← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 79

Sashe 7

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gabanta ya yanke ya fadi ta zurawa yaron ido ta rasa me zatace? Umman ce ta bashi amsa to kace tana zuwa. Ya juya ya fita, kin tsaya ki kam kije ki shiryo mana. Ta shige dakinta sanyi na kwarar zuciyarta. Ta tsaya gaban mudubi ta gyara fuskarta ta suro gyalenta ta yafa tayo waje. Umma na tsakar gida ta mika mata makulli tace ki kaishi falo karku tsaya a waje. Fuska sake ta amsa ranta ya kara sol. Tayi kofar gida cikin sauri amma cikin sanda ta leko yana tsaye jingine da motarsa ya zurawa zauren ido shiyasa tayi arba da idanuwansa masu haske da girma. Sbd haka kunya ta lullubeta ta koma zauren ta lafe tana maida numfashi kawai muryarsa taji bisa kanta yana fadin sallama gareki ma'abociyar kyau! Jim tayi shiru kamar ruwa ya cita hannunta daya rufe da fuskarta haka shima ya tsaya ya zura mata ido dauke da murmushi mai isar da sako barkatai. A nutse ta bude fuskarta ta dubeshi "sannu da zuwa" taushin muryarta yasa jinin jikinsa ya tsinke yaji son Mama ya kara malale kowane lungu cikin zuciyarsa tamkar ya hadiyeta yakeji kai bai tabajin azababben so irin wanda ya kama hsi ba, ya numfasa yace gimbiya ta kenan. An fito lfy? Tace kalau ya hanya? Yasu Baba sukaje gida? Ya amsa duka lfy lau, tace mungide Allah. Yanzu ka ban minti daya zan bude maka inda zaka zauna, yace ni kadai? Gsky ban yarda ba! Tayi dan murmushi to inda zamu zauna. Yauwa yanzu naji batu gara da kika gyara. Ta wuce tana 'yar drya. Shi kuma yayi wawan ajiyar zcya, ya dawo jkn motrsa ya harde. Jimawa kadan ta budo babban kofar get da ke can wani bangare na katangar gidan, ta fito tace dashi, "bismillah!". Bai yarda ta tsere masa ba, jerawa suka yi suna tafe yana fadin, "ga Amarya ga Ango!". Ta ballo masa harara, fuskarta kunshe da kyakkawan murmushi, har suka shige falon. Ta nuna masa kujera ya zauna, ita ma ta koma gefen damarsa ta zauna, suka sake gaisawa. Yace, "to Alhamdu lillah, godiya ta tabbata ga Allah wnda ya nufi al'ameen ya zama angon sakeena. Ko kinsan cewa jiya banyi barcin kirki ba?". Ta kada kai, "me yasa?" "ban taba zaton abba zai saurari kukana ba, shi yasa na kasance tamkar maraya, ni kadai cikn daki, bana aikn komai sai na addu'a, idanuwan nan sun fidda hawaye gaban Ubangiji don neman biyan bukata. Beliete me ma jinina ya hau kfn dady ya dawo......." ta katse shi, "amma da ya dawo fa?" yace, "albishir din da ya dawo min dashi ya hana min barci sbd tsabar murna da farin ciki, cnt explain sakeena" tace, "ka mamayi abba, kuma ni kaina nayi mamakin amincewarsa, koda yake abba mai saukn kai ne, kuma bai cika jayayya ckn al'amarn rayuwa ba" "na yarda da ke. allah ya sakawa abba da alkhairi, domin ya ceci rayuwata. Ko har da taki?" Ta dube shi suka hada ido, ta dan kauda kai. Tayi 'yar drya. Yace, "ban damu ba, tnda ni nayi nasara". Tace, "ni kuma bazan yarda da kai ba, sai naga alkawari na". Ya zuro mata ido, "a tunaninki zan manta ne? No sakeena, kece komai nawa, bazan taba mantawa da wani abu wnda ke alaka da ke ba, balle kuma ace alkawari ne......," Ya tura hannu aljihu ya dauko wani dan karamin mazubi ya bude, ya nuno mata wani gangariyan zoben zinari yace, "ina jin wannan shine alkawarin ko?" Baknta yaki rufuwa, ya matso gabnta ya tsugunna ya miko mata, tasa hannu ta dauka ta zurawa yatsanta. Wayyo! Al'ameen zuru kawai yayi yana kalln zara-zaran yatsnta, zoben nan ya zauna kamar da shi aka halicce ta. "tsarki ya tabbata ga Ubangijn da ya halicce ki sakeena". Ya dago ido ya dubeta, "kiyi min alkawari har abada ba zaki daina sona ba". Tace, "insha Allahu zaka sameni mai cika alkawari komai wuya, komai tsanani zan jure akan alkawarinka. Har abada kai kadai ne, ba wani sai kai" Idanuwnsa suka kawo kwalla, murya sanyaye yace, "na gode sakeena" tace, "kar ka damu". Ya mika mata gidan zoben ta karba. Ya koma mazauninsa ya zauna, abba ya gaya wa dadyna kema irin karatu zaki yi, kinga ta kwana gidan sauki, wai matar likita ta haifi panadol" Ta fara drya, "oh, drya na baki ko? To shikenan, ai ba ke matar likitan zaki haifi panadol din ba........" tace, "au son kai ne abin?" "eh mana. Nawa bouncing baby ne, baby boy ko girl? Zabar min". Ta mako masa harara, ya hau drya. "well, daga nan idan na tashi zariya zan wuce, sai kuma nxt week zan dawo in sake ganin gimbiyata" tace, "Allah ya kaimu lfya, nima anjiman zan wuce minna wajn yayana zanyi hutu" Ya bude ido, "owk, kuma shine tnda nazo baki gaya min ba, ai sai in juya in kaiki, daga can in wuce". Ta kada kai, "bana son ka wahala, ka wuce wurin aiki abinka. Babu komai". Yace, "uhm...... To na gode, amma ina fatan akwai phon number a can, kin ga sai mu rika gaisawa ko?" tace, "eh akwai land-line zan baka" Yayi ajiyar zuciya, sannan yace, "yanzu ki bani labari, ku nawa ne a daknku?" tace, "mu hudu, yaya abdul-kadeer soja, shine babba, sai yaya abdul-kareem yana CBN Minna, shine zani hutu gunsa, then yaya Abdul-rahman yana kadna, lst year ya fara aiki da ma'aikatar kimiyya da fasaha ta jiha, shi kadai ne bai yi aure ba......" "sai kuma ke ko?". Tayi 'yar dryar nan da yake so. Yace, "kun burgeni, Abdul 3, ni kuwa tilo ne ckn gdnmu, bani da yaya balle kani. Kadaicn yayi min yawa sakeena". Tace, "kamar ynda gata yayi maka yawa ba" "haka kike gani? No ba zaki gane ba, naso ace akwai wasu, musamman kanne, na rika yi musu 'yan mazurai ina cewa, kai ku bari mana! You knw, smthn like that dai. Amma ka zauna shiru babu mai maka fada, babu wnda zaka yi wa? Babu dadi abin". Ckn tausayi tace, "ai shirin na Allah ne" yace, "yes haka ne, na yarda. Amma very soon zan samu many babies, su zagayeni, dady kalla! Dady bani wannan! Dady sa min riga! Kin gane? Ina son hayaniyar yara sosai" Tana drya tace, "kana da aiki" "come on, muna da aiki dai. Ai mu biyu ne muna tsakhya, sun zagaye mu, na 6 can 6. Wuu! Confusion! Wa zai gane min ke?" Hannunta tallafe da kunci, ta zuba masa ido tana kallnsa yana ta zuba bayani, idanuwanta suna nuna mata yaran zagaye da shi. Shi yasa yana sa aya ta fashe da drya. Yace, "drya ma na baki ko? Yarnya gudu zanyi in kyaleki dasu" Ta dan tabe baki, ta tashi tsam! Zata bar falon, yace "ina za ki? Har kinji tsoro ne?" tace, "tsorn me? Ruwa zan kawo maka, kaji dadin santin". Sosai yayi drya, har ta bar falon. Ya koma a hnkali ya jingina bayansa da kujera, ya rufe ido tamkar mai barci. Wani kasaitaccen taro yake hangowa, wnda cikarsa baya misaltuwa. Jimawa kadan ya keto taron rike da hannun sakeenarsa, da ka dube su kaga amarya da ango. Jama'a na musu tafi, su kuwa baki yaki rufuwa. Bisa wasu kasaitattun kujeru suka zauna, ta tsiyaya lemu a kofi ta mika masa a baki, ya dauka zai fara sha...... "Assalamu alaikum!". Ya bude ido a hnkali, tana tsugunne gabansa rike da kofin ruwa. "barci kayi? Lallai na dade da yawa, ayi min afuwa". Ya saki wani wawan numfashi, ya girgiza kai, "dogon tunani ne ya dauke ni. A duniya bani da wani burin da ya wuce aurenki sakeena.....". Yayi dan shiru jim! Yana kallnta, ya kada kai, sannan ya karbi kofin hannunta, "na gode". Ya shanye ruwan, ta zuba masa lemu, ta koma ta zauna, ilahirin jiknta ya mutu. Wane irn so al'ameen ke mata? Ta tambayi kanta. Tana ganin ita ma irnsa take yi masa, domin itama burinta ta zama mata a gareshi. Ko don ita kunya na maida ita kurma, shi yasa yake ganin shi kadai ke da buri a kanta? Zurun da tayi masa a rashn sani, shi ya jawo hnkalnsa ya daina kurbar lemun. Ya matso gabnta yasa mata kofn a baknta, ta sha kadan ta dube shi, "ba kai kadai ke da buri ba Dr., sanin kanka ne mu duka muna da bukatar kasncewa tare. Idan baka sani, ynzu na gaya maka ka sani, don ka daina damuwa". Ya numfasa yace, "Allah ya tabbatar mana da wannan buri" tace, "amin". A natse suka zauna suka ci gaba da faranta wa junansu rai da dad'ad'an kalamai. A nan yayi sallar azahar, ya ci abnci, sannan yayi shirn wucewa zrya. Ita ta jagorance shi ya shiga ya gaida umma, don ya matsa kwarai yana son kai mata gaisuwa. Ta kuwa ji dadi, ta kuma yaba da tarbiyyar sa, yanaynsa da alkunyar sa.! Suna tsaye jikin motarsa sallama taki karewa Ya Ali ya danno kofar gidan da jakarsa akafada, bakinta har kunne ta tarbeshi Ya Ali! Sannu da zuwa, ya kalleta ya kalli wanda take tsaye dashi kafin ya amsa. Ya mikawa bako hannu tare da sallama (Allah Sarki ubana akwai jarumta!). Ita kuma tana fadin Ya Aliyu kenan cosin dina ne, Allah sarki inji Al-Ameen an dawo lfy? Yace lfy lau! To madalla. Aliyu yace dauke da matsanancin kishi da mamaki a ransa. Al-Ameen kuwa fadi yake kuna satar kama da juna da an ganshi an ga dan'uwanki, tace ko? To ai da Baban shi da Abba duk dakinsu daya. A Birnin gwari yake aiki. That's gud' ina ganin ya kamata in lallaba in barki ku wuce ko? Kar dare yayi. Tace hakane, kai din ma bana son dare yayi maka. To shikenan karfe tara ISA zakiji wayata. Allah ya yarda a sauka lfy. Ameen. Ya shiga mota ta rufe masa tana kara fadin kayi tuki a hankali, yace thank U. Ta juya zata wuce yayai kiranta Skaeena! Ta juyo tare da murmushi yace "I love you!" Ta kara fadada murmushinta ta rausaya kai ta juya zata wuce Sakeena! Ta sake juyowa. I love u! Tayi jim kafin tace I love U too! Ta ruga cikin gida ya rakata da kallo bakinsa kamar gonar auduga kasala ta rufe
Chapter 7 · 0% Book details