← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 79

Sashe 49

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

BAKIN CIKI 2***13 hasalima rashinki yasa na aure ta koda yaushe ki kace da ni kule da sauri xan ce cas mama don son ki ya zauna a raina, tayi yar dariya tace yaya ali ke nan kar kasa amaryar ka ta tsane. Ni daga wasa sai ka hau jera zance!ba haks nake nufi ba yaya ali muje kawai naga amarya in na dawo na ci abincin bata jira yace wani abuba ta yi gaba abinta tilas ya biyo bayanta yana kada kai!Amare kam masha ALLAH suna dauke da tasu baiwar da ALLAH yayi masu musamman aminar yaya ali har mama na masa tsiya wai ya kamata ya maida sunan sa aminu dan su kara dacewa da juna kallon ta kawai yake yi cikin ransa shi yasan babu wacce tafi dacewa dashi face ita kanta maman,bata wani dade ba ta dawo sasan su ta dauko leda cike da kayan garar amare bayan ta gama cin abinci ta zauna gaban madubi tayi wa fuskar ta kwaskwarima tayi zaman jiran Danliti har barci ya fara dibarta bataji aiken yaro ba,ta kwana zullumi da juyayin abinda ya hana Danliti zuwa alhalin ya sami izinin yin hakan ko har yanzu bai amince wa ransa bane?ya gudun kar yazo ya fuskanci wulakanci!wannan tambayar taso ta hana ta barci domin ta kai sama da karfe dayan dare bata sami barci ba,Da sassafe ta tashi da ciwon kai wanda ya haddasa mata jiri akai akai duk da haka ko karyawa bata yiba karfe bakwai da rabi tasa kai ta fice babu wanda ya sani ta nufi wajen Danliti dauke da ledar kayan garar amaren da aka bata jiya ita ta tashe shi barci ya tashi a gigice yana tambaya lafiya kika bugo sammako haka?tace nayi zaton zaka zo jiya hira me ya hana ka zuwa. ya ja dogon tsaki ya kauda kai jim sannan ya juyo ya dubeta wai me ke damun kine?ba kinzo nan ba sai bayan magariba kika tafiba?to kuma me zanje in yi maki saboda ALLAH ta zura masa ido ya kare mata kwakwazo nan take idanuwanta suka tara kwalla murya na rawa ta ba haba Danliti laifi ne don ban gan kaba na biyo in duba ko lafiya?ya bita da kallo tana ta gugar kwalla ya kece da dariya kamar mahaukaci hakan yasa ta daina hawaye ta zuba masa ido yayi dariya mai isar sa sannan ya natsu shima ya bita da kallo to meye abin kuka ni ina can ina ta billayin neman mana waliyai ai banga ta zaman fira ba sakeena"nan da nan ta hadiye tashin hankalinta ta fara murmushi duk kin wani daga hankalinki don baki ganni ba jiya kawai " kawai ne? In gaya maka dai dai da sakwan daya bana son zama babu kai,yayi wata budurwar dariya yace ko to na kara baki tukuicin kaina ta kwanto masa tana dariya kasan ALLAH da ciwon kai na tashi ga wani jiri na diba na amma na kasa daurewa na fito ko karyawa banyi ba, yace ai ya bebi na sannu ko ya kamata mu karya ki sha magani bari inzo. Ya fice ya bar ta kwance bisa katifar wucewar minti ashirin ya dawo da soyayyun kwai da naman kaza da doya itama hade da kwai ta hada masu shayi suka batse cikinsu harda ayuba anan ta yada kafada daga fira barci ya kwasheta Danliti ya dawo shago ya zauna tare da ayuba ya zura masa ido yace don ALLAH ka tasheta ta koma gidan su yayi banza dashi ya fito yana zuba fito kamar katon arne. -Ayuba ya kada kai yace karshen alewa kasa Danliti idan an ciza a rinka hurawa ya ballo masa harara ya ce ba ruwanka malam ka kyale ni in ci lokacina ya tabe baki yace na barka zaifi kyau suka yi shiru kowa na harkan gabansa, a gida kuwa tunda suka shafa babu mama a dakin ta suke ta kwasar BAKIN CIKI don sun tabbata tana can shagon Danliti karfe tara uban dawaki ya gama shirin sa zai fita ko karyawa bai yi ba saboda tsabar takaici yasa umma ta fito masa da jakar kayan da mama ta shigo dasu ya sunkuta yayi waje da ita kalla ya tarbe shi da sauri ya amsa ya bude but ya saka Abba yace minna zasu tafi amma zasu tsaya shagon Danliti, kalla yaja mota suka wuce yayi fakin kofar shagon abba ya umarci daya fito masa da jakar nan kai tsaye ya wuce shagon lokacin da su Danliti ke ta harkokinsu yayi tsaye babu sallama har hankulansu suka juyo gareshi Danliti ya matso yana fadin sannu alhaji ina kwana yace nasan mama na nan tare da kai ina take baki sake yace tazo amma ta tafi yayi jim yana kallonsa kafin yace ba shi ya dame ni ba wannan ya rage kuda ubangiji ina fatan. Ta gaya maka yace ta gaya min kokarin da nakeyi ke nan na samu na turo yace kar ka bata lokaci domin na kosa na kauda kazantar da nake gani ya dan sunkuyar da kai yana murmushin izgilanci naji abba in ALLAH ya yarda zuwa anjima ko gobe zan turo yace shike nan ina sauraronka amma ga kayan ka nan ka aje idan ta tare gidanka sai ka bata ba na bukatar komai daga gareka sai sadakin da ALLAH ya wajabta ga jakar nan bai saurari wani abu ba yasa kai ya bar shagon ya fada motarsa kalla ya ja suka dauki hanya Ayuba ya matso gare shi yace, Allah na tabaka dama, don ka gyara kuskuran ka Danliti, kar ka bari ta subuce maka, ka dawo kana cizo yatsa. Ya watsa masa harara yace bana bukatar wa'azinka alaramma karfa ka manta da ni da kai duk daya ne. Na ma dai san abinyi, ayuba ya xuba masa ido ya rasa ta cewa babu abinda ya sami Danliti, yasa hannu ya dauki jaka ya shige da ita. Hannu 2 ya rike kugu, yana kallon mama xucyarsa na masa sake-sake. Kusan 5mins yana tsaye, sannan ta tsugunna ya bubbugata. Ta farka tana yamutsa fuska, menene? Tashi kiji? Ta yunkura ta tashi xaune, yasa hannu ya kara janyo jakarta, don ta ganta sosai. Cike da mamaki tace waya kawo ta? Yace, abbanki mana! Wannan kadai ya tabbatar min baya sona, baya kaunta. Bai dameni ba, amma me yasa zai uzzura min dole sai na turo magabata na yanxu-yanxu? Hankalinta ya tashi, ta matso a hankali ta dafa kafadarsa. Don girman Allah kar hankalinka yatashi Danliti.... Cikin sababi. Yace ki daina gaya min wannan maganar! Kora da hali abba ke min, saboda haka ki hkr, kije su baki wanda suke so! Tashi ki bar dakin nan, kar kuma ki sake xuwa, ni babu ruwana! Ta narke da kuka, murya na rawa tace, karka yi min haka Danliti, ina mai tabbatar maka xan kashe kaina idan ka juya min baya. (Kuji banza mtsw :(). Ya cire hannunta daga jikinsa yace, ni ban aikeki ba ya kamata ki gane ki gane ba dole bane na aureki. Don me xa a daga min hankali akan magabata? Banda su, uban wa xanje na tura idan ban nema ba? Kinga ki tshi kije ki gaya musu na fasa. Ta marairaice kamar ranta xai fita ni ina sonka Danliti ba xan iya rabuwa da kai ba, ai dai ni xa'a daurawa aurenko? Xan gaya musu su kyaleka, sai ka shirya. Shikenan? Ya kara murtue fuska, yana kallonta bai tanka ba. Takara matsarsa sosai taci gaba da fadin, muddin suka ki yarda da uxurinka wlh na yi rantsuwa xasu sha mamaki dan wlh nan xan dawo na tare..... Ok, ki sa a daureni kenan? Tace wa xai daureka? Don Allah ki kyaleni ni bana son surutu, tashi ki tafi kawai, sai na nemeki! Dan..... Ya daga mata hannu, idan baki so raina ya baci to ki tashi kawai ki bar dakin nan! Ta cigaba da share hawaye, ta xura takalmi ta dauki mayafi ta mike xata wuce, amma ta kasa, tayi tsaye tana kallonsa, don Allah kayi hkr Danliti. Ya dago ido ya dubeta, hawaye keta ambaliya, yayi dan jim, kafin yace nayi hkr, amma kije tukunna xan nemeki. Xaka xo gidanmu? Eh xan xo ki share hawayen, ba wani abu. Ta share da sauri ta duro bayansa, Nagode Danliti na! To kayi dan murmushi mana ko naji dadi mana. (mayya :() Ya banbare hannayen ta ya mike tsaye, karki damu da murmushina, muje in rakaki, kafin tace wani abu, ya fice, dole ta biyo bayansa, bakin shagon kawai ya tsaya, yace sai nazo ko? Tace, daga nan xaka tsaya? Xan wuce neman wadanda xan turo din ne. Nan da nan sanyi ya ratsa mata xuciya, baki har kunne. Tace, Allah sarki nawan, to sai mun hadu anjima. Ya daga gira yana fadin, sai mun hadun, yana sakin tsaki. Tana shigowa dakinta, ta shige, motsinta kawai Umma ta jiyo ta biyo ta dakin, tana kokarin cire kaya, don shiga wanka. Umma ta kare mata kallo, ta kada kai, tace don girman Allah mama ki rinka xama a gida. Tunda Danliti na sonki kuma abbanki ya bashi dama ai shi xai biyoki. Kullum inaga ya miki babu mutunci ga 'ya mace ta rinka bin saurayi har makwancinsa. Ko bai aikata miki komai ba jama'a ba za su dube ki da mutunci ba. Me yasa Danlit ya sauya miki tarbiya.? Tayi shiru tana ciccika tana batsewa, Umma tacigaba ni rokonki nakeyi, ki taimakemu ki taimaki kanki, don mu tsira da 'yar martabar da tareg mana a idon jama'a. Kinji? Ta amsa da ka, kafin tace, Umma idan abba ya dawo ki fada masa ya daina matsawa Danliti akan turo magabatansa...... Ta katseta kamar ya? To umma tunda an gayama sa kuma ya amsa xai turo din, ba sai asa masa ido ba? Ta mako mata harara, bangane asa masa ido ba? Shi daman can bai shirya auran ba, ya hanaki sauraron wandan ya shirya? To baku isa ba, mu ba wasa mukeyi ba, tunda ya hure miki kunne dole ya gaugauta turowa, ya raba da mu da bakin ciki da muke gani, kinji nagaya miki. Tayi ta tashi tana fadin, to shikenan ai matsa masa ba shine xaisa ya turo din ba. Me kikace? Ta shige bayi da sauri ta rufe kofa. Mama
Chapter 49 · 0% Book details