← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 79

Sashe 13

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

so ya bata min rai ne?" ya kada kai, "bana son kowa ya bata miki rai sakeena, kin gama shiryawa?". Ta amsa, "na gama. Ka ga kayan da mami ta ba ni? Sunyi yawa Dr, kace ta rage". Yace, "me yasa ke baki ce ta rage ba?" "kunya nake ji" "oh, nine mara kunya kenan?". Tayi dan murmushi, "ba haka nake nufi ba yallabai". "to ai mami tasan kinfi karfn wadannan tarkacen ne, shi yasa ta baki su. Gaba daya shopping din makarnta ne. Bari in zuba miki a mota ko?". Tace, "na gode!". Sai ga mami ta shigo. "mami barin in maidata gida, yaynta na jiranta zasu wuce". Tace, "yana da kyau! Sakeena na gode, a gaida min mutan gidan. Insha Allahu duk ranar da na shigo fandagorin zanje mu gaisa da umman taki". Tace to. Ya kwashe kaya ledoji hudu, mami ta riko hannayen yaran suka fito, tayi sallama da su iya. Har mota mami ta raka su, tana tsaye suka fice. Suna tafe a mota suna hirar Mami, zcyar mama gwanin dadi, surikarta na sonta, kuma ta nuna mata kauna. Yayanta na waje yana ta faman duban agogo. Al'ameen yayi fakin suka fito. Yaran suka ruga gunsa, take nan suka fara bashi labarin ina da ina suka je, kamar shi ma bai sani ba. Bayan sun gaisa. Yace mama tayi sauri ta fito da kaynta, don shi a shirye yake, ita kadai yake jira. Ta shiga ciki da sauri dauke da kayan da ta samo, sbd tana so ta nuna wa anti Rabi, kuma ta dibarwa su ameer wani abu. Haka kuwa aka yi, anti rabi na ta sa albarka, ita kanta ta samu mayuka masu tsadar gaske, da turare guda 2. Mama da yara suka fhto da kaya suka zuba. Hankalnsa a tashe yake. Ganin suna satar kalln juna, shi yasa yaya yace, "ina zuwa". Ya shiga daga ciki don ya basu guri suyi sallama. Ya zura mata ido yace, "sai nazo visting, Ok?"tace, "shikenan, ina saurarnka". "zanzo miki da pictures din da muka dauka ki gani". "to". Suka yi shiru sai kalln-kalln suke yi. Idanuwnsa tam da kwalla yace, "gskiya gobe ba don da wuri zaku wuce ba, zuwa zanyi. Ban ganki ba, banji muryarki ba. Anya kuwa zan jure?". Haka nan nata idanuwn suka yi ja, ta bishi da kallo, amma ta kasa cewa wani abu. Motsin fitowar yayanta yasa tayi firgigi, ta wuce da sauri ta bude mota ta fada. Muryar anti rabi taji bisa kanta tana fadin, "to matar likita a sauka lfya, ace ina gaida umma da kyau da kyau". Tace, "zata ji". Ameera kuwa kuka take yi zata bi ta. Hnkaln mama ya kara tashi, tace, "yaya mu tafi dasu mana" yace, "islamiyya ce bana son suyi missing, kyale su kawai sai wani lokaci". Ya ja murfin mota ya rufe, yayi mata key. Al'ameen ne ya dauke ta, "yi hakuri kawata, anjima kadan muma zamu bi su". Bata yi shiru ba, amma ta rage sautin kukan. Suna kalln motar ta bar harabar gidan, ameera kuwa ta kara wage baki. Al'ameen ya jefata a kafadarsa ya rungune, kirjnsa shima sai bugawa yake. Shi kansa yana bukatar rarrashin, shi yasa yayi tsaye jiki ba kwari. Tsawn lokaci sannan ya dagota ya share mata hawaye. "Manta da anti, ba ma yi da ita, tnda ta tafi ta barmu. Yi shiru, yi shiru. To jeki wajen momi, sai na dawo ko?". Tace, "yaushe zaka dawo?" "duk lokacn da nazo garin nan zanzo insha Allahu". Ya ajeta gaban mominsu, yace, "anti zan wuce, sai wani lokaci". Tace, "to mun gode kwarai da gaske. A gaida mutan gidan". "zasu ji". Ya wuce yana dagawa yaran hannu. har suka iso fandogari mama bata cikin sukuni ranta bace yake kwarai. Ganin Ummanta yasa ta saki jikinta. Kowane sassa umma ta turata, tace taje ta gaishesu kuma ta gaya mata an sulhunta. Gab da sallar magrib uban dwk ya dawo daga Kd gaba 1 siyayyar skul yai mata bayan isha' suka taru a falo suna cin abnc. Umma ta baje masa kayan data sami a gidansu al-ameen yasa abarka,sann yace ta aje su tukunna. Umma tace a'a Alh naga akwai abubuwan ci wadanda zasu iya lalacewa, yace banason amsar kayayyakin nan amma bakomai ki bata wadanda kike ganin zasu iya lalacewa kibar sauran. Tayi murmushi Alh ho! Abdulkareem yace danAllah kubar mata kayanta tayi amfani dasu. Menene? Aiba fata akeyi ba kuma sani kanka ne Abba babu abnd zai gagara koda an sami akasi karka da mu Abba. Nasan surutai sunyi yawa akan mama cikin gidannan haka bazai hana ta amsar kyauta daga masoyinta ba. Yace Allah ya shige mana gaba suka amsa da amin. Yayan yaci gaba da fadin gsky yaron nan yana son mama kullum waya sau 2 sau 3 wkend kuwa idan yazo tun safe sai yamma. Umma tace ai ta kare kuma tunda ba a waya a makaranta Abba yace baki tausayinsu kenan? Tace ina ruwana? Suka fara dariya mama ta hada rai. Abba yace ni inaji kyaleta kinji yar Abba? Ta kara matsawa gunsa ta lafe. Yaya yai yar dariya yace abin harda shagwaba? Ido kamar an matse kwado ba inji Umma. Duk suka fashe da dariya ita kuwa kukan shagwaba takeyi. Washe gari da sassafe karfe 8am tare da yayanta suka iso gidansu baraka sbd shima yanason ya gaida innarsu. Ta kuwa ji dadin zuwansa ita da megidanta su kuwa kawayen suna can kebe lbr ya tsunke kamar kurna na zuba. Ita dai baraka wangame baki kawai tayi tana mamakin wann kasaitacciyar soyayya data kullu cikin kankanin lokaci. Tabbas ta shaida domin itama na tattalin kayan skul da mama ta kawo mata sun ishe ta tafiya skul. Jaka inna tasa albarka banda alhairin da AK yai mata da megidan. Kafin ya gama sallama dasu inna mama da baraka sun sulale sun tafi gidan goggo wato kakar alameen. Harda manya goro guda 10 suka satowa inna cikin wanda take siyarwa Goggo ta nuna nata murnar taga kishiya suka bata goro ta amsa ta jujjuyashi tace na toshiyar bakine wann? Lallai kinsa in bar miki mijin. To naki wayon kenan? Suna ta dariya suka fito ta rakosu har zaure tana sa musu albarka. Suna fitowa suka hangi yaya tsaye yana jira suka karasa da sauri, yi hakuri yaya. Ina kukaje masu yawon tsiya? Baraka tace mun danje wajen wata kawarmu ce. Yace I see.. Daga zaure inna ke fadin kaji karya ko? Ni nasan gidan goggo Hausi sukaje kakar alameen. Ya kama baki yace Allah ya shiryeku. Inna sai wani lokaci. Ya bude mota ya shiga inna na fadin Allah ya tsare agaida Rabi da yara. Mama da baraka suka rungume juna sannan ta shiga mota tana yiwa inna sallama yaja suka wuce. BAKIN CIKI 1***8 Suna isowa gida, me mama zata gani? Motar al'ameen aje gefe guda. Gabnta ya yanke ya fadi, haka ma yayanta ke mamaki, "wannan ba motar al'ameen bace?" "ita ce yaya". "mama biyoki yayi?". Tayi shiru tana 'yar drya. Yana fakin yabe fadin, "kai wannan mutum yana damun kansa da yawa. Pls ki gaya masa ya rage sonkh, kaq ya zame masa illa". Ta sauke ido kasa tana murmushi, tana kuma murzar zobensa da ke yatsanta". Yace, "je ki mana, tnda ba zaki iya gaya masa ba". Tace, "yaya kenan". Ta fito yaynda yayan ke fadin, "nayi laifi ko?". Ta kada kai, "a'a wlh". Ba shi ckn motar, sbd haka ta tabbatar yana falo. Don haka ta wuce ckn gida. Ido waje tana magana, "umma sai naga motar al'ameen a waje?" tace, "nima haka abbankuya gaya min. Yana can falo tare da alhajin"". Ta nemi waje ta zauna har da tagumi. "au zama kuma zaki yi?" "ummi kince suna tare da abba, sai kuma imje?" tace, "to zauna. Amma kinsan dama ku yake jira ku dawo ya maida ki makrnta ko?". Tayi shiru. "saura kije ki shantake da surutu. Sannan ki gaya masa don Allah ya rage sonki, zai iya zame masa damuwa". Tuni take kallon umma ido waje, har ta wuce ta bata wuri. Ta zabga tagumi hannu biyu zugum! Tunaninta yaya zata yi ta dumfari al'ameen da wannan maganar? Tabbas ita kanta tasan al'ameen ya makance a sonta, da zai rage din da zata so hakan, don bata son duk wani abnda zai raunana mata shi. "Mama!" taji an kwala mata kira, ta dawo daga duniyar tunani firgigi, ta dubesu tsaye bisa kanta. Abba yace, "tunanin me kike yi?" tace, "ba komai abba". "to yana falo, kiyi sauri ki ganshi muce. Wai rokona yake in barshi ya kaiki, tnda duk hanyar daya ce. Nace masa a'a, ya barshi yaje gun aiknsa". Jiknta ya kara mutuwa, ta juya salalau-salalau. Yayanta na fadin, "ni dai nace ta gaya masa ya rage sonta. Dis is 2 much!". Abba yace, "duk wannan ma bai taso ba, amma a ganshi tare da ita a mota, ai zan shiga bakin duniya, kuma daga ckn gdn nan maganar zata fara. Ba ni a ckn wannan tsarin, ba wai kuma don ban yarda dashi bane. Je kayi wanka kayi shirn komawa". Ya wuce, shi kuma ya wuce sashn da ya kwana don yin wanka. Kwalla ta tsaya take sharewa a kofar falon, zallar tausayn al'ameen ne ya tilasta mata zubar su. So ba zai taba zama laifi ba, amma ya kamata al'ameen ya rika bi a hnkali, kar son da yake nuna mata ya zama laifi a wajn iyaynta. Sai da ta natsu sosai ckn ranta, sannan ta tura kofar ta shi shiga tare da sallama. Ya amsa yana kallnta, ta wuce ta zauna rai bace. Da sauri ya matso gunta ya tsuguna, "da inga irhn wannan fuskar taki gara na kwanta gadn asibiti sakeena. Gaya min waye ya taba min rayuwa ta?". Gaba daya tsigar jiknta sun tashi, ta dan numfasa tace, "kai da kanka ka tabani Dr." "ni? Me nayi?" "nasan kana sona Dr, ni kaina zan iya dafa Kur'ani in rantse. Wlh yadda kake ji haka nima nake ji. Bana son kana tsananta damuwa ckn son da kake min, domin ina jin tsorn kar wani abu ya illata min kai. Ganinka da nayi yau ya fadar min da gaba ba kadan ba. Wnda ya tabbatar min cewa zaiyi wuya jiya in kayi barcin
Chapter 13 · 0% Book details