← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 79

Sashe 43

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya bata, suke karawa juna. Wannan karon da karfinsa ya kara mata, na hannunta ya karye nan da nan ta shagwabe, gaskiya ba hake ake yi ba! Ba haka ake ba Dr. Al- ameen! Al-ameen tsananin kiran ya dawo da shi tunaninsa duniya. A firgice ya dubi Mami dake gabansa xaune. Ba xai iya cewa ga tym da ta shigo ba, don haka yake mata kallon mamaki, haka itama ta xura masa ido mai dauke da questions. Mami! Yaushe kika dawo? Ta sauke numfashi ta kada kai, kafin tace, tsoron na Allah tsorona kar ka xaunce al-ameen ka dawo cikin hankalinka mana! Yai sauri ya runtse ido yana fadin Hasbunnallu wa ni Imal wakil, Allahuma ajirni fi musibati wa akhlifini khairan minha. Ya bnude ido jajur ya dubeta, kiyi hrk mami.... Takatshe shi ba xan bari rayuwar ka ta salwanta ba Al-ameen sai inda karfi na ya kare, Allah na gani yarinyar nan ta xalunce ni. Kafin yace wani abu, ta mike da sauri tai waje, ya bita yana kira, ba su hadu ba sai a dakinta... Mami.... Ta daga masa hannu. Ban son jin komai, ta mika masa wani ruwa da ke hannunta tace shnaye shi ka bani kofi. Yace na menen? Ban son tambaya ni na umarce ka kashanye, ka bani kofin. Ya daga kofin da sunan Allah, ya kafa aabki ya kwankwade. Ta karbi kofin ta aje gefe. Ya sake tambaya mami ruwan me nasha? Tace baba liman ya bani taimako na kawo maka, anjima zaka sake sha, gobe ka kara da safe da yamma. Jibi in Allah ya kaimu lfya za ka koma sch, domin fitar da dadin ka yayi bookin ya je maka, ina fatan kajini? Jikinsa yai sanyi, ya kamo hannnayenta 2 ya ja suka xauna bisa kujera yace Allah sarki mamina. Allah bar min ke. Nagode da karfafa min gwiuwar da kukeyi. Idanuwanta taf da hawaye tace, hankalina bai taba tashi ba irin na yau. Ban taba jin faduwar gaba ba irin ta yaukai da zobuna kake hira kana dariya, Al- ameen ban same xai faru ba nan gaba. Kafadunta 2 ya dafa yace sai alkhairi mamina, kawai xancen xuci ne ya fito fili mami... Tace daga haka sai tabin hakali al- ameen , yayi dan murmushi yace Allah ba xai sa ba mamina, ya san ni kadai ya baki, kuma shi mai tsananin tausayi ne. Allah sa ruwan da kika bani ba wanda xai cire min son sakeena bane. Ta xura masa ido cikin xafi tace, shine Al-ameen Insha Allahu sakeena ba xata zama ajalinka ba, ya numfasa yana murmushi da bai kai ciki ba mami kenan, wa ya gaya miki sakeena xata kashe miki tilon danki? Kuma wa ya gaya miki danki xai ji dadin rayuwa ba tare da soayyar sakeena ciknin xuciyarsa ba? Duka 2 tafiya suke kafada da kafada mami, Allah yayi hukuncinsa, don haka ban ji Baba liman xai iya cirewa. Bayin kaina bane, kiyi hkr mami. Tayi masa xuru duk jikinta ya mutu a hankali ta ce ko bai fita ba xaka ji sanyi cikin ranka. Tunaninn ka xai daidaitu da aikin kwakwalwar ka ta yadda xaka yi mu'amula kamar sauran mutane. Wannan shine farinciknm. Yace, Allah ya taimake ku akan burin ku. Nima ya taimakeni akan nawa..... Tace xamu ci gaba dayi da fada idan har kana gaya min irin wadannan kalaman. Ya kada kai ba xa muyi ba mami. To ka daina. Ya lumshe ido, ya bude yace na daina, Allah yayi maka albarka. Ya dora kansa kafadarta ya amsa da amin. Ta ciga da yi ma nasiha yana sauraronta sai dai can kasar xuciyarsa cike yake da xulumi, Allah ya sa ruwan da mami ta ba shi ya sha ba wanda xai sa ya mance da sakeena bane. Da wannan xulumin ya tafi yin sallah la'asar hankalinsa bai kwanta ba, sai da ya tura yatsansa ya arce makogwaronsa ya kirkiro wa kansa aman dole. Bayan sallar magriba dady ya shigo ya tsare shi yaci abinci. Sannan mami ta debo ruwan addu'arta ta mika masa, ya shanye. Allah Allah yake yi tashi ya koma dakinsa ya jawo aman, amma kmar dady ya sano ya ki barinsa tashi. Yayi ta jansa da hirarrakin duniya, wai don ya rage tunanu. Kafin ya bar wajen ya kwashe awoyi sama da 2 takaice ya ishe shi, don ya tabbata ruwn nan ya gama bin jininsa. Wannan karon bai nemi yin aman ba, gado ya fada ya fara tunanin iska, har bacci ya samuyi, da alama an fara samun nasara. Shi kansa yayi mamakin irin barcin da yayi bugu da kari ya rage jin xugin xuciyarsa ke y, hankali kwance suka yi karin safe. Mami ta kara bulbuo ruwan addu'ar ta a gora, ta mika masa. Ya kwankwada duk ba a son ransa yake sha ba, a yau takardun komawarsa Rasha xasu kammalu, haka dady ya gaya masa. Saboda haka ya umarce shi daya kasance cikin shiri koda yaushe xa'a iya basu tym din tashi. Jikinsa babu kasala ya koma bangarensa ya jwo jakar kayansa yayi ta lda kaya har da wadanda ya dade bai anfani da su ba. Ya wuce dirowar madubinsa ya jawo ya kashe takardun cikin kaf, dinsu ya dauko xai xuba jaka, wata ambula ta fado duk hotuna ciki suka watse bisa kafet daidadi shigowar mami dakin. Ya aje takardun gefen gadon yana amsa sallamarta, sannan ya tsugunna ya kwashe hotunan, akasarinsa duk na mama ne, sai kalilan wanda suke tare. Tayi tsye tana kallon katuwar jakar da yake lodawa kaya, ya akayi mami na? Tace kamar bada jakar nan ka xo ba? Ya mike dauke da hotunan a hannunsa yana amsawa, xan kara wasu kayan ne, shi yasa na sauya jaka. Ya matsya xai cusa hotunan, tayi wuf ta karbe ina xaka da dasu? Ai wadannan hotunan wuta ya kamata ka cinna musu. Wuta mami? Me ya san xan sa wa sakeena wuta? Saboda nan gaba xata xama matar wani, ka ga haramun ne gareka kallon hotonta. Ina fatan ka gamsu? Yayi shiru na 'yan dakikai kafin ya numfsa, ya dubeta idanuwan har sun kada, yace kin fadi gaskiyya mami, amma baxan iya cinna wa jikin sakeena wuta ba, sai dai ina rokonki dan girman Allah ki adana min su har xuwa tym din da xata halasta gareni. Tayi masa xuru tana shakku cikin ranta, addu'ar Baba liman batayi tasiri bane ko kuwa bata fara aiki bane tkunna? Ta kada kai ta dubi hotunan ta sake dubansa, amma shi ya riga ta magana. Mami pls ki ajeye min su inda ba xa su salwanta ba. Ta sauke numfashi, xan boye maka sun tunda kafi son hakan, gwaggo ce ta xo tana daki na. Ya ware ido sosai. Gwaggo? Da sasssafen nan? Dole tayo sammako, hankalinta a tashe yake, ka fito tana daki.Tayi waje da ambulan din a hannunta, shima ya biyo bayanta. Tana xaune a shimfida bisa kafet ya xube gabannta dauke da murmushi, uwargida ran fida, kuma sai ki bugo min sammako kamar ban aika da cefane ba? Duban tausayi take masa, ta dafa kafadarsa tace dole nai sammako, in xo in ga halin da kake ciki. Ina fatan xaka sanya dangana cikin ranka. Ka mance da yarinyar nan, domin dai.... Ya katse ta, ya kamata mu gaisa gwaggo kinxo lfya? Ya tsufa? Tace tsufa na nan kuma lfya lau na xo. Amma me yasa ka katse min magana? Babu komai gani nayi bamu ko gaisa ba, alhalin ya dace na fara gaisheki. Haka ne to ina fatan duk shawarwarin da kowa ke ba, kana ji ka kuma dauka? Ka manta sakeena... Da sauri ya katse gwaggo tuni na hkr da ita, hasalima yau ko geb xan koma sch. Ban xan dalilin katseni ba Al- ameen akwai abinda baka so na fadi. Mami ta amshe, sosai kuwa kina so ya mance da sakeena, kunnunwansa ba sa son ji, shi yasa yake katseki. Tace oho, to wahalar banxa kakeyi, domin dai labari ya tabbata tare da shashashan saurayinta suka tafi, kaga kuwa sai abinda Allah yayi. Gara ka kama kanka ka san inda ke maka ciwo. 'yan mata dai ga su nan birjik duk wacce kace kule xata ce cas. Rayuwa kawai sakeena ta xaba, don na tabbata yaron nan baxai aureta ba, nawa ya lalata, ya watsar tana gani kuma ta bishi, inm banda ita ma, rayuwarka ta sha banban da wacce sakeena ta dauka, kaga kuwa tafiyarka ba xata xama daidai da tata ba. Ka fahimce ni? Wasu kwalla masu xafi suka sauka bisa kuncinsa, hakan ya jawo mamaki ga gwaggo da Mami suka xuba masa ido baki sake. Xugum sukayi, daga bisani mami ta numfasa tace ikon Allah! Gwaggo ta xare tagumi tace, akwai sauran aiki, kuma ina mai tabbatar maka , bata tym dinka kakeyi. Ya jawo hankaci ya share fuska, yace, ko kadan gwaggo, labarin ki tsananin tausayin sakeena ya cusa min, sakeena ba haka take ba, nayi rayuwa da ita sosai na fahimci halayenta, xan iya cewa nafi kowa saninta, na fahimci halinta. ,Zan iya cewa nafi kowa sanin ta hakika ya zalunce ta tunda ya sauyamata rayuwa ya bata tarbiyarta ya gurbata mu'amalarta da iyayenta da yan uwanta ya datse tasananin soyayyar dake tsakaninmu ka ALLAH bazai kyale shi ba ta ko wace hanya ya bi yayi nasa a kanta sai ya ga sakayya,"ya mike da sauri zai bar dakin gwaggo ta kwala masa kira ya tsaya bakin kofa yana goge kwalla tace dawo ka zauna ai ban gama magana da kai ba yana daga tsaye gaskiya gwaggo kunnuwa na ba za Su iya sauraron irin wadannan labarurrukan akan sakeena ba,tausayin ta bazai barni sukuni ba gara a bar ni cikin bakin duhu ina laluben inda ALLAH zai sake hada fuskokin mu har ta zama mata a gare ni," jikin gwaggo yayi mugun sanyi tace dawo zauna nan ya dawo ya zauna gefenta ya hade kai da guiwa ta dafa kansa tace idan nayi kuskure kayi min afuwa amma ba laifi na bane ka sani ko wace uwa tana kishin danta kuma abinda ya faru da kai dole mai kaunarka yayi bakin ciki balle mu da muka fi kowa kusa da kai, na san kana son sakeena sai dai ba na son idon ka ya rufe ka kasa
Chapter 43 · 0% Book details