← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 79

Sashe 76

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ka sha na firij dina babu sanyi yace to barshi kawai bari in tafi ya zubo mata ido suka kalli juna yai dan murmushi tace mene ne ya mike yana fadin nothing sai munyi waya ko ta kada kai a ranta race dokta ke nan ya wuce tanataka masa tana fadin ina sauraronka tara kashi har mota suka y irin sallamar sa suka saba yaja mota ya wuce ta tako a hankali daki irin son da ala- ameen yake mata shi yasa take jin kanta ita wata ce ta shige wankanta ta fito ta sauya kaya ta kwaso littatafanta ta baye a kasa ta fara karatu tana yi tana zuba hamma barci ne sosai yake son kamata gashi yamma tayi babu kyau yin barci a wannan lokacin don haka ta aje littafinta yunkura zata tashi da nufin fita wajen zainab suyi hira ko barcin ya fita idonta, wani sauti mai dadi ya fito wayarta alamun sakon ya shigo ta dubi wayar kawai ranta ya kwao mata zakin zuciyar tane tasa hannu ta dauko tana dan murmushi ta bude sako amma sai taga sunan yaya ali dake rubuce kamar haka, Assalamu alaiki ya kanwata sai yau nayi saranda na sauke hannayena daga rokon soyayyarki a yau na yarda na amince kin sami gwarzo jarumin da nake da yakinnin zai shaer miki hawaye tamkar yadda nake zaton zan miki shine nake da tabbacin zai rike ki babu gori balle mugun kallo ko zargin kin taba yin wata mummunar rayuwa a. Baya amma ina so ki aje a ranki wallahy wallahi!!! Wallahi!!! Al-ameen bai fini sonkiba sai dai zanyi hakuri ne saboda ke shi kika fi so a gunsa duk farin cikin ki yake to nima ina son farin cikin ki mama shi yasa na ke son abinda kike so ina muku fatan alkari tare da tayaku murnar sake haduwa da juna,,Yanyaki aliyu!! Hawaye kawai taji ya goce mata saboda. Tausayin yaya ali to doka tagumi tana kalubalantar kanta me yasa nake zama butulu akan son da yaya ali ke nuna min laifi na ne meyasa ban yarda. Na aure shi ba tun kafin mu sake haduwa da dokta ta goge kwalla ta kada kai abin ya dame ta kwari ta rasa inda zata sa ranta taji sanyi sai kawai ta nemo lambobin sa ta kira bugun farko taji muryarsa yana mata sallama murya na rawa take fadin don girman Allaj yaya ali kayi hakuri ka yafe min.. 148-yace mama kuka ki keyi me yasa tace dole inyi kuka yaya ali don ban taba sanin ni butulu bace sai yau komai ya faru laifina ne kamar yaya laifinki komai bana Allah bane tace laifina ne me yasa ban aure ka ba tun kafin mu sake haduwa da al-ameen kuma ni nasan kana sona fiye da tuna ni na me yasa na zama butulu akan soyayyar da kake nuna min ya numfasa ya dan kada kai yace saura reni da kyau mama ai yanzu mu ba yara bane dai dai gwargwado mun yi hankali gane komai shirin Allah ne ni nayi imani sabo dani ba mijin ki bane shi yasa aurenmu bai yuwuba alkawari ne sai kin auri al-ameen shi yasa Allah ya sake hada ku wallahi bana BAKIN CIKIN auren ki da shi illa iyaka ina ciwon rasa abinda ni nake so.. Abinda na rubuto miki a sakona har cikin zuciyata haka yake Allah ne shaida na saboda haka ki manta komai ke yar'uwata ce ta jini abar alfaharina a ko'ina kar ki sake zubda hawayenki idan har kin yarda kin amince da abinda nake fadi kin yarda? Ta sauke munfashi wasu kwallar suka sauko bisa kuncinta tace na yarda da kai yaya ali ya ce to share hawayenki tasa bayan hannu tana sharewa kafin tace na share ya yi dan murmushi yace zamanin kuka ya wuce har abada da yardar Allah farin ciki muka fuskanta babu waiwaye yanzu gaya min ranar da kuka fara ganin juna duk a sume kuka fadi ko yasa dariya ta kubce mata ta cw wane irin suma yaya ali ah ya baza ku suma ba saboda murna ai so ba karya bane kanwata,,, , 149-tace hakane amma ina mai tabbatar maka shi din ma Allah ne yayi dole sai na aure shi wallahi da da gaske nake bazanyi aure ba sati uku muna dauki. Ba dadi har na bar makaranta saboda shi daga baya muka sasanta saboda abokinsa ya cika min ido yace baki kyauta ba kuma da kin zalunci kanki akan aikin banza don nayi rantsuwa kina son al-ameen to alhamdulilahi tunda Allah ya gyara komai sauranmu shan biki ko? Yayi dan murmushi ta sunkuyar da kai kin yi shiru. Tace me kake so in ce ki gaya min ranar shan shagali mu fara shirye shirye tace kaji yaya ali baku. Ne masu sanyawa ba yace eh gaskiya ne dama abba ya gayawa su baba za'a zo asa rana da zarar sun turo ni zan bada shawara kar asa da tsawo yaci gaba da dariya yaya ali ke nan yace ba dai kunya ki ke ji ba na sani to shi ke nan bari in kyaleki ki huta sai mun hadu a gida ko to shi ke nan Allah ya kai mu lafiya.. Yace amin suka danyi shiru jim sannan tace yaya ali ya amsa ina jinki ta sanyaya murya tace indan na gaya maka wata magana zaka yarda yace me zai hana tace ina sonka yaya ali ya yi jim shiru kana ya numfasa yayi dan murmushi yace to na gode ki gaida min angonki tace zai ji...bata karasa amsawa ba taji ya kashe wayar ta runtse ido tana mai da numfashi kwalla suka tsatso mata tayi sauri ta goge su ta jawo filo ta jin gina shiru tsawon lokaci sannan ta kada kai tace a fili Allah sarki yaya ali Allah ya kara maka dan gana haka zalika yaya alin jikinsa ya yi mugun mutuwa ya dade yana sakar zuciya sai dai kalmar da mama ta furta. Masa tayi masa dadi kuma ya tabbata duk lokacin daya tuna zaiji sanyi a ransa, 150- TABBATACCEN ALKAWARI duk inda ka duba kofar gidan uban dawaki jama'a ne kwatsam babu masa ka tsinke motoci kuwa sun tasar ma bakin babban titi zan so mai karatu ya tsamo mutum daya cikin wadannan daruruwan mutanen ku kwatanta irin FARIN CIKIN da yake ciki a halin yanzu kuma a wannan rana mai dimbin tarihi cikin rayuwarsu sanye yake cikin wani farin lallausan yadi yar ciki da wando hadi da mulun malun hula fara da farin takalmi. Fari hakan zai tabbatar da yanayin da yake ciki koba ka kalli fuskarsa ba,idan ka kalleta kuwa kai kace gonar auduga ne a haske da walwaki da annuri wajen kwatance,Ayi kurum ke nan tabbas shirun shine zaifi domin kwatancen bazai yuwu ba tsaye yake jikin wata makekiyar jeep yayin da wasu rukuni na manyan lokitici daga ko ina gida da wajr suka zazzagaye shi domin dai akwai wasu jajjayen kunnuwa su uku gab da za'a daura auren dr lawal ya sake ketowa da wasu tawagar bakin likitocin a matsayinsa na mai tarbar baki al-ameen ya tarbesu kusan dama sune kawai dr al-ameen yake zaton basu iso ba tawagar likitoci ne da wasu ma'aikatan jinya daga sakkwato ana ta musabaha baki yaki rufuwa kowa ka kalla ka san yana cike da farin ciki daga ciki kuwa waliyyai ne ke ta shirye shiryen gabatar da daurin auran cikin dan kankanin lokaci alhaji basiru ya mika amanar sakeena a hannun alhaji nuhu waliyyin dr al-ameen akan sadaki dubu hamsin... -nan da nan masu. Shela suka hau aikin su wasu tsofafin mata suka fara rangada guda makada da mabusan marafan lafai suka dirfafi ango rerawa suke yi abin sai wanda ya gani kwarai suka birge bakin turawan da ke tare da ango shiyasa suka zaro wayoyinsu suka fara dauka baya ga haka ga makadan nufawa nan birjik kowa na gwada basirarsa da kwarewar sa duk inda ango yake takawa kuwa kudi ne kawai yake zubdawa marokan da mawakan na kwashewa daga nan ma'aikatan hotel din da a ka kwaso daga minna da kaduna suka fara raba wasu manyan fararen ledoji guda biyu ake mikawa kawanne mahaluki dake wajan koda almajiri ne al-ameen ya bada umarnin a basji kamar yadda akaba kowa leda daya kayan kwalama ne dangin abubuwan da ake yi da fulawa watau (snacks) nama kala kala akwai na kaza rago da shanu jus iri iri da robar ruwa, dayar ledar kuma abinda rabonka ya tsaga domin dai babu abinda ba 'a raba ba,, Agogon bango da na hannu da wayoyin hannu dardumar sallah kai harda takalma da huluna turare masu zafi banda kana nan abubuwa irin su tawul hankici birorin rubutu da littafan addini da sauran abubuwa zaiyi wuya ka bude jakar ka ka sami kyauta kasa da iri bakwai can kuma sai ga wasu kananan yara suna raba wata yar karamar jaka mai ban sha'awa bakin jakar a tsuke take in ka bude ka sha dariya domin babu komai cikinta face SACET SACET NA PARACETAMOL nan. da nan abokai suka kaiwa ango don ya ganewa idanuwansa lallai yau shagalin na likitoci ne yana karba ya kwashe da dariya turawan wajrn na taya shi su kansu. Abin ya basu al'ajabi har daya daga cikinsu yace lallai wanda yayi kyautar nan yana da basira hakan yasa al-ameen ya duba sunan take nan yaga (CUT CEE BARAKA) ya kada kai yana yar dariya yace best friend din ta ce aka ci gaba da dariya tare da annashuwa mai yawa...... .idan muka shiga daga cikin gida kuwa ita uwar gayyar kusan can ake kankat.wajen ado tayi canji sama da talatin tun kwanaki uku dafara shagalin bikin.dole tasa domin angonta yasa mata kaya akwati goma sha biyu.ita kanta dataga kayan ciki saida suka girgizata.musamman kit din na kayan karas.mai karatu nabarka da tunanin ya suke?kusan yanxu abubuwa sun kawo karshe.tunda anfara neman amarya ana zagawa da ita gun manya dan su samata albarka.inna saude ke riqe da mayafinta.sasan gidan aka zaga da ita.iyaye suka tofa albarkacin bakinsu.daga qarshe akajata falon abbanta.inda gabadaya yayunta suke zaune shi.suna shigowa ta wuce jikinsa,yawan shekarunta bai hanata gaucewa da kukaba.shikuwa abban farin ciki! yasanya shi zubda hawaye.yau autarsa zata tafi gidan mijinta hartakai ga
Chapter 76 · 0% Book details