Sashe 45
Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
laifi ya dora masu ba har ya rinka jiran kalaman tubansu. Su ma fah yanxun ba yara bane, girman 'ya'yan su ya kai, ya gane shekarun su sun cika daidai matsayin masu 'yanci. Zuwan Ali da Ya saed don duba jikin Umma da kuma jin labarin Mama ko ta bayyana, Al-amarin bai yi musu dadi ba, ganin Yadda iyayen su suka ware ubandawaki suna masa yankar baya. Musamman Ya ali, hankalinsa yayi mummunan tashi, babu bata tym ya gurfana gaban abba yana bashi hkr. Daga bisani Ya saeed ya shigo falon. Ya ali Yayi rantsuwa da ace mama zata dawo ta amince da auransa, maimakon Danliti, a shirye yake a daura masu aure. Ko a gaban iyayen sa haka ya maida zancansa. Haj. Hajjo ta rufe shi da bala'i Allah wadarn wannan so kuwa, tunda yake hana ka kishin kanka. To idan ma mafarki kake yi, ka wanke idon ka, ka saurareni, idan har ni na haifeka, ba xaka auri ragowar Danliti ba. Wannan kalma tayi masa ciwo, bai san tym daya tasshi ya tabbatar wa su Haj. Hajo cewa kashe miciji sukeyi basa sare kansa. Domin ko banza sun kwana da mamakin Ya ali da yayi tafiyarsa, daga magana, shima ya gudun kenan? Ko mene nufinsa? Muna iya cewa matsalarsu ce, ko dama abba ya fadi kaddara na kan kowa....... Inna saude ke xaune gefen gadon tana mata fifita. Kallo daya zakayi mata, ka gane cewa ta jima tana fama da ciwon tsananin damuwa, domin dai ta fyade ta fita kamanninta. Amma hakan bai hana ragargazar shagalin bikin da akeyi cikin gidan ba. Nasan xakuyi mamaki, idan na gaya musu cewar bikin yaya Ali da Ya Sa'ed akeyi. Iyayeyn sun hur masu wuta, tun tym din da suka lura da take taken shi Ya alin, sam hankalinsa ba shi akan abinda zai fishshe shi. Shi yasa suka matsa kwarai da gaske akn ya fiddo matar aure ko su su fidda masa, ya kuwa tabbatar da mahaifiya sa xata ita. Gudun kar ta manna masa alakakai ya sa ya fito da yarinyar da ta dade tana sonsa a birnin gwari. Amina sunanta, kuma makwabtansa ne a gidan daya ke xaune. Sa'ed tuni yake tare da Hassana a kd. A yau ne maza suka daura auran 11am. Daga can suka wuce kd, inda xa'a daura na sa'ed bayan azahar. 8pm wannan rana motocin amare ke shigowa layin gidan angwayensu, haka daidai wannan tym motar Danliti parkn a kofar shagon sa dauke da tasa amaryar. Cike da mamki ayuba ya taso, ya bude kofar yana fadin, wa nake gani kamar amafarki? Wai dama kuna tunanin gida? Dan liti ya fito yayi doguwar miki, yana dariya, yace ah gamu kuma mun dawo, ya juya cikin mota ya cigaba da fadin, ya Gimbiya anan zaki sauko ko na karasa dae gida? Ta kada kai, tace, naji tsoro ya kamani Danliti, bansan yadda xanyi ba? Yayi 'yar dariya. Yace tsoro kuma? To me xa suyi miki? Ta kada kai bari dai na sauka nan, canm ajima na karasa gidan. Ya kace da dariya. Amma ke shirmen ki yayi yawa, to fito ki shiga ciki. Ta ballo murfin ta fito, kai! Anya kuwa Mama ce? Tayi wata shegiyar kiba ta kara ja, ina ganin shi yasa Ayuba ya xura mata ido, tym din da take mika masa gaisuwa. Danliti ya bude but suka ciro manyan jakunkuna guda 2 da kit, sai manya ledoji guda 3. Ayuba ya taimaka suke shige da su cikin shago. Kai tsaye dakinta shige ta xube a katifa. Duk suka biyo bayanta. Danliti ya xauna kusa da ita. Yace kin gaji ko? Tace kai dai bari, kamar in kwanta inyi ta barci wlh. To ki kwanta mana, ai ba kya jin yunwa ko kinaji? Ta kada kai, banji, to ki kwnta ki huta ne, xuwa karfe goma sai in tashe ki, ki koma gida. Haka za'ayi, ta jawo filo ta yada kai, suna kallon juna suna musayar murmushi. Ya lukuce mata hanci, yace baby na kenan. Ta juya gefe tana 'ya dariya. Ya mike ya dubi ayuba yace, to muje dogari. Ya juya yana murmushi, ina tsarabata? Yace yauwa ka tuna min, ya suri jakar leda suka fice da ita. Ya xauna bisa kujera ayuba na kan tabarma, ya zazzzage kayan kedar a gabansa. Gaba daya kayan sawa ne. Na gayu ya siyo masa, ya dube shi suka hada ido, yace ga tsarabar legos nan. Baki sake yace babu wai, har ma ga tsaraba nan duka naka ne. Ya washe baki m amma na gode, watau shi ya sana kunyi jajur abinku, ashe kuna bakin teku. Yace, hutu ba karya bane ayuba, ga kuma lafiyayyar bebi na, nake gaya ma. Yayi shiru yana kallon sa, fuskarsa gaba daya tabayyana babu abinda bai faru ba. Ya numfas duk jikinsa ya mutu yace, bakaji Danliti. Me nayi ma tukunna? Ko kaji surutu ne a gari? Ya gyara zama yace ba'a tonawa Danliti, abinda nake son ka da shi, ku sasanta ka aureta kawai, ka ba masu surutu kunya, donn sunce ba auranta zakayi ba, tayi saki reshe ne, ta kama ganye, ya shafa habarasa yace, ko? To ai ba suyi karya ba, shagali kuma basu ga komai ba daga nan ma illa masha Allah ba za mu daina ba. Ya kada kai yace, meye nawa a ciki? Idan ka huta ko xuwa gobe mayi lissafi. Yace ina fatan akwai kudi sosai, don wanda na tafi da su naci uabansu, ya amsa ciniki na na ba laifi, sati biyu ma da suka wuce na je kno na karo kaya da cinikin yafi haka. Da kyau mutumina, shi yasa nke sonka wlh. Yayi 'yar dariya yana daga kayan da aka kawo masa, ni kuma ina sonka da nutsuwa ba amma kakiji. Ya mike ya nufi daki yana cewa, kai ka fiye surutu, bari in baka wuri. Ya shige dakin ya bar ayuba da kallonsa. Ya kada kai yace aransa, Allah ka shiryemu. Shi kuwa Danliti komawa yayi ya hana mama barcin. Karfe 10 ta dan gota, dan liti ya umarci Mama da ta koma gidan iyayenta, su san ta dawo, dan su san matakin karshe da zau dauka. Watakila hakan su ta cimma ruwa. Watau su amince da auransu cewarsa madugu uban tafiyar. Ya hado mata kayanta taf! Da katuwar jaka, tana xaune tana kallonsa, kafin tace gaskiyya ba xan dauki jakar nan ba, guda uku kawai dauka cikin kit, in tafi dasu. Ido waje ya tambaya, sabda me? Ka sani ko su koroni? Ka bari tukunna mu gani, idan suka kyale ni, sai in dawo in kwashe sauran. Idan basu kyaleki ba fah? Sai na dawo nan ka yanke hukunci duk da zaka yanke. Ya xura mata do, ai iyayenki na san ba su ki karbarki ba, hasalima ai laifin su ne, na tabbata yanxun sun gane kuskurensu, dole su lallabaki. Ta doke kafadarsa tana dariya, har ma kasan dole su lallabani? Kai dai ka yi fatan su amince da auranmu. Yace shikenan, yanxun ki dauki abinda xaki dauka na rakaki, dare nakara yi. Ta bude kit ta xuba kaya kala 3, yasa hannu ya dauko wata 'yar karamar doguwar riga yace..... Yace ba xaki dauki wannan rigar ba? Tace wannan shegiyar rigar? Shegiya? Lallai ba ki san yadda take mi ki kyau bane, a'a ka dai barta anan, sanin kanka ne, su Abba bna za su barni na sanya taba cikin gidansu. An wuce wurin, ki barta kyasa a gidana. Ta yada kai kan kafadarsa tace ashe ka gane. Ya tsikare ta, ta mike xumbur! Ban fa so Danliti banso! Ta figi kit dinta, tayi waje baki a ture. Ya kwaso mata gyale da takalmi ya biyota yana fadin sorry 'yar bebi na! Taja ta tsya tana haraarsa, ya yafa mata gyalen, ya aje takalmin gabanta ya jawo kafufuwanta, sa abinki mu tafi. Ta xura kafar tace wa Ayuba, sai da safe. Yake yayi ya amsa, Allah ya kaimu. Suka fice, Danliti na cewa, har kin tabbatar da xamanki a gidan ne kike ce masa sai da safe? Tace gane min hanya wai, makaho ya so gulma. Ya ci gaba da dariya, suna tafe suna hira. Gab da gidan, ya tsaya sukayi sallama, idan kuma ya gan ta ta dawo shikenan. Y koma ita kuma taci gaba da tafiya hankalinta kwance yake, don bata saka komai illa in su koroto, ta koma inda ta fito. Daga bisani ma wata dabara ta fado mata. Tana dosowa kofar gidan, ta hangi kamar ana hada hadar jama'a, duk da dare ya fara yi, kana iya gane wa ana sha'ani a gidan. Bata yi wa kowa magana ba,a haka suma babu wanda ya shaidata. Sai da ta shige xauran karshe ta aje kit dinta, ta xauna akai ta hade kai da guiwa ta kirkiro kukan dole ta shiga yinsa har da shesheka, sannan hankulan masu wucewa ya fara xuwa gunta kuma, Ya ali shine mutum na farko daya fara dosar ta da tambaya, wai wacece xaune? Gida kike son komawa? A zata son cikin 'yan kawo amare ne, yayi dan murmushi, don ta bashi dariya. Da girmanki da komai kike kauyanci? Dan Allah tashi ki koma cikin gida tun kafain yara su fara miki dariya. Ko an yi miki wani abu ne? Daga ji ta gane mai magana, shi yasa ta dago sosai ta dube shi, kawai batare da tayi magana ba. Gabansa ya tsinke ya fadi xuciyarsa ke ambato sunan, mama? Sannan ya tsugunna gabanta ya furta a hankali, mama! Hawayenta suka kara tsunkewa, ta sadda kai, tana gogewa da bayan hannu. Innalillahi wa Inna illaihir raju'un! Ya waiwaiga babu mai kallonsa yayi sauri ya ja mayafinta ya rufe fuskarta, yace, taso muje, kar ki bari kowa ya ganki. Ya ja hannunta suka sulale dakinsy Danlami. Babu kowa cikinsa, duk suna can wajen fatin da sukeyi da abokansa. Ya xaunar da ita gefen gado ya tsugguna. Yace, yaushe kika dawo mama? Baki na rawa ta amsa, yanxun, idanuwansa suka kawo kwalla a raunane. Yace abinda kikayi kin kyauta kenan mama? Da mtuncin ki da komai? Iyayen mu masu girma da daraja a gurin jama'a, kika tozarta su? Haba mama, kamar baki sami tarbiya ba? Ta goge kwalla. Tace, ba haka bane, Ya ali me yasa zaku rinka