← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 79

Sashe 48

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

turo kofa ta shigo sa sallamar ta dauke da uwar jakar kaya babu wanda ya amsa mata ta wuce ta gabansu ta tsugunna tace sannu abba, wani irin kallo yayi mata mai isar da sakon haushi da takaici kafin yace daa ina kike?ta dan sunkuyar da kai tace naje gaya wa Danliti sakon ka ne ai na gayawa umma kafin na fita ko um..."Ya daka mata tsawa rufe min baki don ALLaH shine zakije ki zauna har bayan magariba kiji tsoran ALLAH mama ki sani cewar mutuncinki ki ke zubarwa wannan uwar jakar da kika shigo da ita tawace tukuna? idanuwanta suka kawo kwalla ta fara rawar murya na...nawa ne.. Kayan da...Danliti ya siya min ne yace to ba a gidan nan ba idan yazo ki maida masa kayansa ya baki can gidan sa,ai kinji ni ko,?ta amsa da kai umma ta cire tagumi ta kare mata kallo sannan tace Alhaji ya kamata a tuhumi yarinyar nan idan idan tabada kanta gareshi kasan istibira'i ya kamata, kafin a daura auransu domin ni banyarda da mama ba a yadda suke tare da yaron nan,ya numfasa ciki da bacin rai yace ki na da gaskiya don ni ma wallhy ina wasi wasi cikin raina ke mama ki gaya min tsakaninki da ALLAH ki fi jin tsoran sa akan komai na duniya ki gaya min gasjiyar abinda ke tsakanin ki da Daliti kar kisa muyi kuskure da gangan idan kin san da wani abu to ki gaya mana mubi tsarin da ALLAH ya shimfida. -sosai ta goce da kuka murya na rawa tace ALLAH abba babu abinda ya shiga tsakanina da shi duk sukayi shiru suna dubanta kamar sun gaskanta ta kamar basu yarda ba amma dolensu yarda tunda basu da wata hujjar kama ta don haka abba ya daka mata tsawa ya isa don ALLAH tana wani bare baki kamar mummuna tashi kiba mu wuri kuma na gaya miki yana zuwa ki maida masa jakar kayansa,ta goge hawaye ta dan sunkuyar da kai tace yace ya gode insha ALLAH zai turo din suka yi banza da ita shiyasa da dago ido ta dube su uwar hararar da ta yi arba da ita tilas tasa tayi saurin maida kanta kasa jim sun kikara cewa komai yasa ta mike simi simi ta janye jakar ta, ta wuce daki bakin nan tamkar na agwagwa kai tsaye bayi tashige tayi wanka ta dauro alwala ta fito ana ta kiran issha'i,don haka tana yin magariba ta dora issha'i bayan ta kammala ta fito neman abinci nan falo sukayi kicibis da yaya ali wai me ki ke nufi baza kizo kiga amarya ba?ta kama kugu hannu biyu tace wannan amarya an damu nazo na ganta hala tafini kyau ne ya kama dariya kafin yace soosai kuwa tafi ki kyau muje ki ganta tace haka yake amma duk kyanta dai ni aka fara so kifin ita saboda haka a daga min kafa inci abinci tukuna"kalamanta sun ruruta wutar zuciyarsa ba kadan ba koda ganin yadda jikinsa ya saki kasan ya fada wani yanayi ya zura mata ido hannayensa rungume a kirjinsa murya sanyaye ace zancan ki dutse yar uwata,.
Chapter 48 · 0% Book details