← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 79

Sashe 31

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

irin na yara. Tace, ya za muyi baban ameer? Dole mu rungumi kaddara. Ya mike babu isasshen laka a jikinsa, yayi mata sallama ya fice, batare da hajiyar ta kara ko motsi ba. Wucewar awa daya da rabi tana zaune xuciyarta cike da sake-sake iri-iri. Ji take kamar a mafarki abdul yaxo mata da wannan mummunan labari, wanda take ganin zai iya salwantar fa rayuwar dant tilon danta da takeji da shi. Duk fadin duniyar nan bata hada shi da kowa. Yaya marafa zaiji, idan wannan labari yake kunnen sa? Tabbas xai fita shga damuwa, domin yafi ta sanya Al-ameen ransa, ko alama baya son yaga ya nemi abu. Waya ta dau ruri a falon, ita ta katse tunaninta tare da haddasa mata faduwar gaba mai tsanani. Ta mika hannu ta dauka ba tare da tayi hasashen mai kiran ba. Tayi sallama cikin raunin murya. A raunane taji muryar Al- ameen ya amsa mata kafin yaci gaba da cewa, mami na, ashe sakeen ba ta da lfiya shine aka boye min? Ni ban ma yarda bata da lfiya bane Mami, kawai ku gaya min idan mutuwa tayi, xan hana Allah ikonsa ne? Ai nasan yafi ni sonta, kuma ta shi ce ban isa in hana shi amsat kayansa ba.... Tace saurareni Al-ameen, kar hankalinka ya gushe.idan baka yarda ba da maganar yayun sakeena ba, ai ni mahaifiyar kace, ba xan rufe maka komai ba, ka yarda ko baka yarda ba? Murya na rawa ya amsa, Na yarda mami, tace to sakeena bata mutu ba, rashin lfya ce ta sameta aka maida ta gida. Bana so ka damu da yawa, domin sosai take samun sauki, gobe ma xan sake xuwa in dubo ta, kaji? Ya numfasa yace, amma Mami me yasa za'a ajiyeta gida? Akaita asibiti mana, ko can xariya xanyi magana da abokina, na tabbata xai kula da ita tamkar ni. Pls mamy ki basu shawara idan kinje goben. Tace ba ciwon asibiti bane, shedanu ne suka tabata, kuma su iyayen nata suna tsye neman magani. Kai ma kasan xa su xauna ba. Ni dai rokona gareka shine ka nutsu ka kwantar da hankalinka, ka fuskanci jarabawar ki mai xuwa. Ka zama mai imani da Allah, shi xai sa ya karbi addu'ar ka idan kayi mata. Ka jini? Ya goge kwalla, yace naji mami don Allah idan kinje ki dafa kanta ki karanta mata ayatul kursiyu, falaki da nasi. Idan har gane ki ko da baxa ta iya miki magana ba, ki gaya mata Al- ameen dinta na gasheta, kuma xan ciga ba da yi mata addu'a har xuwa lokacin da xanji muryar ta a waya. Idanunwanta suka tara kwalla. Tace, Insha Allahu xan gaya mata, tare da dukkan abinda kace, muddin kayi min alkawarin zaka kwantar da hankalinka. Da sauri ya amsa, Allah nai miki alkawari mami, kinsan bani da wani buri daya wuce in faranta maku rai. Tace, Allah yasa dalilin alkawarin da kayi min Ubangiji ya yayewa sakeena abinda ya sameta! Yace, ameen Mami na! Dadina bai dawo ba ko? Bai dawo ba sai zuwa jibi. Yace Allah ya dawo da shi lfya. Ta amsa da ameen. Yace ki gayawa su iya su taya mu da addu'a, Allah ya taimake mu. Tace, xan gaya musu. Al-ameen, karka damu kaji? Murya raunane ya amsa, to mami sai kinsake jina. Bata iya kara komai ba ta aje wayar, domin muryarsa kawai ta isa jefa mutun cikin damuwa. Taci gaba da xama dauke da tagumi tunani na cin xuciyarta fiye da tunanin mai kallonta. Haka al-amarin yake wajen Al-ameen, domin dai rayuwa tayi masa tsauri kuma hasashen rashin lfiyar Mam yafi koma zama cikin ransa. Ba don yayi wa mamy alkawari ba, da babu makwa zai iya baro abinda yakeyi ya dawo ya ganewa idon sa Mama, tana cikin mummunan hali. Kafin kace kwabo, kowa ya fahimci samun sauyin sa, domin ya yamutse ya wayi garim duk kuzarin da nutsuwar sa basu jikinsa. Yana zaune addu'a yana tafe addu'a, haka acikin aji, hankalinsa yafi rinjayea ga addu'o'in da yakewa mama cikin ransa. 12pm washegari lokacin ne motar Mami ke fakin kofar gidan Uban dawaki. Yayin da mama ke kwance rankas ciwon jiki, sakamakon fadowar da tayi daga mota. Can da nan bata iya motsawa, Baraka ke tare da ita tana zazzaga mata nasihohi, duk da ta san bata sauraron ta, sai dai ya zama wajibi gareta, ta kara gaya mata gaskiyya. Mami tayo sallama falon ta shigo, gaban Umma ya yanke ya fadi. Ta amsa tana fitowa daga dakinta. Yake baki kawai takeyi, amma zuciyarta ta shake take da takaici tare da BAKIN CIKI mai tarin yawa. Ga wata kunya da ta yo wa idanuwanta dirar mikiya, mai alaka da ciwon dundumi. Sannu da xuwa Hajiya! Ta amsa mata da fara'ar karfin hali. Ta nuna mata kujera ta xauna, tana kara yi mata sannu da xuwa. Sannan ta debo mata abubuwan sanyi masu ruwa. Ruwan ta fara xuba mata, ta mika mata ta sha. Suka gaisa cikin girmama juna. Ta kara gyara xama, tace, sai kika ganni da rana tsaka ko? Fuska kunshe da tashin hankali. Tace ke dai bari, nasan kin sami sako maras dadin ji. Ta kada kai dauke da damuwa. Tace naji sakon da ya hani barci jiya, wanda ya sanya ni rama kafin safiya. Ina jajantawa shi kansa Al-ameen da ya sallama rayuwarsa kaf kan sakeena. Nayi kuka da wadannan idanuwan nawa, don na tabbatar da amsata ba alkhairi bace a gareni, domin komai zai iya faruwa ga tilon da na, farin ciki na kuma sanyi idona. Shi ya sa nace xama bai ganni ba, tilas inxo in rarrashi sakeena, ta tausaya min kar in rasa Al-ameen. Wadannan kalami sosai suka sanya hawayen Umma suka tsinke nan take, ta rasa me zata ce wa Mami ta sanyaya mata rai? Dole tayi kuma domin dai bata da kwakkwarar mafada, mama na nan akan bakanta babu sauyi. Da kunnunwata ta, taji lokacin da take gaywa Baraka tabbas zata iya kashe kanta, saboda Danliti. Mami ta cigaba da fadin ki daina kuka Hajiya, Baban ameer ya gaya min tashin hankalin da kuke ciki, kukan bashi da alfanu....... HAUSA BAKIN CIKI 2***4(TRUE LIFE STORY) umma ta hare kwalla ta katse ta Tabbas mama bata da lafia ciwon daya kamata mai tsanani ne maganin Allah, dole kuwa in yi kuka , don mama ta dasa mana BAKIN CIKIN da ban taba tunani ko mafarkin irinsa ba daga ni har Abban ta mu na cikin rudu tare da mamakin yadda wannan alamari ya kasanze haka, hakuri zakuyi hajia sannan ku taya mu addua mama kam ko ta so ko taki doke ta auri Alamin, tunda zabin ta ne na farko bamu muka cusa mata shi ba. Hasali ma bamu san lokacin da suka hadu ba. tsabat rashin kunya ce irin t yayan zamani da rashin sanin mutuncin mutane. saboda. haja hajia karki damu kuma dabarar da kikayi wa alamin tayi daidai sai dai akwai sauran rina akaba domin fadar kalmar ciwon ma ba zai bar shi yayi sukuni ba. Tace zaifi sauki akan a gaya masa gaskiar magana ni na dauki dawainiyar kwantar masa da hankali kullun ya kira waya. Tace to shikenan Allah yasa mu dace ta ce ina sakinar take mu gaisa Ta mike tana fadin Taso muje in kaiki kwance ma take bata iya tashi. Ah me ya faru? ina fatan ba dukanta kukayi ba, ta ce Baban Amira bai gaya maki bude mota tayi ta diro kasa ba? ido waje ta dafe kirji ta diro daga mota? tace ya wuce wai! zo muje ki ganta ta tashi dauke da mamakin tana fadin naga abinda ya ishe ni ni yasu, sakina da gaske take bata son Alamin. suka cusa kai dakin, baraka dake zaune bakin gado ta mike tana gaishe su. umma ta nuna wa mami wurin zama a bakin gadon tace zauyna hajia kinga idanuwan maras kunya ta juya kan mama taci gaba ga hajia nan tazo da kanta inkinga dama ki bude ido ta kudundune kai cikin pilli mami ta dube su tace ku bamu wuri hajia ita baraka suka bar dakin mami ta karasa matsowa tasa hannu ta birkito ta kuka taga tanayi tasa hannu biyu ta tallafo kuncin ta ta sanyaya murya tace sakina dan dubeni kinji? ta dago idanuwa jajur ta dube ta hawaye suka wuce bisa kuncinta. mami ta kara goge su . ta ce na san ba'a siyan so mama da yau nayi cinikin sa ko nawa ne na siya wa alamin, koda zai kasance zani daya zai rage min a fadin duniya. amma kash hakan ba zai taba yuwuwa ba, sai nayi imanin ko dan yaya ne kin san mahimamcin rike alqawari me yasa kika dauki alqawarin da ba zaki iya cikawa ba? me yasa kika yaudari shi kika bari tsananin son ki ya zauna a zuciyarsa? kina so ki kashe shi ne sakina? ki tausaya min ana gaya masa sakon nan zuciyar sa zata iya bugawa ya mutu mama. shi kenan na rasa shi kuma ban da wani alamin na sonki mama sai dai ayi zancen dan adam ssaboda haka ki gaya mani abubuwan da yake miki wadanda baki so har suka sanya ki tunanin fasa aurensa. wallahi nayi maki alqawarin zan masa fada tare da lallashi in kuma. gargade shi kinji? gaya man matsalarki da alamin. hawaye suka ci gaba da ambaliya bisa fuskar mama domin ko sunan alamin bata son ana ambatowa tsawon lokaci bata tanka ba sai kwarara ruwan idonta kamar zai kare mami ta sake fadin da alama alamin dai bai maki komai ba sakina tsuntsun son sa ne kawai ya tashi daga kansa ya koma wa wani ko? ta kara aje ido kasa mami tai wawan ajiyar zuciya idanuwanta suka kawo kwalla baki man halacci ba sakina a iya tunani na mutuwa ce kawai zata raba ki da alamin shi yasa gaba dayan mu muka dora burin mu a kanki. bamu da wami buri face Allah ya nuna mana ranar da zki zama mata danmu sai gashi dare daya kin juya mana baya. A tunani ki kinyi daidai? baki gudun kar amana ta ci ki sakina? kiyi tinani cikin natsuwa duk wanda ya ha'inci wani Allah ba zai kyale shi ba. zan barki kiyi tunani
Chapter 31 · 0% Book details