← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 79

Sashe 10

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

BAKIN CIKI 1***6 Karfe bakwai da rabi na safiya wayar tebur ke ta bugawa a babban faln. Dawowar anti rabi kenan daga rakiyar mai gidan da yara da zai aje makrnta, kfn ya wuce wajn aiki. Can gefn wayar ta nufa ta dauka tare da sallama. Bai mance muryar da ya fara ji jiya tawaya ba, don haka ya zarce da fadn, "ina kwana anti?" tace, "lfya kalau, wa ke magana?" "al'ameen ne'. Take ta fara fara'a, "au Allah sarki, ya aiki?" "Alhamdu lillahi" "madalla, bari in kira ta" "to na gode". Ta aje kan wayar gefe ta wuce da sauri tana kira, "mama! Mama ki aje girkn nan kizo, mutumin naki ya bugo!". Ta fito daga kicn da sauri, suka hade a kofa. "wannan likita naki da naci yake" "kai anti!" ta fadi cike da fara'a. "ke dai jeki da sauri". Ta wuce tana drya, ta dauki wayar, daddadar muryarta a sanyaye tace, "hello!". Ya runtse ido yace, "hello 'yan mata ya aka yi?" tace, "kalau, an kwana lfya?" "sosai ma, har da miyan barci". Tayi 'yar drya, "kaji dadnka" yace, "har na kai ki? Nasan barci kike yi aka taso ki". "haba, kamar wata raguwa?" "ita ce mana. Kowa ya ganki ai yaga kalalatu" "kai kuma kalala ba" Yayi drya yace, "tun asuba nake tsaye ina shirn ofis. Na rataya neck tie, shine nace bari in kira madam ta daura min" Ta dan rufe fuska da hannu daya tana murmushi. Yace, "baki ce komai ba" tace, "to me zance?" "au ba zaki daura min ba?" tace, "na daura!" yace, "ga abu a wuyana yana lilo kice kin daura, don Allah ki daura min" Ya fada a shagwabe. Tace, "yau na bani! To rufe idnka". Ya kuwa runtse yace "na rufe" "me ka gani?". Ya danne kan wayar a gefn wuynsa ckn tunaninsa yake magana ido ruee, hannaynsa na aikin daura neck tie din. Yace, "ga ki nan kin fito daga dakn barci, kin zuba kwalliya da wani farin less, kin yi kyau bebyna. Sai murmushi kike min, kin kama neck tie din kina daura min........ "Wash!" ya bude ido firgigi, jin ya shake wuyansa. "menene?" Ta tambaya ido waje, ji tayi ya shagwabe, "Gaskiya ba haka ake yi ba, ba haka ake yi ba sakeena. Ai dai ba'a shake wuya". Drya sosai ta kubce mata, "ni na shake ka?". Yana sassauta daurn wuyn yana fadin, "da kyar fa nake numfashi, so kike in suma?" tace, "kaga zaka makara wlh, idan suka ma bulala babu ruwana". Yace, "ya zaki ce in tafi? Kin bani brkfst ne? Ga kofn tea nan a gabana, yi sauri ki ban insha in wuce". Tace, "oya, dauki kofi kayi bismilla". Ya dauka ya rufe ido yana kurba, yana ganinta ckn idanuwnsa, itace ke bashi. "ka shnye?" "minti daya, na kusa saura kadan". Ya kwalkwale ya aje kofn, "yauwa, na koshi". Tace, "good boy. To sai ka dawo ko?" "to me zan cewa zobenki?" "ina gaishe shi". Ya zura wa zoben ido, sannan ya sumbace shi yace, "wai yana amsawa". Tayi murmushi, "shikenan, tek care, ok?". Murya sanyaye ya amsa, "i will......." yayi dan jim, tace, "ina jinka!" ya rada mata, "I love u!". Ta dan numfasa tace, "me too!". Tayi saurn kife kan wayar. Da baya da baya ta tafi har ta jingina da kujera, ta wuce a natse ta zauna shiru, hannunta na gugar zoben yatsnta. A lokaci guda shi kuma al'ameen ya rataye kot dinsa, ya suri makullai da jaka ckn kuzari ya fito ya kulle gida, ya fada motarsa. Mai gadin rukunin gidajen ya bude masa get. Bayn sun gaisa ya mika masa dubu daya ya wuce. Mai gadi na ta murna tare da sa albarka. Shi kam kullm ckn sawa Dr. Al'ameen albarka yake, domin shi kadai yake masa alkhairi duk safiya, yace yaci abnci. Da ka dubi fuskar al'ameen zaka tabbatar yana tattare da farn ciki ba karami ba. Tamkar ynda mama ta kasnce babu sukuni sbd tsabar kewar al'ameen dnta. Bayn ta gama ayyuknta tayi wnka ta kimtsa, sai ta kwnta bisa gado ita kadai, bata aikn komai sai tunaninsa. Al'amarn kamar zai zautar da ita, domin da zarar ta tuna shagwabar sa, "GASKIYA BA HAKA AKE YI BA! Ba haka ake yi ba SAKEENA!! AI DAI BA'A SHAKE WUYA!". Ta kan yi kamar zata mutu da drya. Idan ta rufe ido shi take gani yana mata yawo tare da yin abnda yake fadi a aikace. Kai a hakikanin gaskiya al'ameen ya gigita zcyr mama, ita kanta ba zata iya fayyace ynda take ji ba game da so da kaunarsa. Duk ta kosa ya dawo ofis, don tabbatar zai sake bugowa taji muryar sa. Ilai kuwa yana shigowa gida biyar da rabi na yamma a gajiye, kai tsaye wayar ya dosa ya kira. Sai da yaji muryarta tsawn minti talatin, sannan ya daina jin kasala. Har ya sami natsuwar yin wnka, ya dan kwanta ya huta kamar ynda ita gimbiyar ta umurce shi. Haka suka kasnce suna renon jaririyar soyayyar su gwanin ban sha'awa. Ita knta anti rabi abin na birgeta har ta kan yiwa mama addu'ar Allah yasa ynda al'ameen ke ji da ita abin ya dore har ckn rayuwar aurnsu. Sun saba sosa, ba da mama kadai ba, da kowa na ckn gidan babba da yaro yasan al'ameen ta waya, kuma gaba daynsu babu wnda bai kosa sati ya kare ba, don al'ameen yazo su ganshi. Sai dai kash! Yanayn aiki bai shigo minna ba sai karfe takwas da rabi na safiyar asabar. Lallai ba karamin asubnci yayi ba, sbd tsabar kosawa kai tsaye gidnsu ya wuce. Kamar koda yaushe haka aka shrya masa tarba, amma sammaknsa yai matukar ba maminra mamaki, bata dai tmbaya bane don tasan daliln ba zai wuce na sakeena ba, sbd gaba daya wannan satin ita knta ta tabbata danta ya kusan zautuwa, duk wayar da zai bugo labarin sakeena yake bata. Suna gama gaisawa ya nufi kan waya, tayi zuru tana kallnsa tare da saurarn da wa zaiyi waya daga isowrsa? Tsammaninta ya zama gaskiya, iabin ran nasa ya kira ya shaida mata ya iso, kuma karfe goma insha Allahu yana nan karasowa. Dadi kasheta mana! Ta kamo su ameera abokn hirarta ta zayyane musu yaya zai iso anjima kadan, duk suka dauki murna da tsalle. Gagarumin shiri ya kankama, ta tsala ado na fita tsara. Kai mama akwai kyau, yarnya kamar aljana. Yaynta da anti rabi kansu kallnta suke yi, duk da cewar sun saba ganin ta, kuma sunsan mai kyau ce. Motsi kadan ta duba agogo, karfe goma taki yi mata sauri.!! Dan alkawarn kuwa goma daidai yana fakin a harabar gidan, abnka da dan gari adireshn da ta gaya masa tiryn-tiryn ya kawoshi gidn ba wata matsala. Ya fito yayi tsaye jikn motrsa,ba tare da yasan gimbiyr tasa na kallnsa ta tagar daknsu ba. Da alama bai san ynda zaiyi bane asan ya iso. Murya kawai taji a baynta ana fadin, "au leknsa ma kike yi?". Ta juyo a firgice, duk kunya ta rufeta, domin dai yaynta ne mai maganar. Tana murmushi tare da boye fuska a jikn labule tace, "a'a yaya". Yace, "zai fi kyau kije ki shigo dashi, ba leknsa ta taga ba". Tace, to, ta wuce simi- simi, yabi baynta da kallo yan 'yar drya. Ta kama hannayn yaran suka fito tare. Kiris ya rage al'ameen ya zube kasa, amma ilahirn jiknsa babu inda baya rawa. Da sauri ya tokare jiknsa damota ya zubo mata ido. Ita kuma sanyn gurin ne ya bugeta, ya ratsha ckn fatarta har ya tilasta wa tsigar jiknta tashi, sannan ta gane ashe bata dauko mayafi ba sbd daburcewar da tayi lokacn da yaynta ya kamata tana leke. Sbd haka ta duka ta dauki ameera, suka karasa gunsa. Fara'ar dole take yi a zahiri, amma gaba daya ta tsargu, sam bata ji dadn fitowrta haka ba. "oyoyo!" tace dashi. Ya sauke wawan numfashi, murxa a dishe ya amsa, "kema oyoyo!". Ya maida kallnsa kan yaran. Ya ci gaba, "ga abokina ameer, ga kawata ameera. Zo mana". Ya mika mata hannu. Da sauri taje gunsa tana drya. Ya mama ta iya? Haka nan ta dake tana jinsa da yaran, "wu! Kawata kina da nauyi sosai. Shekarnki nawa?" tace, "4" tana nunawa da yatnta. Yace, "kai kai kai! Gskya kin girme ni, amma don gata har daukarki ake yi. Antnki na sonki ko?". Mama ta watso masa harara, nufnsa ya ganota ne? Ko kuwa duk tsabar tsarguwar ce? Ita kuwa ameera drya kawai take yi. Ameer ya tmbaya, "dama kai ne yaya al'ameen din?" yace, "ni ne. Kana sona kaima?" ya makale a jiknsa yace, "ina sonka". Ya rungumo kafadarsa, "to Allah ya barmu tare". Yaynda ameera ita ma take faman fadin, "nima ina sonka yaya". Ya zura mata ido, yanaynta kamar sakeenarsa, nan da nan ya sumbaceta yace, "nima haka ameera ta!" Mama tace, "ya kamata mushiga daga ciki, surutn yarn nan ba zai kare ba". Ya zura mata ido baice komai ba. Tace, "muje mana" yace, "ai ke muke jira". Bata so ta wuce gaba, shi yasa tace, "Bismilla muje". Ya sauke ameera yana fadin, "bari in dauko muku tsarabarku ko?". Ya bude gidan baya ya kwaso ledoji 2 manya, ya mika wa ameera 1 yace, "to muje ckn gida". Yara suka yi gaba suka bar mama na ta nuku- nuknta.! Suna shiga falon kafin ya gama sallamar yaran ta sukake tabar falon, shi dai ya dagi kai ne bai ganta ba yaran suka wuce da ledar tsarabarsu. Ya aje ta hannunsa gefe ya nemi waje ya zauna yana maida numfashi domin har yanzu kirjinsa bugawa yakeyi shiyasa yana zama kasala ta rufeshi. Jim kadan Ya AbdulKadeer ya shigo tare da sallama Al-Ameen yayi wuf ya mike dauke da fara'a ya mika masa hannu suka gaisa suka tambayi juna aiki. Ya AK yace kuma harda dawainiya? Yace ahaba ba wani abu. Madalla an gode, zauna mana nizan dan fita ne saina dawo yace to a dawo lfy. Baiyi sakwan uku da zama ba Sakeena ta shigo jikinta rufe da mayafi hannunta dauke da tire cike da abubuwan sha gabansa ta aje, shi kuwa bai daina kallonta ba ta dago ta dubeshi suka hada ido tayi dan murmushi ta kauda
Chapter 10 · 0% Book details