Sashe 73
Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ne wanda kikasani.ta kada kai tace bashi bane al'ameen dina saurayine,wannan kuwa harda furfura!ya fashe da dariya yana tambaya furfura?ina furfurar take? itama ta fara dariya gatanan ina gani bisa kanka!Allah sarki dr na ya tsufa!yace sakeenarfa?ai ita ma ta canza.taci gaba dayi masa dariya.yana kallonta kwalla suka taru masa ya numfasa yace Allah nagode maka da dr lawal da zainab.dasuka dage da farin ciki na ya dawo.sakeena kigayamin ranar da za'a daura mana aure tun kafin a tasheni daga baccin nan! 126Yace sakeena har abada asirinki a rufe yake.kuma zaici gaba da zama a rufe har qarshen rayuwarki.duk wanda ya nemi ya tona miki sai naga iyakarsa.ina mai tabbatar miki qarshen sa zai zama tamkar na danliti.karkiyi kokanto ko kadan tunda ga fuska har zuciyaata alameen dinki ne wanda kikasani.ta kada kai tace bashi bane al'ameen dina saurayine,wannan kuwa harda furfura!ya fashe da dariya yana tambaya furfura?ina furfurar take?itama ta fara dariya gatanan ina gani bisa kanka!Allah sarki dr na ya tsufa! yace sakeenarfa?ai ita ma ta canza.taci gaba dayi masa dariya.yana kallonta kwalla suka taru masa ya numfasa yace Allah nagode maka da dr lawal da zainab.dasuka dage da farin ciki na ya dawo.sakeena kigayamin ranar da za'a daura mana aure tun kafin a tasheni daga baccin nan! Yace sorry ba baraka yadace infara tambayaba ya umma dasu ameera?tadanyi shiru jim kadan ta dubeshi ido ya kawo kwalla tace umma ta rasu dokta.....yace what?innalillahi wa inna ilaihi rajiun.ciwo tayi?ta goge kwalla tace BAKIN CIKI Ne yakasheta dokta!umma takasa jure ganin halin qasqancin dana shiga.shisa bana son tunata.hankalina tashi yake tun lokacin shima abba yasamu matsalar paralise.andai samu yanxu hannun yana dan aiki amma baya tafiya a keke ake turashi.yace subhallahi Allah ya jikanta ya mata rahama.ta amsa ameen.ya miqo mata hankici share hawayenki kiyi haquri kinji?ta share fuska yana qara bata hakuri.sundan jima shiru kafin yace pls kidena damuwa insha Allahu abba zai warke idan har akwai yiwuwar hakan sai inda qarfina ya qare.ta numfasa nagode hira ta tsunke labarin bayan rabuwa sukeyi.kiran magruba dole ya miqe sukayi musayar lamba,yafito ta tako masa zuwa gaban motarsa.ya bude ya shiga,sannan yace to sai munyi wayako?tace ina sauraronka.ya qara zuba mata ido yace i love u! tace mee too!yace so much?tayi murmushi ta tura hularsa gaban goshi tace so much!ta juya tabar wajen tana waigensa.bakinsa har kunne yabar wajen, 128.tana karasowa ta iske zainab tana mata dariya.taja ta tsaya meyabaki dariya?ta daga gira ta kama kugu hannu biyu so baya tsufa,sai dai masoyan su tsufa kinga oganmu baki har nan?ta nuna da hannayenta mama tayi murmushi tana kada kai ke mayya ce zainab,wato ido kikasa mana ta window? zangayamasa.tace karki hadani da oga kisa ranar monday ya kasheni da tambayoyi.tana dariya ta tura qofarta tana fadin barinyi sallah.akwai abincifa kixo muci,tace sai na shigo ina jiranki kowacce ta nufi bangarenta.sannan suka hadu cin abincin karo na farko da mama ta gayyoto zainab saboda jin dadin shawarwarin data bata,har suka taimaka wajen dawo mata da farin cikinta. Haka al'amarin yake wajen dokta yana fitowa masallaci wayan dr lawal ya kira yagaya masa yana gida cikin yan mintoci dabasu fi ashirinba ya isa gidan.yana fitowa yaga dr al'ameen ya nufosa baki har kunne ya rungumesa.ya dubesa yaya dai likita?yace Allah yasaka maka da mafifi cin alheri!ya ware ido sosai yace amin likita meya jawo min wannan kyakkyawar addu'ar?yace ta amince dr sakeena ta amince zata aureni!ah haba?yace gaskia nake gaya maka,bansan irin godiyar dazan makaba dr lawal.ya numfasa yace yazame mini dole in taimaka maka.don na tabbata fadi kawai kake bazaka iya haqura da itaba.nima ngd Allah data dubi girmansa ta amshi rokona!nagaya mata bakai kadai zata kasheba. Allah kadai yasan mutanen dazasu mutu idan ta bari sonta ya wargaza mana kai.ko ba gaskia ba?abin ya dameni da yawa.koda kace kar insake mata magana najika ne kawai amma tunani yana kan yadda zanyika auri sakeena.muma hankalinmu ya kwanta.so yaushe tace zamusha bikin?ya rungumeshi yana fadin.bazan taba mantakaba a rayuwa dr lawal.yace to nima nagode.suka dubi juna fuskokinsu cike da annuri to yaushe zamusha bikin?yace tace wata uku amma gaskia yayi yawa munbarshi a sati uku.yayi dariya dr love!watau ku kuka sanya wa kanku rana koh? tsokanarka fa nake dakaji na tambayeka.ya zura masa ido yana yar dariya.wlh madam na fama da iya shegenka.to miye dan musa rana?ya tabe baki hannayensa cikin aljihu babu komai sa'ido ne kawai irin na lawal mushiga muci abinci.ko sakeena ta baka?yace banceba dr lawal.karka min sharri.suka shige ciki sunawa junansu dariya.dr al'ameen na fadin ranar sati zamu wajen abbanta a abuja shima sati uku zamu gaya masa.bakuda kunya shima sai kun nuna masa kun kosa?suka fado falo suna kyalkyala dariya.ah madam kenan!ta yunkura ta tashi tana murmushi oga ne dakansa?ashe yana dariya haka abokin naka?tana tambayar mijinta dr lawal.yace kingano kenan?ai sirrin zuciya a tambayi fuska.ko?yace hakane mana ke me kika fahimta kan fuskarsa?130.Tace wataqila sakeena ta janye gudumar data daga!yace shisa nake sonki mairo.akwai ganewa ingayamiki har sunsanya wa kansu rana!tace ahaba dai!?kace biki ya kusa.yace sati uku kinkuwa san akwai sonkai aciki suna nufin sun kosa.takama baki wai!maganar tafi qarfina.wannan tsakaninku ne.dokta ka zauna akawo ruwa ko?yazauna yana fadin kungama sharrin?toya yarana.tace suna lafiya tun dazu suke sallah yace yayi kyau.tace to congrats! muna murna Allah sa ayi damu yace amin madam.ta wuce yayinda dr lawal ke zama kusa dashi.kai mugun maasharranci ne wlh.yace rantse da Allah baka kosaba?ya zura masa ido yana dariya yace yo see! nasan bakada abin cewa nidai ina roqon likita pls nd pls karka manta wa wani almakashi acikin kai.arinqa ajiye sakeena a kofar tiyata.ya bashi hannu suka tafa suna kyayatawa kasamu ni dayawa dr lawal.amma ba komai gidanka naxo.maryam ta fito da tiren kayan abinci ta nufi tebur ta jera musu.sunata yankar dr al'ameen.yazaiyi?sai dariya kawai dan sunfishi baki.shiyasa yace wa dr lawal duk ka bata madam da sharri Allah shiryeku.ahaka suka gama cin abincin takwas da rabi yabar gidan yakoma nasa.can yayi sallar isha'i yayi wa Allah godiya ya rokesa daya nuna masa ranar dazai ganshi da mama a matsayin matarsa.yayi shiru ya rufe idonsa.wayarsa tayi qara ya dauka dadinsa ne.yamayar masa yanda akayi.dadi ya lullubesa.yasa musu albarka tare da fatan Allah nuna musu wannan rana da zata zamar musu abin tarihi a rayuwarsu.bai iya bacci ba dan daya rufe ido mama yake gani tana tura hularsa tana fada masa so much! ranar asabar akan hanyarsu ta zuwa abuja.kaduna suka tsaya makarantar da waleed yake (TURKISH INTERNATIONAL SCHOOL.)inda yake karatunsa makarantar kwana ce ta yaran masu kumbar susa.suna zaune falon karbar baqi aka kawo musu shi.ya rugo ya rungume babansa murna kamar ta kasheshi.mama tayi zuru tana kallonsu tana murmushi daka ganshi kaga al'ameen..ya dago shi suka zurawa juna ido dady yaushe kazo?yace banwani dade ba dama nace kar a gayamaka sai naxo kaganni suprise ko?yace amma kaje kaga waleeda?yace sau daya naje Allah sau daya naje ya tura baki a shagwabe gaskia ba haka akeyi ba .ba haka akeyi ba dady.ya fara dariya ya kama kunnuwansa biyu sorry.i'am very sorry abdul kayi?ya qara rungumeshi i miss u dad.yace nima haka yarona! ya dagoshi ya dubi mama ta zura musu ido tana murmushi.har wasu kwallan da batasan dalilinsuba suka taru.dadi wannan fa?ya dubeshi ya numfasa mominku ce saura sati uku adaura mana aure kana sonta?ya zura mata ido tamkar yadda take kallonsa ina sonta dady wlh tanada kyau kamar balarabiya! suka fashe da dariya mama ta jawoshi jikinta ta rungumeshi.tace nima inasonka kaima kayi kama da larabawan my beloved son.ya kwashe da dariya yace harda waleeda?tace sosaima.131Yace sister nane tana can suleja wajen kakarmu.zakije ki ganta?tace daganan can zamu wuce ya miqa mata yatsansa promise?ta jawo shi ta rungume al'ameen ya sauqe numfashi ya zura musu ido yana murmushi..ta dago ta dubeshi to nagode tunda kana sona kaga zamu zauna cikin farin ciki kenan koh?ya amsa da kai dady kuzo ku dauken ranar daurin auren.yace ai bakuyi hutu ba waleed kasan makaranta bazata bariba.kayi haquri inkunyi hutu kai tsaye zariya zan wuce dakai wajenta.yace waleeda zataje bikin?yace wai meyasa waleeda tazamo kishiyarka?to ita bazata jeba shikenan? gaba dayanku sai anyi hutu inkaiku.yadan saki fuska.mama tadauko wata farar leda ta miqa masa duk wannan naka ne.ya karba ya dudduba.kwalayen biskit da cukulet kala kala wanda yakeso.ya dubeta yana dariya momy na gode!tayi murmushi nima nagode.dr al'ameen yace bari mu wuce koh? muna sauri muje muga waleeda kar dare yayi sai mundawo.sukayi sallama da waleed kamar zaiyi kuka.hakanan suka tafi suka zuciyarsu cike da tausayinsa.shiyasa mama tayi shiru a mota tsawon lokaci sannan ta numfasa waleed kamar kayi kaki dokta!133Yayi dan murmushi Allah ko? tace har muryarku iri daya.ga shagwabar gado.ya kyalkyale da dariya yace.haka kema zaki haifa min ameer da ameera.ta watso masa harara,tace kai ka sansu.yace ashe kingane.kullum na rufe idona su nake gani.suna tumurmusani uhm...mafarkina yakusa zama gaskia.Allah kaban ameer da ameera ta tsatson sakeena wannan shine babban burina.ta zura masa ido harya tsargu yajuyo ya dubeta suka hada ido.yayi murmushi yadauke kai.itama tahauyi cikin ranta tana tayashi addu'ar Allah ya cika masa burinsa.suna tafe suna hira nanda nan suka iso suleja mama tana ganin yanda yadauki babban titi tace ina zamu? yace wajen waleeda mana!tace gaskia inajin kunya dokta.mu wuce kawai watarana na ganta.yace kunya?ina alqawarin dakika dauka wa waleed?tadan runtse ido ya salam.ta dubeshi ta ci gaba sai kuma muje kace musu ni wa?yace mominsu waleed ofcourse!cike da damuwa tace aikaji.sai ace banda kunya harna biyoka ganin yarka.ya karkace kai yace salo!to idan baki biyoni ba waza ki biyo?ta zura masa ido harya gaji yace tsaya kiji karewa cemusu zanyi kece nafara so rashinki yasa na auri ruqayya..tace kaga tun anan ansami matsala kana fadi zanyi baqin jini. Da dai....yanxu zakice bazakije kiga waleeda bako? ta bishi da kallo haka shima yasa mata ido jim! sukayi shiru kafin tace muje dokta amma ka taimakeni dan Allah karka basu labarin daya wuce.yayi dan murmushi yana tada mota fuskarki kamar na mara tsoro can cikin zuciyarki kamar farar kura.ga tsoro ga ban tsoro.tace muje a tsoron aini nasan menakeyi.yace nine bansani ba ko?tace wuuu! banfada ba Allah huci zuciyar mai gida. Da wutsiyar ido ya kalleta in banda abinki gidansu ruqayya ai gidan mune aminin dady fa.yadda yake abbanta nima abba nane tace nima abba nane.har kofar