, ni ne iya, surprise ko? Ya dan rungumo tana fadin, ai kaki koya min turancin nan, da yanxun na gane nufinka. Yana murmushi ya rabu da jikinta, ya dubi Ladi, Hajiya Ladi ina fatan kunje kun duba min jikin sakeena ta? Tace muna dai shirin tafiya da hada tsaraba. Ya ce, baku da tsraaba? Gaskiyya kunyi min babban laifi. Tace, mun san hakan amma tuba muke. Ta ya kuke? Ta amsa lfya lau ya hanya? Yace, Alhmdlh. Yana juyo wa sukayi ido hudu da mami tana masa kallon mamaki. Ya nufe ta da sauri ya rungumeta, Mami na! Idanuwanta suka tara kwalla, ta kasa cewa komai har ya dago ya dubeta, yayi dan murmushi. Yace, nayi muku laifi Mami, kuyi min hkr na kasa daurewa ne. Tace nagode Allah da ya kawo ka lfya. Amma banji dadin xuwanka ba Al-ameen. Yace, na tuba Mami, ki duba halin da nake ciki, kiyi min uzuri. Ta dan kada kai. Tace, muje ciki ka sha ruwa ka yi sallah. Suka wuce yana tambayar Dadinda. Tace, xai dawo anjima daga kd. Yana xama Ladi ta shigo masa da ababen sha masu sanyi. Bayan ya jika makoshi, ya dubi Mami yace, ya jikin sakeena? Na daina kiran waya, don kunnuwa na ba za su jure jin mummunan labari ba, koda yaushe. Dalilin da yasa kenan, nace ya xama wajibi in xo inga halin da take ciki da idanuwa na. Dan hutu muka samu na sati daya, shine na yi anfani da wannan damar. Yaya yanayin jikin nata yake? Ta numfasa sosai kafin tace, jikin ta har yanxun a rikice yake, xan so ace Allah ya saka maka hkr, da dangana akan sakeena, domin kwakwalwarta ta jirkita Al-ameen..... Hauka Mami? Kina nufin sakeena ta haukace? Inna- lillahi wa Inna-illaihiri Raji-un! Idanuwansa suka tara kwalla, ba xan iya hkr da ita ba Mami, ko ba zata taba warkewa ba, sai na aureya. Alkawari ne wannan Insha Allahu ba xan karya wa sakeena ba. Tana ina ne yanxu? Ita ma nata idanuwan suka kawo kwalla. Ta ce, tana Fandagori, kuma ni ma xan so hakan Al-ameen, domin duk abinda kake so, nima shi xuciyata take matukat so da kauna. Amma al-amarin ya sauya salo, ka dauki kaddara kayi hkr da ita, hankalina zaifi kwanciya Al-ameen. Da gudu hawayen sa suka wuce bisa kyakkyawar fuskarsa, ya matso ta a hankali, ya dauko hannayenta biyu ya matse, ya dubeta ido cikin ido. Yace, har abada bana fatan in saba umarnin ku mama, amma ina rokon alfarma ki ban izini in cikawa sakeena alkawarin da daukar mata. Zan tafi samun nutsuwa, idan ina kallonta a matsayin mata ta kowane irin yanayin take. Ina rokon ki Mami ki taimaka min. Ya jingina goshinsa bisa kafadar ta, ya matse hawayensa tare da ajiyar zuciya mai karfin gaske. Haka maminsa ke cikin irin wannan yanain. Ta jima shiru tana tunanin zuci, tana son gaya masa gaskiyya, amma bakinta ba xai iya furtawa ba, saboda tausayin dan tilon dan ta. Ta yi ajiyar zuciya. Tace, nayi maka Umarni akan duk abinda yafi xama alkhairi Al-ameen. Mike ka je kayi sallah kaci abinci. Ya dubeta yana share kwalla. Yace, nagode Mami. Ta danyi murmushin dole. Jeka yi sallah. Ya tashi da sauri ya dauki jakarsa, ya fice. Mami ta raka shi da kallo, hannunta a kunci. Ta nunfasa kafin tace, Allah gamu gareka. Yana shiga, bangarensa ya isa ya yar da jakar hannunsa ya xauna gefen gado Ya kama kai hannayensa 2 yana yiwa Allah tasbihi. Jim kdan ya tura hannu aljihunsa, ya xao wallet dinsa ya bude ya xurawa dan karamin hoton Mama ido, nan da nan hwaye suka goce masa, bai ma san tsaninin kukan da yake ba har da shassheka, kamar xuciyarsa zata tsago kirjinsa. Allah da ikonsa, tamkar mami na da masaniya ta taso ta biyo shi dakin, don ganin a wane yanayin yake? Da sauri ta karaso ta zauna kusa ta shi ta rungumo abinta, idanuwan na tara kwalla. Komai ya sami bawa daga Allah ne Al- ameen, bai kamata ka xauna ka rinka kuka ba! Jin muryarta yasa hankalinsa ya dawo jikinsa, sannu-sannu hawayensa ya tsane. Ya dago ido jajur! Ya dubi Mami, yace mami ki amince min inje in dubo sakeena Yanxun. Ta goge masa guntun kwallan dake bisa kuncinsa. Tace, na baka izini Al- ameen, fargaba na kawai dare. Yace, kar ki damu Mami. Allah xai tsare. Shikenan, Ubangiji Allah ya sa ganinka ya xama waraka gareta, hankalin kowa yakwanta. Yace, Ameen Mami. Tace , To kayi sallah Maza-maza, don Allah kar ka zauna dogon tunani. Yanxun xan fito Insha Allahu. Ta mike ta bar dakin. Al-ameen Ya sauke numfashi, shima ya mike ya fada bayi, nan da nan ya watso ruwa ya dauro alwala ya fito. Bayan yayi sallah ya kimtsa, ya fito Mama ta matsa yaci wani abu, amma bai iya zama ba, gaba daya hankalimsa ya koma Fandogari. Sai dai ya sha Mamaki daya ga Mami ta nace dole ya tafi da direbanya, bai yi musu ba. Kai tsaye ya shiga mota direba ya ja shi suka dauki hanya suka bar Mami cike da damuwa tare da tunanin yaya al'amarin zai kasance idan Mama ta juya wa Al-ameen Baya? BAKIN CIKI 2*** 8 Ba su ido Fandogari ba, sai karfe 8pm, babu bata tym gidan Uban dawaki suka dosa. Ya shige sassan sa tare da sallama. Umma ta amsa ba tare da ankara da mai muryar ba. Sannu Umma. Ta dube shi da kyau, gaban ta yayi mugun faduwa, ta mike tsaye tana fadin, Al- ameen! Saukar yaushe? Yace, yau din nan Umma. Ikon Allah. Sannu da xuwa! Zauna mana, ya zauna yana amsawa. Kafin yace, ina yini Umma? Ta amsa, lfya lau ya karatu? Mun gode Allah, ya jikin sakeena? Tayi dan shiru, kafin tace wani abu. Abba yayi sallama ya shigo, duk suka amsa amsa
Chapter 37 · 0% Book details