← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 79

Sashe 33

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

iya hakura da sakeena ba kowane irin hali ta shi ina son ta haka koda kuwa ciwon hauka ne ya kamata,Roko na gare ku shine ku taimake ni ku kai ta asibiti don Allah ko nawane zan kashe yaya please ku taimake ni ya goge hawayen dake zuba bisa kuncinsa yayin da jikin yaya soja yayi mugun la a sar cikin taushin murya yace kar ka damu al'ameen zamu kaita kar ka damu kaji sai da safe. Ko kamin ya gama amsawa ya kife kan wayar al'ameen sai da ya lalubi wuri don baya gani yadda ya kamata sauran abinda ke zuciyar sa kuwa biro na ba zai iya rubuce shi ba domin al'amarin gagarumi ne maras misaltuwa sai dai muce Allah ka kiyashemu sharrin masu sharri amin summa amin Anti amina keta faman neman ran mama shi kuwa yayanta bai sake komawa ta kanta ba dakin sa ya shige don yin abubuwan da yake ganin suna da muhimmanci a gare shi ita kuwa mama zafin. Mari da tsananin yunwa tare da tarin damuwa su suka taru suka jefa ta cikin doguwar suma awa daya da rabi ta kwashe babu motsin rai sannan ta dawo duniya,ta fasa kuka tana fadin wayyo Allah na zan mutu wayyo Allah! wayyo!" Nan da nan hawaye suka tsunkewa anti amina saboda tausayin da ya kamata murya na rawa ta tarairayo ta tana fadin mama ki tausaya wa kanki wannan mugun halin da kika jefa kanki kin kuwa ga yadda kamannin ki suka sauya wane irin masifar so ne wannan na bala'I. Akan da namiji kike wahalar da kanki a banza a wofi ki mutu ya nemi wata ya aura,wannan sakarci ne mama kiyi wa kanki fada tun dare bai miki ba sannan ki sani idan kika ci amanar al'ameen Allah ba zai kyale ki ba,ta fizge jikin ta ta sake faduwa bisa shimfida ta kara fasa kuka, malami ya budo kofa ya shigo cikin sanyin jiki ya karasa gun su yace mami uncle al'ameen ya bugo waya, kafin anti amina tace wani abu tuni mama tayi wuf ta tashi zaune cikin sababi take fadin ba za a zo ba kaje ka gaya masa bazan dauki wayar ba dole ne sai na aure shi nace. Ba zan aure shi ba duk ku taru ku kashe ni kowa ya huta ta sake komawa ta dase ciki anti amina da malami suka saki baki suna kallon ikon Allah. Jimawa kadan ta dube shi tace,Mu je falon." suka fice jiki babu kwari,musamman Malami da sababin ya bashi tsoro ba kadan ba.Anti Amina ta dauki wayar tayi sallama,suka gaisa kafin yace, Ya jikin sakeenar? Ta farfado kuwa? 'Ta farfado Al- Ameen, har ta samu barci. Ya sauke numfashi,'Allah ya kara mata lfy. To amin.yace Anti,don Allah ki taimaka ki tuna wa yaya tafiya asibitin.Ni ina ganin babu abinda zai gagari asibiti koda matsalar junnu din ne, akwai ta su irin gudumawar da zasu iya badawa. Please Anti a kai ta asibitin a gwada." Idanuwan ta suka kara tara kwalla,jin yadda muryar sa ke rawa,ta tabbata hawaye ne ke zuba bisa kuncin sa.Ta numfasa tace "karka damu Al-Ameen,duk wani iya kokari ana yinsa.inshaAllahu Allah zai dube mu ya yaye mata wannan lalura.ka kwantar da hankalinka kaji? Ya amsa,Hankalina ba zai kwanta ba Anti,har sai naji muryar sakeena da bakinta ta gaya min tabbacin samun saukin.Ban san halin da sakeena ke ciki ba Anti,kowa cewa yake tana samun sauki,amma ni ban ji alamun ba a jiki na.zuciya ta tana min sake-sake iri-iri akan sakeena kuma tana nuna min ita acikin mummunan hali.jin muryar ta ne kadai zata warware min rudun dana fada.....Anti Amina ta amshe,komai yayi zafi mgnin sa Allah Dokta.ka tsaya wa addu'a kawai ita ce kadai zata taimake mu.shi kenan Anti,ngd.Idan Allah ya kaimu gobe zan sake kira ko na dace jin muryar ta.Tace To Allah ya yasa a dace.ameen Sukayi sallama ta aje waya ta koma bisa kujera ta kama kai hannu biyu ta matse kwallan ta tace wannan masifa Allah ka yaye mana,muryar mai gidan taji yana fadin kema zai zauna kina bata lokacinki yau mu ma bazamu ci abinci ba ke nan Ta share fuska ta dube shi yallabai ba ka ki kalaman dokta bane su suka kara dafani wallahi ya ya zamuyi da yarinyar nan ne yace oho!ni kizo ki ban abinci ina jin yunwa ta mike ta nufi kicin shi kuma ya wuce ebur yana kiran malami ya sauko da gudu yana amsawa gani dadi kaima yau baza kaci abinci. Bane yace ai na ci dadi to koma daki kayi barci sai da safe,ya juya ya haye saman yayin da anti amina ta fito da jerin kayan abinci bisa tire ta jera bisa tebur sannan ta zuba masa taja kujera ita ma ta zauna yana ci tana maida masa kalaman al'ameen sai da ta kare ya kurbi ruwa ya dube ta, Yace ni kinga duk wannan shiriritar ina yi ne kawai saboda hajiyar sa ta roki a rufe masa amma ni ban ga dalilin yawo da hankali ba yanzu ina fa'idar yin shirun tunda hankalin sa da ake so ya kwanta bai kwanta ba? mama ko zata mutu shi zata aura to me ne ne abin jin tsoron gaya masa matsalar da ake ciki banda shiriritarku ta mata,ta ce ai ba haka bane yallabai kaga kuma shi kansa marafa ya goyi bayan hakan"shi ke nan sai ki yi ta rarrashinta kafin gobe idan ta amince yin maga da shi shi ke nan idan kuma taki kya nemi wata karyar ki shirya masa kinga sharo karya ya same mu ke nan sai abinda Allah yayi ina amfanin sa Ta numfasa tace al'amarin hakuri zamuyi tayi rokona gare ka don Allah ka daina dukanta wallahi taurin kai zai kara mata ido waje yake magana muddin tayi min rashin kunya zan tabbatar da na hukunta ta yadda ya kamata don ni ba sa'an ta bane,you know that so ba zan dauki iskanci ba kina iya hawa sama idan kin kare maganar,tace ran maza ya huce yallabai ba ina nufin wani abu bane yaci gaba da cin abincinsa bai tanka ba ta zura masa ido tana dan murmushi ta san halin yan kayan ta idan kayi magana kaji yayi shiru to kaima ka tsuke dan bakin ka ka kama kanka shi zai fi zama alkairi. Garin Allah ya waye,baya ga sallah babu abinda Mama ta aikata,ta yada kai bisa kafet tayi lamo kamar sumammiya.Gaba daya ta rame,fuskar ta ta tsuke duk ta bushe idanuwanta sun kode sun firfito waje, sbd tsabar kuka.Malami ya fito wanka ya tsugunna gabanta yace "鐭沶a kwana Anti?Tayi banza dashi,ya zura mata ido,Baki da lafiya ne Anti? Tunda ku ka zo da Daddy baki min mgna ba. Ta ballo masa harara,sai na tsinka mka mari ka sake min magana! Ta ja tsaki,ta juya kan ta wani gefen.Haushi ya kama shi,ya tashi ya ci gaba da shirin sa. Wannan karon kam bai gane kan gadon Antinsa ba. Me ke faruwane? Karfe bakwai daidai Anti Amina ta shigo,tana shigowa Mama ta rintse ido. Anti Amina ta dauko bisa kanta,ta dan dafa ta na san ba barci kike yi ba,ki tashi don girman Allah ga Dokta can ya kira. Kamar yadda na gaya miki jiya so yake yaji muryar ki,hankalinsa ya kwanta ko da gaisuwar sa ki amsa,zai ji dadi Mama. BAKIN CIKI 2***6(TRUE LIFE STORY) Ku da baku wurin in kun amsa.To Mama ta amsa. Haushi kamar ya kashe anti Amina.ta mike tsaye tace, kar ki tashi Mamaa,idan kin sake jin nayi mik閾� mgn akan Al-Ameen,duk abinda kika so kiyi min! Mts....... Ta ja tsaki ta wuce. Mama ta rakata da nata dogon tsakin anti amina ta waigo rike da kugu ta zubo mata ido,lallai mama,ni kike yiwa tsaki? Yayi miki kyau! Taja kofa ta fice.kan wayar ta duka rai bace. Tace, hello! Yace hello anti,ta tashi? Bata tashi ba dokta. (nace"dokto ka fiya nace dolene?) "ba matsala,ai barcin ma yana da amfani a gareta.zan sake kira,ngd ant閾�. Cike da tausayinsa ta amsa,kar ka damu sai anjima. To suka aje waya. Ta haye sama shake da haushi,amma bata nuna wa yallabai ba,don ta san ita zai tsatstsage danya. Iyaka tace da shi bata tashi barci ba Wasa wasa mama fa har ta sake kai bayan la'asar batasa kwayar abinci a bakinta ba hankalin anti amina ya tashi kwarai da gaske mama kam bata cikin hayyacinta gaba daya ta galabaita yunwa na neman tayi mata illa koma in ce tayi matan,shiyasa tana jin waya na ta bugawa taki dagawa don tasab mai kiran kuma bata da abinda zata gaya masa a hakikanin gaskiya ma hankalinta yafi rinjaye akan mama dake ta zama da yunwa tun safiyar jiya Tayi fada tayi rarrashi duk a banza misalin karfe biyar ta hada tea ta shigo da shi dakin wai ko Allah ya bata sa'a ta dan kurba me zata gani mama ke ta madedewa tsakar daki wata irin farar kuffa na hauhawa bisa bakin ta,tasaki kofin tea ta tarairayo ta tana sallalami kinga irinta ko mama nayi nayi dake kice abinci kin ki kina so ki kashe kanki a banza a rude ta sake bazamowa falo ta dauki waya ta kira wayar ofishin yaya abdul kadeea ta shaida masa halin da mama ta shiga Amma yanzu za a fara wucewa da ita asibiti nan take ya bata izini yace zai same ta asibitin babu baa lokaci soja daya ya sakata mota anti amina na tare da ita a gidan baya tana shafa mata ruwa a fuska sojan na jan motar an bata gado ga ledar ruwa na aiki a jikinta, wucewa minti talatin yayan ya iso ya same su jugum jugum,suna kallon ta rai bace ya watsa hannaye aljihu yace dama haka take so ba kuma shi zai taimaketa ba muddin tana motsin rai al'ameen ne mijinta so idan ta farfado ki fara gaya mata kafin na dawo zan koma ofis muna da mitin,tace to adawo lafiya ya wuce cikin kuzarinsa kuratan sa na biye da shi har bakin mota suka koma sannan guda ya bude masa ya shiga direban yaja suka wuce,anti amina ta ci gaba da zama dauke da tagumi zuciyar ta na mata saka iri iri haka wayar al'ameen ke ci gaba da bugawa cikin gidan ba
Chapter 33 · 0% Book details