Sashe 51
Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Mama, don tashinta. Tana kife ruf da ciki, Umma ta dada mata duka ta tashi a firgice. Umma ta xura mata ido, tace, in kin ga dama ki tashi kiyi sallah! Tayi waje ta bata wuri. Da kyar ta mike zaune, kanta ya sara mata, ta dafe shi hannu biyu, gaba daya miyan bakinta ya kafe. Makoshin ta ya bushe. Tana daga xaune, amma jiri ne ke dibar ta.... Idanuwanta na ganin duhu, don haka ta runtse su tamau! Tana maida numfashi, ta wuce minti sama da goma ahaka, sannan ta iya tashi a daddafe ta shiga bayin. Tunaninta kawai tayi wanka ko tafi jin dadin jikinta. Nan da nan ta kwashi ruwa a bokiti ta fara wanka. Kamshin sabulun( Joy) Ya gauraye bayin, ba xato ba tsammani taji xuciyarta ta tsani kamshin, kan ka ce kwabo ta goce da amai. Ta kwarara mai isarta, wai don ma babu komi cikin nata. Tana gamawa ta dauki bojitin ta juye ruwan ajikinta, tun daga kai. Ta jefar da shi ta yayo xani ta daura, ta banko kofa ta dawo daki, ta bar bayin face face da amai. Ruf da ciki ta sake fadwa gado fadi take, wash! Wayyo Allah xan mutu! Tun daga tym din al'amura suka kwance mata, ta rasa kanta ta rasa meke damunta tana rashin son abinci da yawan tashin xuciya, ga wani cikin safe da jiri wani tym din jikinta yayi xafi, don kansa kuma ya sauka ba tare da tasha magani ba. Duk ba wannan bace babbar Matsalarta ba, Ina Danliti ya shiga kwana 2 babu labarinsa? Me kuma yake nufi da tafiyarsa? Duk da cewar tasan dole ya dawo, idanuwanta da xuciyarta sun gaza jure rashin sa na 'yan kwanakin 2. Shi yasa koda yaushe tana kunshe a dakin matsalolinta masu yawa na neman xautar da ita. Umma da kanta bata gane kanta ba, musamman rashin xuwanta neman abinda xat ci. Amma yawan xaman daki umma ta jingina da rashin ganin Danliti da ta rataywa xuciyarta, balle ayi maganar jingina shi da wanccan Matsalar. Ta kan kada kai, tace, kaico! Abincin wani, gubar wani! Allah ka raba mu da muguwar kaddara... A yau asabar ake sa ran xuwan yayyin Mamma, ga shi babu magana mai kwari ko kuma muce uban gayyar baya gari, shi da kansa abba xaune yake shiru dakin ta same shi, ta xauna gefensa tace, kana xaune baka shiga wanka ba? Yayi gajeran tsaki, yace maganar nan ke damuna, da yarinyar nan xata gane da ta amince cewar Dalinti ba xai turo kowa ba. Banda aikin rashin gaskiyya, menene na kama hanya kabar gari, kai da aka ba damar ka aiko a baka mallakar abinda kake so. Wane bata tym xakayi saboda Allah? Ta numfasa, tace yaushe xata fusknaci hakan yadda ta makance gaba daya, bata ganin kowa sai shi? Ai na gaya maka ko abinci bata ci, duk ta fige saboda bala'i, ni yaran nan ma dasu wahala suke nake tausayawa ba su gama warware gajiyar biki ba, ga aikinsa mai dan banxan wahala, da da halin da xa'a ce da su dakata, wlh da ance suyi xamansu. Ya gyara xama kyale su suzo ko hira mukayi, ai maji dadi, ko ba haka ba? Haka ne, Allah ya kawo su lfya. Amin ke ki kira min Mama ta zo yaushe, dan liti xai dawo? Ta mike ta nufi daki Mama ta tura kofa kakarin amai ya fara dibar hankalinta, cikin fargaba ta nufi kofar bayin ta murda ta bude, Mama! Tana durkushe kame da ciki, kamar xata mutu. Kan Umma ya kara daurewa, domin bata taba ganin Mama na kwarara amai haka ba. Ko rashin lfya takeyi, bata amai, sai dai xafin xaxxabi. Don haka ta nufe da sauri ta dafe ta, me xan gani haka Mama, baki da lfya ne ko yaya ne? Bata iya amsa mata ba, tana tsaye kame da haba, tagama kakarinta, ta kuskure baki hade da fuska, tayo waje abinta, ba tare da kula Umma ba. Bisa gado ta fada ta datse ciki tana numfarfashi. Umma ta biyo a fusace tasa hannu ta birkito ta, ba kyajin ina magana ne? Nace lfya kike sheka amai? Ido jajur! Cike da kwalla tace, cikina ke min ciwo, tun yaushe? Yau 3days. Ta jawo ta waje cikin haske sosai, ta kama hannayenta ta dudduba, sannan ta gwale idanuwanta, ta duba cikinsu, a tsorace ta tambayeta ke, kina yi al'ada kuwa? Tayi shiru tana xaxxare ido, baki na rawa tace, nima ban sani ba Umma. Ba ki sani ba? Ke xaki gaya min ko sai na farfasa bakinki? Ta goce da kuka, don ita ma ta kideme, ta mance rabonta da a'alada. Umma ta xura mata ido, jinin ta na kara hauhawa, da sauri ta wuce ta bar mama tsaye. Dakin abba ta koma ta xauna, ta rike kai tana maida salati. Me akayi? Tace alh. Magana takare ka dauki mama ka kaita asibiti ayi mata gwajegwaje! Gabansa ya fadi gwajegwaje? Name kuma? Na komai Alh. Ina shiga na sameta tana sheka amai a bayi, wai cikinta ke ciwo, amma alamu a bayyane sun nuna Mama juna 2 gareta........ Tsaye ya mike tare da fadin me? Hawaye suka kara tsunke mata, ya koma a hankali ya xauna bakin sa na karanto salatin Manxon rahma. Gaba dayansu tsit! Sukayi tsawon lokaci sai Umma ke shatatar hawaye, baiyi aune ba kawai ya ga ta dungura ta fadi a sume. Ya xabura ya tarairayota, yana kiran Halima! Halima!! Don girman Allah karki kara min tsahin hankali akan wanda nake ciki, ya jawo goran ruwa ya xuba a hannunsa, ya yarfa mata, ya cigaba da shafa mata ruwan bisa fuska, ahankali har ta dawo hayyacinta. Ta bude ido, jim tana kallonsa, sannan ta sake fashewa da kuka, nan take tausayinta, yasa kwallan Ubandawaki suka fara sauka bisa kuncinsa. BAKIN CIKI kamar ya aika shi barxahu. Kiyi hkr, ki kwantar da hankalin ki Halima, wannan jarabawa daga Allah Ubangiji take, babu wanda ya isa ya kankare mana ita, bana son tsanin damuwar nan da kikeyi, tana jefa ni mummunan matsayi, ko dogara da Allah Halima shine xai magance mana komai. Ta goge hawayenta tayi, iyayinta don ta tashi xaune amma ta kasa. Yace kar ki damu da sai kin tashi yanxu kiyi kwanciyarki ki huta, bari in kwaso magungunan ki in duba wanda ya dace kisha. Ya mike da sauri wani duhu ya rufe masa idanuwansa, bai ganin komai face wasu miliyoyin taurari kanana, tilas ya dawo ya xauna ya fadin Hasbinallahu wa nimal wakil. Yayi ta maxa ya sake mikewa. Umma tace ka xauna Alhaji kar kaje ka fadi ka nakasa. Bai tanka ba, ya fice. Jimawa kadan ya dawo da kwanndon magungunan ta ya xauan yana bincikawa, jikinsa na rawa saboda bacin rai. Sallama sukayi daga falo kuma babu tantama muryar Ya abdurahman ce, abba Ya amsa, ya kara da fadin gamu nan, ku karaso ciki. Ganinsu jugun2, Yaya take ya rasa kuzarinsa. Yaya dai Abba? Jikin nata ne ya tashi? Yace shine abdulrahman, nan da nan ya xube gabanta, da dauko kanta ya dora bisa cinyoyinsa, sannu Umma! Sannu! Ta matse kwalla, ta dube shi, kaxo lfya? Ina safiyya? Ya amsa lfya lau take, tace in gaisheki. Ina amsawa, me yasa baka xo da ita ba? Ya goge mata kwalla, tayi nauyi ne Umma bata jin dadi, idan tayi doguwar tafiya, koda muka koma, bayan daura aure sai da tayi xaxxabi. Ta dan kada kai, tace Allah sarki, Allah ya raba su lfya. Amin. Ya amsa sannan ya dubi Abba suka gaisa. Kafin su kama wata maganar, muryar Manyan yayin ta gauraye cikin falonm. Abba ya gaya musu suna ciki, kowa ya shigo da kuzarinsa, ya ga Umma a kwance sai yayi turus! Bayan sun gaisa tasha magani. Abba ya kwashe abinda ke faruwa kaf, ya gaya musu, kowa yayi shiru, kawunansu sunkuye tsawon tym kafin Ya soja, yace, yanxun Ina Maman take? Oho inji Abba, gaba daya sukace oho? Ta bar gidan nne, Umma tace tsakar gida na barya tsaye, ban sani ba ko ta koma daki ko ta fice don ba sani xamuyi ba. Duk tym din ta so fitarta, ficewa ta takeyi.