Sashe 27
Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
kina hira da wani...." 'Wani? Ba ka ma san danliti ba?"Shut up don Allah!waye danliti kike gaya min magana ba dadin ji?Hauka kika yi?Ina mutunci ga'ya mace tana hira da maza a kofar shago gaban jama'a? Ban san ki da wannan ba,yaushe kika canza mama? Ta ballo masa harara ta ja dogon tsaki ta kwahsi sauri ta wuce shi,shi ma ya biyo ta yana fadin,ban gane nufin ki ba?"Ta juyo ta dube shi tace,wai menene yaya ali?"Shi kike so?" 'Ai kaji,menene na sake tambaya? ya kara cika da mamaki,'Ban fa gane shi ki ke so ba mama.Ina Al-Ameen din?" Ido jajur! Ta dube shi,"kai ka san wannan sunan,don girman Allah ka kyale ni da tambayoyin nan." "Ba zan kyale ki ba Mama,hasali ma sai na gaya wasu Abba.Wannan ai zubar da mutunci ne da cin amana!Me ya tsone miki ido a wajen Dan-Liti?Ke ma kin shiga sahun 'yan matan da yake ruda da kyan sa ne?Kai na ya daure Mama.Allah yasa abinda na ke gani da ji ba gaskiya bane." Da gaske ne yaya Ali! Kuma ko baka gayawa su Abba ba,ni da kaina zan gaya musu."Ta zura da gudu ta bar shi tsaye, shakare da mamakinta.Kafin ya iso gida kansa,ya kusa fashewa sbd tunani da al'ajabi.Rokon Allah kawai yake yi Allah yasa mafarki yake yi. Kai tsaye sasan su Mama ya zarce.Suna tsakar falo umma ta tirke ta da tambaya,"Idan biki gaya min inda kika je ba sai na sumar dake yau a gidan nan!"Yayi sallama.Umma bata iya amsawa ba,sbd bacin ran da take tare dashi.Ya-ce,'yanzu na koro ta daga shagon Dan-Lati suna zaune bisa benci suna hira Umma.Yaushe Mama ta sauya haka? Tuni Umma ke sallallami,ta dafe kirji ta-ce "shagon Dan-Lati ki ka koma Mama? Mu kike so ki zubarwa mutunci a garin nan? Ai kuwa baki isa ba,ba ki isa ba Mama!'Ji ka ke tim! Ta rufe ta da duka ta ko'ina.kafin yaya Ali ya kawo mata dauki,ta sha dan banzan duka.Kukan ta ya watsu cikin sassa,matan gidan da kananan yara suka sheko don ganin meke faruwa?Al'amarin ya daure masu kai,ganin Mama na birgima tsakar falo tana ture hannayen Yaya Ali dake kokarin rarrashinta BAKIN CIKI 2***2(TRUE LIFE STORY) Wa ya mutu Ali? "suka tambaya,yayin da umma ta fito daga daki dauke da wayar rediyo kafin su yi aune,ta fara tsula mata.Haba gaba daya matan suka cafke hannun Umma, 'Hajiya Halima! Lafiya wannan abu haka?Me ta yi da zafi irin wannan duka?" Umma na haki tace wai yarinyar nan ita ce zata siyar mana da mutunci? Ta rasa wanda zata tsaya da shi, sai Dan-Liti? "Dan-Liti? Waye Dan- Liti?"Dan gidan Buzu mai shayi mana! Yau kwana uku kenan muna fama da ita ta rabu da yaron nan,ta ki! Jiya yazo kofar gidan nan.Alhaji da kansa ya same shi ya gaya masa tana da rana a kanta.shine don dibar albarka ta bi shi shagon sa,yanzu Ali ya ganta ya koro ta! Wace irin tijara ce wannan sbd Allah! Tuni suke kallon juna suna tafa hannu,hajiya hajo tace "danliti kuma?Waye bai san tarihin su ba a garin nan?Yaron da tun tasowar sa garin nan basu da aiki sai bata 'ya'yan mutane koda baki da wayau sosai ai kin yi dan hankalin da zaki gane buzu mai shayi kasurgumin kwarto ne,shi kuwa danliti kananan yara sau nawa ana kama shi dasu?Ko kin mance ranar da dubu ta cika suka ci shegen duka.Danliti ya sha da kyar shi kuwa buzu ya shura barzahi?Me ya dawo da shi kike kwadayi da har idon ki ya rufe kika kasa duban kazantar dake tare dashi?Hajiya Gaje tace "duk ba ma wannan ba kina nufin zaki fasa auran Al-ameen ne?Umma tace,karya take yi sai dai bayan ran mu,bari kuma alhajin ya dawo,yau din nan zai maida ta minna tnda zaman naki anan abinda ya haifar kenan!Ta tashi da gudu ta fada dakinta har da danna sakata ta bar su nan suna maida yadda aka yi. Shi dai yaya ali tunda ya sunkuci jakar sa ya fada dakin mahaifiyarsa bai sake kyakkyawan motsi ba sai tsabar tunani.Muryar mahaifiyarsa yaji a kansa tana fadin,"kai kuma yaushe ka shigo garin?"Firgigi ya dube ta na'am!"Ta zura masa ido,nace yaushe kazo?Ya sauke gwauron numfashi yace,"zuwa na kenan inna".ciwon daya sami mama,ai ya same ni domin jinin mu daya......"Gafara can sakarai kai ka san wannan,da su ma sun san cewa jinin ku daya ba'a hana ka auranta ba ai sbda haka ban ga dalilin dogon tunanin da kake yi ba,don daga ita har iyayenta basu san ka na yi ba!Gara tun wuri ka halkantu ka gane cewar alhakinku ne ya kamasu!Idan ba haka ba,ina mama,ina danliti? Marasa asali da tushe ga tarin abin gori da na kunya a jikin sa?"Ya dafe goshi idanuwansa suka kara kadawa,yayi hucin zafi ya dubeta,"duk wannan maganar bata taso ba inna abinda nake so ki gane shine muddin mutuncin mama ya zube,to martabar gidan nan gaba daya ta fadi,ashe kuwa dole in damu tnda nima dan gidan nan ne,ga shi kuma mama ta dauko hanyar bada mana kasa a ido. Tace can dai zata badawa iyayenta masu kwadayi,ban sa aka ba balle ya dameni wahalar banza kake yi dama ruwa da abinci ka samu ka ci,daya fiye maka wannan sakarcin!Ya sake dafe goshi yana kada kai,me yasa innar sa baza ta gane ba?Takaici ya kara kama shi ya sunkuci jakarsa ya koma dakinsu.Haj Gaje ta shigo saboda gulma ta cigaba,sharri kala kala suka yi ta jifar uban dawaki da su.La'asar sakaliya abba ya dawo gida ya iske idanuwan umma sun jirkita jajur!Ga kumburi sun yi,ko bai tambaya ba ya tabbatar akwai abinda ke damun ta,don haka ya kasa cin abincin data kawo masa,ya zura mata ido yace kamar akwai abinda ke damunki sadiya? Tace akwai matsala alhaji amma ka ci abincin sai mu san abin yi."Fuska ki ta bayyana tashin hankali dake tare da ke ban jin abincin nan zai iya wuce min ba tare da naji damuwae ki ba.Gaya min uwargida,ni kadai gareki wanda zai saurari kukan ki."Ta dan yi murmushi karfin hali tace mama zata siyar da mutuncin mu a garin nan gara ka dauketa ka maida minna ko abj ta zauna can har zuwa lokacin bikinta."Gaban sa ya fadi yace,me tayi?Bata daina zuwa shagon yaron nan ba,yau ali da kan sa ya koro ta tana zaune bisa benci suna hira,benci fa a kofar shagon bakin titi?Kamar mama yadda muke a garin nan take zama tare da danliti?Ta goge kwalla,ina zan sa BAKIN CIKI Alh,anya kuwa mama ce ke aikata wannan abu?Hankalin alh yayi mummunan tashi ya fuskanci umma da kyau ya sanyaya murya yace,ki daina zubda mata hawaye halima ke mahaifyarta ce,sai abin ya kara wargaje mata......" "Ba yin kai na bane alhaji,hawayen ke tilasta wa kansa zubowa."Yace duk da haka ki rinka daurewa kina mata addu'a,insha Allahu gobe zan maidata minna ko ta ki ko ta so dole ta zauna.Ni abinda ban gane ba shine,tana nufin ta fasa auran Al-ameen ne?Idan wani abu yayi mata ai sai tayi bayani,ba wai ta nemi ta maida mutane sakarkaru ba!Ina take ne?"Tace tana daki a kulle tun safe daya koro ta,haushi yasa nayi mata duka har ynzu bata fito ba."Ya mike cikin fushi ya nufi dakin ya buga da karfi yana fadin,"tashi ki bude kofar nan!"Tana budewa ya cafko hannunta ya jawo ta zuwa falonsa,hakan ya sanya mama cigaba da tsiyayar hawaye,ya cillata tsakar dakin ta zube gefen ummanta.Ya zura mata ido yace,"ashe wani lokaci zai zo da zamu ce ki bar abu ki ki bari mama?Kin dai san maganara auren ki da al-ameen ko?To ynzu nake so ki gaya min manufarki ta bin danliti shagonsa.Gaya min inji tun kafin mu tara 'yan kallo!Tayi kasa da kai kukan ta ya karu.Abba ya daka mata tsawa,"kuka na tambaye ki? Ki gaya min dalilin bin sakaran yaron nan nace?Ta cigaba da share kwalla tana mutsu mutsun rashin gaskia,leben ta na makyarkyata tace,"shi....shi na ke......na..na...ke so ab...."Umma ce ra doke ta da bayan hannu tace rufe mana baki mara kunya!"Ta dubi abba dake tsaye sake da baki tace,"ka ji ko?Ni na san take-taken ta kenan!"Ya matso ya cafki kunnenta cikin tsawa yake magana."Idan barci kike yi to ki farka ki bude kunnuwanki da kyau ki saurare ni! Ni ba tsohon banza bane,in har kin ga ki auri yaron nan,tabbaci hakika ni uwaisu na mutu an binne ni cikin kabari na! Ya girgiza kunnen kamar zai tuge shi,kin ji ni! Wannan itace magana ta karshe da zanyi akan danliti kuma gobe ki shirya kayanki zan maida ki minna!"Ya shirga mata dundu tare da fadin,"tashi ki bani wuri!Ai bata iya tashi ba nan ta baje ruf da ciki sbda tsananin zafin dundun da yayi mata abnda bata saba ba,sai ta ji shi har cikin kayan cikinta sun dau zafi ba kadan ba,Ta fasa kara mai shiga zuciya tace wayyo Allah na shiga uku! Na shiga uku! Yaya ali ya mike a firgice,gabansa ya yanke ya fadi ya fito da sauri yana tsinkayar kukan mama,ya nufi sasa.Umman ke fadin,'ba ki shiga uku ba mama sai nan gaba muddin baki dauki nashihar da muke yi miki ba!"Hannu biyu yaya ali yasa ya ciccibe ta ya mikar da ita,zafin duka da tsananin BAKIN CIKI dake dankare cikin ran ta yasa ta kwakume.Yaya ali bakin gado ya zaunar da ita ya dago fuskar ta hannu biyu yake share hawayenta,yayin da nasa kwallan ke neman sauka,yace "haba mama ki yiwa kan ki fada mana!"Murya na rawa tace,me nayi masu yaya ali!Sbda Allah me nayi?"Me kika yi? ynzu a wajen ki wannan ba laifi bane?Haba mama!Ba haka kike ba,kin sauya da yawa kar dadin bakin danliti yasa hankalin ki ya gushe,laifin me al- ameen yayi miki kike so ki yi masa wannan sakayyar?A zato na koda babu Al-ameen nine mutum na farko daya kamata ki fara kawowa ran ki don na dade ina yawo da ciwon son ki mama.Ki tausaya mana me zai sa ki canza kyawawan halayen ki? Ya Girgiza kunnen kamar zai tuge shi. Kin ji ni! Wannan itace maagana ta karshe da xanyi akan Dan-liti, kuma gobe ki shirya kayan ki, zan maida ki bani wuri. Ai bata iya tashi ba, nan ta baje ruf da ciki, saboda tsanannin xafin dundun da yayi mata. Abinda bata saba ba, sai taji shi cikin kayan