← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 79

Sashe 3

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

dariya ta zauna sannu Inna ina kwana? Ta amsa lfy lau an dawo lfy? Tace wllh lfy lau inna, kinga dinkinta dama za'aje kai mata Mama ta fiddo su a leda ta daddaga kai amma atamfofin masu kyau. Suka dan taba hira suka wuce dakin Baraka kowacce ta cire after dress. Mama ta fada katifa tace tun dazu ya kamata in shigo gidan nan bakon unguwarku ya tare ni. Bako? A ina?tace oho! Wai nan gidan Alh lado suke cewa ko? Eh nan ne gidan kakarsa Al- Ameen yace min sunansa, bakinta har kunne ta jawo hannunta suka tafa ban mu kashe yar'uwa bakar fata kice kinyi gamao da katar. Likita bokan turai yau shiya kawo Maman tasa kenan. Ta ware ido kina nufin Dr ne? Kwarai kuwa ko bai kammala ba kiris ya rage, don tuntuni naji ana fadin sabis yake, ta kama baki har kin kara min son shi ina ma ace wann abu ya tabbata kusa bikin likitoci, au kema likitance? Tace zauna nan in gaya miki jiy-jiya Abba ya gaya mina bnd zan karanta kenan, kuma gsky Al- ameen yayi min matsalar kawai Abba. A'a ina cewa ya soke maganar su Ya Ali? Eh mana to ai baki sani ba soke maganar ita ta janyo min tsiyar. Kina zaton su kawu baza suji haushi ba? Ance karatu zanyi kuma wani yazo an bashi? Ai sai Umma tayi bakin jini acikin gidan. Bansan yanda zanyi ba shi kanshi yaban tausayi tahowata kawai nayi na barshi kinsanni da karfin hali Baraka ta bata rai kai yakamata a nemi mafita Al-Ameen yayi kawata zan soki dashi don na hango kun dace kwarai. Ta sata ta zabga tagumi ta zuba mata ido, ina tsoron Abba Baraka bazan iya dumfararsa da wann maganr ba bayan jiyan nan yaja min kunne ya gaya min burinsa akaina ina zansa raina nima inason Al-Ameen! Ta dafe goshi ga koshi ga kwanan yunwa, Baraka tayi iya tunaninta ta rasa mafita, sbd tsoron hanyar da za'abi a dumfari Uban dwk don haka ta numfasa tace to ai shikenan sai ku dauki hakuri idan kuma yana iya dakatawa ya jiraki ko kuwa? Tace kyaleni haushi ya isheni dauko wani topic din kona manta da wann. Tayi yar dariya to ya skul? Mu koma wancan fannin dame-dame suka faru? Ta gyara zama suka tsinke da hirar makaranta daga abinci sai sallah har zuwa bayan la'asar lokacin da Mama ke niyyar tafiya da zarar ta idar da sallah.Tana sallamewa yaro ya shigo wai ana kiran Mama ta leko tace jeka kace ta tafi Inna ta leko tace uwaki baki zuwa ko wanene? Kai kace gata nan zuwa. Yaro ya fice inna taci gaba da fada ba kyau wulakanci ko baki son sa ki saurare shi ki bashi hakuri a zauan lfy, ta shige daki Inna kenan bazaki gane ba. Ta maida after dress dinta tasa mayafi tace Baraka zoki rakani, donAllah ki tafi ke kadai kinsan sirrin da zakuyi? Ta ja tsaki ta fito yana tsaye a kofar gidan haba gimbiya, kuma saiki tafi kibarni da tension? Ina kikeso nasa raina yau wllh ko abinci na kasa ci sbd tunanin matsalar da kika ambato. Tayi masa zuru tausayinsa ne zalla ke bin jinin jinkinta tace kasan Allah nima tunani na ya kara na rasa me zancewa Abba ganin yan'uwana ma na jini ya dakatar dasu balle wani kuma watakila kana bukatar auren ne da wuri kaga Abba bazai amince ba. Ya goge zufar goshinsa da hankici, don dai in jure ki karee sakandire zan iya jira mana. Idan ma kinaso cigaba ne bayan munyi aure ni zan dauki nauyin ki karanta duk fannin da kikeso donAllah ki taimakeni kiyiwa Abba wann bayanin. Ta dafe goshi! Wane zan masa ya gane? Ya fada a ransa yace na dameki ko? Yes nima nasan na fiye naci ga duk abnd nake so. Yace mata tunda baki da abinyi ni ina dashi abnd nake bukata daga gareki kawai ki tabbatar min tsakaninki da Allah har cikin mind dinki kina sona? Ki fada kanki tsaya kawai! Mamana tana gab da fitowa zamu tafi.Tace Al- Ameen na amince kar kaji wani shakku a ranka amma...... Ya dan daga mata hannu don't sai it pls! Kin faranta min rai Sakeena na tabbata zan samu inci abinci ya wuce min. Sauran magana ki kyale min, nace yanzu me zaki bani na rike na alkawari? Al-Ameen fa na bata mmk na yadda gaba daya ya sallama kansa gareta ko shiyasa itama ya mamaye mata ko ina? Tayi dan murmushi me zan baka kuwa? Ya nuna yatsanta wann ring din yayi min kyau shi zaki bani, ai bazai yi maka ba, inji wa? Miko shinan ki gani. Ba musu ta zaro ta mika masa ya turawa karamin yatsarsa zobe yayi zamansa daram kamar daman can na sane. BAKIN CIKI 1***2 Ya dubeta yana murmushi U see? Mu biyu akayiwa zoben nan kika kama ke kadai kika rike, tayi yar dariya "haka naji" "nima kuwa hakan naji" amma matsalar ni bani da jar azurfa dana baki wann kuma saidai kiyi warwaro dashi ba dai zobe ba. Ta zubawa zoben ido yana ta daukar ido ko in baki zoben haka? "Kawo" ai yayi miki yawa gimbiya ayi min hakuri a biyoni bashi in Shaa Allahu zan biya. To Allah ya baka iko, ya kara zubo mata ido yace to ameen gimbiyata. Ya cigaba da kallonta sannan ya sauke numfashi wai yanzu zamu tafi gashi ban gaji da ganinki ba. Yadda kikasan in saki a aljihu in tafi dake. Tace ka saceni kenan? Yayi yar dariya me karawa fuskarsa kyau da kwarjini kamar yanda kika sace ni ba. Ji sukayi ana tambaya ina Al-Ameen din ya nufa ne? Yace gani Mama anan. Ta fada zaure da saurinta ta fara dariya zoki ganta Mama donAlla! Ta kama baki Oh ni Hafsatu Goggo fito kiga ikon Allah! Itama yar tsohuwa ta fito ina kishiyar tawa duk ta susuta min miji! Mama ta manne da bango ta rufe fuska ruf da mayafi. Ta sulale kasa tun kafin su karaso, Goggo zoki sha kallon yar bebi ba irinki ba bude fuskar su ganki. Maman da kanta ta bude fuskar yayin da take gaishesu. Ta amsa cike da fara'a ah! Mashaa Allahu Al- Ameen ka iya zabe, Allah yasa albarka Goggo tace ameen dai. Ai ka kwantar da hankalinka nan gida ne babu abnd zai gagara In Shaa Allahu! Yace Allah yasa Goggo suka baro zauren Hajiar na fadin kai fa nake jira karka shanya ni.. Gani nan Mama, Mama tace Allah ya kiyaye ta amsa da ameen. Ya gyara tsayuwa yace kingani? Bani kadai nake sonki ba Sakeena sbd haka ki saurare ni, tace ina nan ina sararonka Allah ya tabbatar mana da alahiri, ameen gimbiyata to bari mu lallaba tace Allah ya tsare amma zaka yi min alkawari? Me zai hana? Fade shi indai ba zakice in daina zuwa gunki bane , tayi yar dariya bashi bane kayi min alkawarin zaka ci abinci idan son samu nema mama ta dan jiraka kaci ko yaya ne, kai Dr ne kasan matsalar rashin cin abinci ya ware sosai yace waya gaya miki ni Dr ne? Tayi nuni cikin gida yar'uwata dake nan gidan. Yayi jim! Murmushi kawai yake fiddawa kafin yace its true 4mnths back aka damka min letter of appointment a ABUTH Zaria hope kinason Dr? ta dube shi da gefen ido sai ya tsira mata ido domin kallon yayi masa sosai ko shi kadai ya isa amsar tambayarsa, in ba don son jin baki ba bata ga ma dalilin wann tambayar ba don haka ta juya zata shiga gida. Sakeena! Ya kirata a sanyaye ta juyo dauke da murmushi tace a sauka lfy Allah ya tsare ta karasa cikin gida don ta lura idan ba hakan tayi ba bazai tafi ba kuma ana jirransa. Gaba daya kasala ta sauko masa ya sauke numfashi ya jima tsaye bakin zauren sannan ya fito wajen mota inda Mamansa ke jiransa. A hakikanin gaskiya Al-ameen ya kamu da wata sabuwar cuta wacce shi kansa a matsaynsa na likita bai taba cin karo da maganinta ba. Duk iya karatnsa da yayi kuwa. Sosai yake ji a ckn ransa idan bai auri mama ba babu makawa zai fusknci matsala. Shi yasa tunda ya damki hnya baya iya magana da kowa illa addu'ar Allah yasa sakeena matarsa ce! Hakazalika al'amarn yake wajn mama, tas! Al'ameen ke neman rusa shirinta na son zurfn karatu, kamar ynda tayi wa Abbanta alkawari. A halin ynzu kam shirun da tayi bisa shimfida tun shigowarta gidan, tunanin auren al'ameen take yi, kuma da son samu ne kar aja lokaci mai tsawo. Anya abbanta zai yarda kuwa? Baraka ma taso ta kauda mata wannan tunanin, amma ta kasa. Ta yunkura ta tashi zaune tace, "bari in wuce baraka". Kallnta kawai take yi, ta mika hannu ta jawo jakarta ta rataya, tayi waje. Yaynda baraka ta dauko mayafi ta biyo ta. A dakin inna ta sameta suna sallama, hannunta daya rike da ledar kayan dinkin umman ta, "ki gaida min ita da kyau, sai na zo" tace, "to zata ji insha Allahu". Ta juya suka fito tare da baraka. Sawun tayoyn motarsa ta tsaya tana kallo tsawn lokaci, kafn ta dubi baraka, "al'ameen ya wuce, ban jin zan sake ganinsa......." "wannan mugun zato ne, me yasa kike wa kanki mugun fata?" ta kada kai, "ba mugun fata bane, sauya ra'ayin abba shine fargaba na, tabbas babu abnda zai hana shi dakatar da al'ameen, tunda ya iya dakatar da 'ya'yan 'yan uwansa na jini daya". Tace, "ni kuwa a tawa wautar gani nake al'ameen zai iya jiranki, tnda yana sonki". "lallai kam wauta, baki ganin al'ameen ya girma sosai, na tabbata a halin yanzu iyaynsa basu da wani buri da ya wuce su ga yayi aure. Yaushe zasu lamunci jirana shekaru barkatai masu zuwa? Banzan tunani kike yi baraka, kawai ki yarda zan iya rasa al'amee".! Ta fizgo hannunta suka wuce tana fadin, "ni banji a jikina ba, kuma ai Allah na nan, ba sai mu kai kukanmu gunsa ba" "haka ne, dole in gayawa Allah, don gaskiya ban taba jin wani sauyi a zuciyata ba, sai a kansa. Zaki tayani kawata?" tayi dan murmushi tare da kamo habar ta,
Chapter 3 · 0% Book details