Sashe 47
Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
barya cike da farin ciki da baya misaltuwa. Nan da nan ta fada bayi tayi wanka, ta kintsa jikinta ta kwanta. Kewar Danliti ta lullube ta, fadi take cikin ranta, ba dan dare yayi ba da naje yiwa sweety Na albishir. Da kyar barci ya sace ta saboda murna. Washe gari hidima taci gaba, mama na cikin dakin na kulle babu wanda ya san ta dawo, daga Ya Ali sai su Umma. Kuma anyi sa'a taji maganar Ya Ali batayi marmarin fitowa ba, sai shi ne ma ya kan saci jiki ya shiga wajenta, ya ganta yaji dan ji sanyi aransa. Allah sarki! Garin dadi na newa, iska na ta wahalar da mai kayan kara, bayan sallahr la'asar baki suka koma muhallin su aka bar amare da angwayensu. Shi kuwa Ubandawaki 'yan uwansa ya tara falon baki yace, naki ku ne a matsayin ku na kannena na in shaida muku cewar Mama ta dawo daren jiya, kuma har na yanke hukuncin ta gayawa Danlitin ya turo magabatansa, muyi maganar aure. Ban san yadda zaku karbi abin ba, ko da mahimmanci ko ya zama abin dariya a gareku, duk daya ne, ni dai na fita hakkinku. Suka dubi juna cikin sigar tsarguwa, sannan Alh.basir yace, ai shikenan yaya, amma banji dadin yadda kayi mana fassara ba, ya kamata kayi mana uxuri tunda mun ce maganar nan bada wata manufa muka fadeta ba. Amma ace mama ta dawo tun jiya, sai yanxun mukeji? Ba komai. Alh. Adam ya cage, tabbas naga Danliti a shagonsa, sai dain banyi tunani tare suka dawo ba, tunda banji labarin ba a cikin gida. Sai dai Yaya a gaskiyya muna so mu ganar da kai cewa ba farinciki mukeyi da abinda ya sami mama ba, mutuncin gidan nan, ai duk namune, me zai sa muyi murna da rugujewarsa? Abba yace duk naji, magana ta gaskiyya, Allah kadai yasanta, don shine masanin sirrin xukata. Abinda ya sa bau san Mama ta dawo ba, sai yanxun. Ali ne ya fara ganinta kuma ya xo ya sameni guiwa 2 ya roke ni da kyale mama kar in daga murya, saboda baki fa ke cikin gidan nan. Idan sun tafi ayi su wacce xa ayi. To maga ma ta kare, nacewa Danliti ya fito a daura musu auran, su karata. Allah dai ya gani ba da son raina bane. Fuska Ya mutse Alh. Basir ke cewa, Dan liti xata aura? Yace bamu da abinyi, haka Allah ya so, sai dai muyi mata fatan alkhairi. Saboda haka bana son abin yayi tsawo, yana turo sai aure. Ya turowa za'a sa rana kuma ba zata wuce sati 3-4 ba duk abinda Allah ya hore min shi xa'a kai mata. Ita kenan maganara, kowa na iya tafiya harkokinsa, mu saurari xuwan magabatan nasa shikenan, Allah ya nuna mana. Haka suka fadi baki dayansu. Abba ya amsa da amin, suka bar falon ba yabo ba fallasa, cikin xukatansu, ma'ana intayi ruwa rijiya in ba tai ba masai. Suna shuga sasan su, suka bajewa iyalensu babu bata tym suka fara xuba sharhi. Haj. Gake kuwa har da guda. Daga bisani suka baxama sassan Uban dawaki, don gain Mama tare da yiwa Umma murna dawowar Mama fida, amma a zahiri a cikin xukantasu yanayin Maman suke son gani. Suka kwarara sallama, umma ta amsa, sai mukaji daddadan labari! Ina maman? Inji Haj. Hajjo, tana dakinta, gaba daya sukace Allah shi kyauta na gaba. Yanxun da Danliti xa'ayi auran? Tace, nufi ne Allah, duk abinda ya rubuta bamu isa mu goge Ba. Haj. Hajjo tace gaskiyya ba haka muka so ba. Sai dai hkr kwai. Haj. Gaje ta tabe baki tace, ya xama dole, amma a hakikanin gaskiyya mama ta bamu kunya. Ajin ai ba daya bane in banda batan basira. Koda yake ance so mako ne. Allah ya sanya alkhairi. Sukayi dan shiru, kafin suka nufi dakin Mama, ina kike? Kina jin mu amma ba xaki fito ki gaishemu ba? Tana xaune gefen gado, ta fesa ado kyanta ya kara bayanna, banda haka da ibar da ta kara suka kalli juna sabe da haba, kafin Haj. Gaje ta soma xuba, lallai Mama, watau hankalinki a kwnace kika je, ki ka dawo! Wannan kiba haka? To Allah yasa ki sami irin wannan a gidansa. Haj. Hajjo ta amshe amin dai, kin dai riga kinsan halinsa, komai yayi miki sai ki hadiyewa cikinki, kar ki doshi kowa, tunda kin nace shi kike so! Ko kuwa gaje? Tace haka yake yaya, ai kowa ya sayi rariya yasan zata xubda ruwa. Mayafinta dake bisa filo ta figo ta mike tsaye ta xura takalmanta tayo waje tana yafa gyelenta, ta barsu anan sake da baki, suna kallon juna. Ko kinga dibar albarka? Inji Haj. Hajjo, Haj. Gaje tace, mamaki kikeyi Yaya? Karfa ki manta watanni 3 ta shafe a bariki, an kuwa ce xama da madaukin kanwa, shike kawo farin kai. Mu meye namu? Ta malam ai bata wuce amin. Can suka sameta dakin Umma tana neman izinin zuwa wajen Danliti, don ta shaida masa sakon abba, suna isowa, umm ana fadin bance kije ki xauna ba, mutunciki shine ya biyo ki nan kofar gidanku. Saboda haka daga yau kar na sake jin kin koma shagonsa. Tace, to Umma, insha Allah yanxun xan dawo. Ta sa kai ta fice, ba tare da Umma ta kara wani abu ba. Nan su Haj. Hajjo suka xauna suka cigaba da kwasar tsegumi, ita kuwa tana fitowa xauran farko, angwaye ta ci karo dasu, saeed Ya maka mata harara, ya wuce abinsa cikin gida. Ta dubi ya Ali, tace me nayi masa? Yace kin fi kowa sani. Taja dogon tsaki, aikin banxa, to shinme me? Don ya ki min magana? Yace, kin baci da Rashin K mama, me yasa? Da ba haka kike ba. Ta dan tabne baki tace, ni ina da wurin xauwa, ba na fito magana da Ya Saeed bane. Yace amma ba kije kinga amare ba. Xanje ai, so nake in sauke wannan nauyin ko ni,a na kama dahir. Yayi dan murmushi yana kllonta, mama kenan, to a dawo lfya, nasan sakon bai wuce na Danliti ba. Tayi 'yar dariya. Shi ysa nake sonka Yayana, bari dai in dawo amaryarka ka xan fara xuwa na in gani. Ta wuce tana cigaba da dariya, ganin yadda yayi tsaye duk jikinsa ya mutu. Ya bita da kallo, sannan ya kada kai, yace, ni ma ina mutuwar sonki Mama. Ina ma ace hankalinki xai dawo gareni? Ya sauke numfashi ya shige wajen amaryarsa. Bakinta har kunne take sallama kofar shagon, ayuba ta gani xaune ckin shagon ya amsa mata cike da fara'a amaryarmu kenan, ya gajiyar tfya? Tace tabi lfya, ina mutumin? Ya amsa yana ciki tun azahar yake barci saboda ragwanci. Ta fara dariya, lallai kuwa ragwanci, barin inshiga dole ya tashi ya bani goron albshiri. Ta wuce ciki, ayuba na fadin, ya dai kamata ya tashi ko salla ya samuyi. Kan tsaye bisa katifar ta fada, ta dada masa duka cinya, don Allah tashi rago! Ka wani baje kana gugar barci, ni ina can ina tunaninka. Ya bude ido firgigi yana kallon ta jim, sannan yayi dan gajeran tsaki. Yace kash! Wlh ba don ke bace, marin Mutum zanyi. Kin ji dadin barcin kuwa? Tayi far da ido, tace ko? To ka tashi, na tabbata dadin barcin bai kai albishir din baki na ba. Ya xuba mata ido yace fadi ina jinki. Idan kuma bai fi ba, kinsan Allah sai na sanya ki kuka, ai kin san gamuwar mu babu tausayi. Tayi 'yar dariya, tace, haba duk wannan kukan wasa nakeyi, kama daina hura hanci. Yayi murmushi, haka kikace? To shiknen, fadi ina jinki. Ta gyara xama albishirnka? Yamasa goro. Xaka bani Ah! Me xai hana? Ke dai gaya min inji. Abba yace in fada maka ka turo, ranar auren mu za a sanya. Ya xuba mata ido, ya kasa ko motsi, kayi shiru? Ya sa hannu 2 ya mutsutsuke idanuwansa yace, dan Allah karki xalayeni! Ta ware ido, kana nufin baka yarda ba? Gaskiyya ban yarda ba, yaushe Abba xai yarda ya bani ke, bayan ya san bani da kowa a garin nan? Sannan suna min kallon dan... Tayi wuf ta rufe bakinsa, sau nawa xan gaya maka ka daina dorawa kanka maraici? Ina sonka Danliti..... su abba kuma sun amince ka turo asa mana rana da gaske na ke gaya maka maganar nan ba wasa ba da sauri ya figo ta jikinsa yayi wani irin ihu wai shi murna ayuba ya kwaso a guje ya fado dakin ya same si kankame da juna dan haka. Bai tsaya tambayar komai ba ya juya ya fita yana kada kai cikin ransa yana fadin "Danliti akwai dan iska"ya jima bai kyale mama taci gaba dayi masa bayani ba yanzu yaushe. Zaka turo? Ya yunkura ya tashi zaune yace bashine matsalar ba wadanda zan turar sune matsalar ta dan bata fuska tace ai ba za ka rasaba "Danliti ko yan dattijan daku ke gaisawa sun isa su wakilce ka ko kuwa? Ya zura mata ido duk sun juye, yace haka ne sai ki baru in gan su mudaidaita tukunna sannan in gaya miki ranar daza su zo ko" tace shi ke nan bari in kwashe sauran kayana in koma gida ya kara matsarta haba tun yanzu ?" Umma ta ce kar na dade kuma tunda sun amince da kai ai zaka rinka zuwa ne kan ka tsaye,"ya kankameta ya na fadin haka ne amma ban so ki tafi yanzu sonki kawai ke azabtar da ni ina kewarki da yawa jiya da kyar nayi barci kinji yadda ki ke tashin kamshi?gaya min dame dame ki ka shafa in karo miki irinsu?"Bata iya bashi amsa ba don tun tafiyar su yake koya mata irin wannan renon ya gama da rayuwar ta gaba daya kai ALLAH ka raba mu da sharrin masu sharri,magariba ta wuce wadan da sukaje masallaci ma sun koma gida yayin da mama ta fito daga shagon Danliti jaye da katuwar jakar kayanta. -yar tafiya kadan ya taka mata ya dawo abinsa bata sami dan dakon da zai daukar mata kayanba ba don haka da kanta tayi ta ja har gida abba da umma na zaune a falo dauke da bakin ciki maras misaltuwa mama ta