Sashe 4
Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"mama kenan, sai ma kin tambaya? Matsalarki ai tawa ce. Ki sha kuruminki, insha Allahu by nxt year zamu sha bikin likitoci, ranar duk wani mai ciwo a fandagori zai warke" Ta fara dariya, "au dariya na baki ko? Kinag dai PANADOL shine tekaway dinmu, ANTI BIOTIC kuwa su kowa zai sha a wajen dinner, to ina cuta zata zauna?" Ta buge kafadarta tana kara darawa, "surutunki yayi yawa baraka, ubangiji ya cika mana burnmu" ta amsa da amin. A bakin titi suka yi sallama akan zata ji duk yadda al'amarin ya kaya nan gaba. Ta tsallako hanya tana tafe zuciyarta kunshe da sake-sake kala- kala. Wani lokacin ta kanji kamar kwalla zasu zubo mata sbd tsabar damuwa. Ta shigo gida yaran gidan sunyi nisa da karatun allo, kamar kullum. Malamin su ke zuwa ya basu darasi. Taja birki ta gaishe shi, ta wuce da sauri ta shige gida, ta mika wa ummanta dinkunan ta. Bata tsaya bata lokaci ba ta sungumo Kur'aninta da sauran littattafai ta koma wajen malam ta kwashi karatu. Sai da ta tabbatar karatun ya kama bakinta, sannan ta koma dakinta ta ci gaba da nazari. Hakan ya dan kauda mata damuwar da ta tsinci kanta ciki yau. Shi yas ma taki sassauta wa karatun, don bata son ummanta ta fahmci wani sauyi a game da ita. Sun Sallaci Isha'I sun ci abinci tana like gefen Abbanta Umma ke fadin wann karon kuma ina zaki hutu? Kanta tasye ta bata amsa wajen Ya abdulkareem zani. Baki sake take kallonta wai! Wai! Yau kuma aljanun can suka buga? Tayi yar dariya umma kenan ai dama ba wai bana son zuwa minna bane kawai Anti rabi ce matsalata kayita aiki kamar boyinta. Ta dan harareta uhumn ke kuma malalaciya uwar son jiki ba a haka ake koyo ba? Ta kada kai a'a wllh naje hutu kuma inyi ta aiki ina amfanin hutun ko Abba? Yace kyalle Umman nan kema kike zuwa gunsu kiyi zamanki wajen Abbanki inga me samin ke aiki. Umma tace oho! Shi zaki goya miki baya? Ta ai gidan wani zata aiki kam dole tayi shi ko anan dinma. Yace ok hakane? Kinga kiyi tafiyarki Abj wajen soja. Ta kada kai bari dai in tafi minnar Abba, kasan shima yaya yana ta korafi wai ban zuwa gun sa. Yace amma nasha mamaki..... Name Abba? Son zuwa minar nan koda yake duk yarinta ce take saki zuwa hutun nan da zarar kin fara jami'a ajewa zakiyi, Umma tace likita ba! Dokta Sakeena! Ta langwabe jikin Abbanta tana dariyar dole amma cikin ranta tausayawa junan su takeyi musamman Al-Ameen da kansa yake rawa yana ganin matsalar me sauki ce abin ya kara kashe mata jiki data dubi Abbanta taga yadda muraran fuskarsa ta nuna alfahari da kalaman Umma. Kwance bisa gadonta amma barci yaki yuwuwa dabarar ta taje hutu minna ko Allah yasa su kara ganawa da Al-Ameen koda Uban Dwk ya soke bukatarsa. Shin yaya zatayi ne? Mafita kam babu sai abnd Allah yayi. Ta kuwa kwana gayawa Allah don ya zaba mata abnd yafi alhairi. Ko karatu ko auren Al-Ameen wanda zamu iya kiransa mai sa'a gwarzon da yayi nasarar ciwo zuciyar Mama da yaki har take tunanin dama ace burin Abban ta aure ne bason zama likita ba. Shawara ta zauna kan jibi da yardar Allah zata wuce minna. Sha biyun rana daidai tana shimfide bisa gadonta tare da muguwar kasala, shigowar Uban Dwk gida dawowarsa kenan daga kewayen gonakinsa. Ya daga labulen dakinta tare da fadin yaya dai yar gidan Abba? Ta tashi zaune tana murmushi, babu komai Abbana har ka dawo? Yace na dawo Mamana lfy dai? Naga kamar jikinki a mace yake. Ta amsa Allah ya taimaki mai martaba lfy kalau Mamanka take bacci ne bai isheni ba. Ya karasa shigowa dakin ya tsaya akanta yace ni kuwa banason ki saba da yawan bacci Mamana kin fa san karatun da zakiyi mai wahala ne bayason lalaci ko kin manta ne? Ta dan rausaya kai tana murmushi ban manta ba Abba ko yanzun ma rashin abin yine yasa. Rashin abin yi? To taso muje in dai abin yine ni zan baki shi yanzun nan. Ta fara dariya meye shi Abbana? Yace ki zagaye tsakar gidan nan sau 12, ta kame baki wuuu! Abbba a tsakar ranar nan? Ai sai in zube sumammiya, duk suka dauki dariya yayin da wani matashin yaro yayi sallama sassan yace ana sallama da Alhaji. Umma dake waje ta karaso da sakon. Shi mutum ne me girmama bakinsa don haka bai bata lokaci ba ya fice don ansa sallama, wata zungureriyar marsandi ya fara cin karo da ita a kofar gidan sannan idanuwansa suka kai ga bakinsa maza su 2 a tsaye wanda kallo daya zakai musu ka tabbatar manyan mutane ne. Kai! Guda a cikinsu ma Uban Dwk ya sanshi farin sani kuwa domin fitaccen mutum ne a gwamnatin data shude ambassador ne 10yrs back, watau Alh Saifullahi Sodangi Lafai kuma marafan lafai. Take nan mamaki ya saukarwa Uban Dwk ganin cewa babu abnd ya taba hadasu na mu'amala. Cike da mamaki ya bisu da sallama cikn fara'a suka yi musabaha, sannan ya kira yaronsa Kalla yace maza ya bude masa falon baki. Can suka rankaya da bakin nasa, ya nuna masu kujeru yana fadin "bismilla! Kai sannunku da zuwa!" Sun fara gaisawa kenan kalla yayi sallama ya shigo da gorunan ruwan (Swan) bisa tire da kofuna, ya aje gabansu. Ya sake dibar gaisuwa ya fice ya bar falon. Uban dawaki ya shayar da bakinsa suwan sanyi. Bayan sun natsa Ambasada ya soma da cewa, "watakila ka shaida ni, watakila kuma baka taba sanina ba". Uban dawaki ya cafe, "farin sani kuwa, mai girma marafan lafai". Suka yi 'yar dariya, "babu shakka, to wannan kuma kanina ne uwa daya uba daya, alh. Nuhu lafai". Uban dawaki ya jinjina kai, "tabbas kuwa, ga kama nan, sannunku da zuwa" Suka kara amsawa, sannan alh. Nuhu ya zarce da bayani, "Allah mai yadda yaso, kuma shi yake shirya al'amuransa yadda yaga dama. Watau jiya yaron wajenmu yazo garin nan, domin mahaifiyarsa, ya kuma ga 'yar wajenka wacce ta tabbatar masa cewa ita 'yarka ce. A hakikanin gaskiya dai yaro ya gani yana kuma so da aure, shi yasa yana zuwa ya sanar mana, mu kuma muka ce ai babu bata lokaci dole mu kawo gaisuwa, tare da neman izini. Domin a haln ynzu bamu da wani buri da ya wuce Allah ya nuna mana aurensa, tnda ya kammala karatu har aiki ya samu. Don a gaskiya mun yaba da bayanin da yayi mana, yarinyar ta fito daga babban gida. Ina fatan za'a karbi kokon barar mu? Go to Home BAKIN CIKI 1***3 Uban dawaki yayi jim, shiru yana tunanin me zaice da manyan bakinsa da suka wanko kafa takanas takano suka zo da babban alkhairi gidansa? Girma da kwarjinin Marafa sun cika masu ido, har ya rika ji ckn zuciyarsa bazai iya kabar da kokon bararsu ba. Amma abin tambayar shine, ina burinsa na tuntuni da ya kwallafa akan mama? Tun tana ckn zanin goynta? Muryar ambasada yaji yana fadin, "nasa daliln shirunka alh., Al'ameen yayi min bayanin komai game da burinka na sakeena tayi zurfin karatu. Wannan kuduri ne mai kyau, kuma ni kaina ina sha'awar hakan. To amma ina son in tunasar da kai cewar aure baya hana ilimi. Ina roknka da ka tausayawa halin da al'ameen ya shiga na fadawa tarkon son sakeena. Shi kadai gareni alh, kuma daidai gwargwado soyayyar da na nuna masa bata gurbata tarbiyyarsa ba. Yaro ne mai ladabi da biyayya ga kowa, tare da tsananin bin dukkan abnda muka umarce shi. Dalilin da yasa kenan nima nake tsananin son abnda yake so. Bana sanya wajen taimaka masa da addu'a, a duk lokacn da ya tsinci kansa cikn wata matsala kamar ynda na lura ya shiga wani hali daga jiya zuwa yau da muka baro shi. Babu sukuni a zuciyarsa, alh. Ka taimaka ka amince wa al'ameen auren sakeena da zarar ta kammala sakandare, karatu kuwa ko wane iri ne, ko a ina ne sakeena zata yi shi da yardar Allah" Wannan dogon bayani na marafa ya kwabe wa uban dawaki guiwa, zcyrsa tayi rauni, ba zai iya ja da nufin Allah ba. Ya gyara zama sosai yace, "ba shakka naji duk abnda kuka fadi, kuma nayi farin ciki kwarai da gaske, sbd haka na amsa kiranku, duk da cewar ya kamata in shawarci sauran 'yan uwana, amma babu komai zan yi musu bayana idan muka zauna. Al'ameen ya ci gaba da neman sakeena, Allah ya tabbatar mana da alkhairi" Kawai gani yayi marafa ya daga hannu sama yana fadin, "Alhamdu lillah!" ya maimaita har sau uku, sannan ya dubi uban dawaki, "bansan kalmar da zan fada ba alh......." yayi murmushi, "ai ka fadi alh., tnda kayi godiya ga Allah". Ya jinjina kai, "haka ne, to mun kara godiya gareka Allah, ka nuna mana lokacin" duk suka amsa da amin. Alh. Nuhu ya zarce da fadin, "yanzu dame-dame ake bukata na gaisuwa da baiko?" yace, "kar ku damu da wannan, da zarar mun zauna da 'yan uwana zaku ji bayani insha Allahu". "to babu laifi, muna saurare. Ina sakeenar take? A kira min ita mu gaisa, don in cika alkawarin da na dauko......" "alkawari?" "kwarai kuwa, har mota ya biyoni yana fadin, don Allah daddy in kunje ku isar da gaisuwata ga sakeena, koda mahaifnta bai amince min auranta ba. To kaji, dole in cika wannan alkawari. A kira min ita inga farin cikn al'ameen" Farin ciki ya lullube uban dawaki, bakinsa har kunne ya mike, "Allah sarki, to tana zuwa". Yayi ckn gida da hanzari ya sami Hajiya Halima, "ina mama? Ashe bakin nata ne" tare da mamaki ta tambaya, "bakinta? Kamar yaya?" "zan miki bayani, je kice ta shiryo tsaf ta sameni falon baki". Ya juya ya koma. Ita kuma dakin mama ta wuce, gaban madubi ta sameta zaune tana shafe-shafe, fitowarta kenan daga wanka. Ta matsa gareta tace, "dama kinsan da zuwan wasu baki gunki?" "baki?" ta kada kai, "daga ina umma?" "ni zaki tambaya? To kiyi maza suna falon baki inji abbanki". Ta juya ckn juyayi ta fice. Mama kuwa kasake tayi tana tunani, "baki?" Al'ameen ya fado mata