← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 79

Sashe 56

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da tayi nadama. M. Kasim yayi shiru, jawabin Uban dawaki na cike da tausayi, ya numfasa, yace, na yarda da kai Alh. Sai dai har yanxun ina rokonka, da ka sake bata dama ta karshe, mu gani.idan bata daina ba, to muma sai mu tsame hannayen mu. M. Kasim ya cikwa Abba ido kwarai da gaske, ya jima kafin ya numfasa, yace, shikenan ba komai nagode. Yace nima nagode, Hajiya akara hkr, a bata damar karshe, tace babu komai M. Kasim, Allah saka da alkhairi. Yace amin, barin in koma in turo saude ta dawo ita. Tace to ka tsaya kaga abin kari akawo maka mana, ya mike cike da fara'a, yana fadin alhmdlh, kar ki damu nagode, to nabr ku lfya, Allah ya shige mana gaba, suka amsa amin. Yaka hanya fice. Bayan tafiyarsa kamar da hadin baki, jama'a sukayi ta xuwa suna ba uban dawaki hrk tare da rokonsa ya daure ya maida 'yarda gabasa xai fi kyau agareshi. A cikin su har da abokansa da yaron gidansa, watau kalla. Duk ya karbi rokonsu, kuma yaji dadin kulawar jama'a gareshi tare da tausaya masa akan kaddarar da ta fada wa iyalinsa. Karfe Tara saura, Inna saude ta taso Mama xuwa gida. Bata ma biyo da ita ta shagon Danliti ba, balle ya gansu, haka suka taru da matan gidan kamar zasu cinye ta danya, sannan matza suka shigo suka dasa nasu. A gaban kowa suka tilasta, ta dauki alkawarin ba xata sake xuwa ko ina ba, kidan kuwa ta saba, to a yanke mata hkunci da yafi wannan. Kwana 2 hatsaniyar nan ta kwnata, mama na xaune cikin gida bata fita daidai da tsakar gidan sasansu. Muna iya cewa Danliti bai murda kambunsa bane haka? Saboda haka xuciyar Mama ta sami 'ya nutsuwa. Bata ita kadai ba, su abba ma sun sami 'ya nutsuwa har tana debo 'ya'yan itatuwan da Abba ya ka siyo ta kawo mata, tace ta sha saboda rashin cin abinci da take fama da shi..... ***************** A wannan asabar din ma abdulkrm ya xo daiyalinsa duka. Su ameera nata murnar ganin auntynsum domin sun jima basu ganta ba. Dr. Na ta dabo, yana son ya taka, sai 'yar banxar kuiyam shi ya sa yaki yarda Mama ta daukeshi. Aunty Rabi ta tasa ta da nasihohi, ayoyi, hadisan Manxo SAW akan ta dage ta yaki xuciyarta ta dawo kan kanya, sannan ta nuna mata wannan ba shine soyayya ba, duka saurayin da ya nemi lalacewa da yarinyar da yake so, a hakikanin gaskiyya ba son gaskiyya yake mata ba. Sha'awar sassan jikinta kawai yakeyi. Haka yayanta ta tsatsagge mata gaskiyya, har yayi mata alkawarin idan ta nutsu ta xauna gida kamar yadda aka umarceta, to bayan ta haohu za'ayi bikinta, duk abinda take so, shi xai sayo mata. Mama ta wani kuka tana ba su ameera tausayi. Anann suka kwana, washegari lhadi karfe 12noon suka juya. Su ameera nata tambayar antyn su yaushe xata xo? Tace kar su damu tana nan xuwa nan bada dadewa ba, suna isa gida, yayan ya kira 'yan uwansa, ya labarta musu abinda ya gani game da Mama, idan har ya dore a hakan, alhmdlh! Ana iya cewa an fara samun nasara. Kowa yayi farin ciki jin wannan labarin da fatan Allah ya shige mus gaba. Allah, da ikonsa a yammacin yau din, tun bayan sallar la'asar mama ke cike da kewar Danliti, kafin 5pm ra mance kaf! Da alkawuran da dauka, babu abinda take so face gain Danliti, kewarsa ta gigita kwakwalwarta, ta birkita ta. Kamar an tsikare, kawai ta tashi ta suri gyale da takalmi ta fito kanta tsaye ta fice abinta. Dan gogan ta samun cikin dakin barcinsu, tana shigowa yana xubawa wani kaskon rushi ruwa, ya dago ido ya dubeta, yace ba xan miki sannu da xuwa ba. Ta xaune gefensa tana murmushi, saboda me? Ya xubo mata harara, yace kwanaki nawa rabon ki da nan? Sabo da nayi miki fada ko? Ta rungomoshi tana dariya, ayya nawan ba haka bane, kowa yasa min ido, sai surutai sukeyi kamar ni kadai na fara soyayya agarin nan. Amma kana cikin raina, kaima ka sani, bani da burin da wuce in kasanxe tare da kai, ta bae baki yace tsarani, au baka yarda ba? T yanxun ba ni na xo ba? Dana kiraki ba? Ka kirani? Kamar ya? Ya ture kaskon ba xaki gane. Sai dai na yarda kina sona, tunda kika amsa kiran. Ta xura masa ido tace ngode, tunda kasan hakan, me kake yi da kasko? Ke duk xamanki a dakin nan baki taba ganinsa ba? Da shi fah muke turaren daki. Kai amma wannan bai hadu ba, kauri gare shi, kin kuwa san tsadarsa? Ai ku maza ba gwabe bakin ku ake wajen siyayya? Kabari xan kawo maka mai kyau, idan ka sanya shi sai makwabta sun tambayeka ina ka samo. Ko? To sai kin kawo din. Yanxun mu ake maganar turare, ina kuka kwana da su Abba? Ta tabe baki, me ma? Wai an bashi hkr ya kyaleni, amma idan na sake xuwa nan, dole in tafi. To kice kin karya doka, tunda gaki kin sake xuwa, ni kuma da har nayi cinikin wani gida can bayan tasha, ina fasa kenan? Bakinta har kunne, tace ka fasa kuma? Ai xai mana anfani idan munyi aure ko? Ya shafa kai, gaskiyya ne, xan biya kudin in sa a gyara shi, ai sau muje ma ki ganshi ko? Ya xama dole, yaushe xamu? Duk tym din da kika shirya. Ko yanxumn a shirye nake, mu tafi kenan? Bismillah. Ta sumbace ta yace, amarya ta kenan, maman bebi! Ta rausaya da kai tana dariya. Tare suka fito yana rike da hannunta, har gaban motarsa. Ya bude mata ta shige, ta dawo maxauninsa yaka suka tafi. Gidan ginin kasa ne mai dauke da dakuna 2 kicin da bayi, tsakar gidan turbayar kasa ce, haka ginin babu digon siminti ko kadan, zallar kasar ce kawai, illah iyaka cikin dakunan anyi masu dabe, suna tsaye kafada da kafada, ya dubeta yace, kinga gidan, ina fatan yayi miki? Ta yake baki ta makalo wuyansa tace, ya fiye min kowannne irin gida muddin da kai xan xauna cikinsa. Kar wani abu ya dameka,a hankali na gyara shi, kyau xaiyi fa, yayi dan murmushim ya falla ido sannan yace, toh shikenan, tunda yayi maki, yau din xan nemi dillalin in bashi kudin. Ta kara kankame shi tace, ina tayaka murna. Ya xubo mata ido yace ni xaki taya murna, ko ke xan taya murna, gidan ki ne fa? Tayi dariya sosai. To dukkan mu Congratulations! Ya sumbaci labbata, tace thnk U! Sun jima cikin gidan suna sharholiyar su, ana kiran magriba, suka fito, ya kulle kwadaon gidan suka koma shago, maimako ta koma gida sai ta rashe nan, tana nishadantar da shi, kamar yadda ya bukata, ya siyo mata abubuwan da take so, tace, tayi hani'an, kai barci sace ta mana, ta yada kai bisa filo tai tayi kuwa...... 11pm za su kulle hsago, ayuba yayi juyin duniyan na Danliti ta tashe ta, ta tafi gida amma yaki, ya kuma hana Ayuba ya tasheta. Da ita suka kulle shago, ayuba ya kwana tsakar shagon, shi kuwa dan gogan yana tare da gimbiyar. Tsakar dare ta farka da ganta tare da mutum. Ta tashi xaune ta bubbuga shi ya tashi, menene? Tace dama ban tafi gida ba? Yace ga shi nan kin gani, ai da ka sani ka tasheni Danliti. Yace waya gaya miki ana tashin mai ciki barci? Kiyi kwanciyarki kawai da safe kin koma, Abba xai koro ni Danliti, yace akwai gida na biya kudinsa, baki da haushin wannan. Idan kina kwanciyarki, ki kwanta ida kuma yanxun xaki fita 2am ga hanya nan babu ruwana. Bebi na kawai nake ji. Ta watso masa harara ni banda ni ko? To! Na ga kin wani hakikance ne, meye sabo idan kin kwana anan? In banda gulma! Ta dare ruwan cikinsa ta kai masa duka, ni ce magulmaciya? Kai din fa? Todama mai neman kuka ne aka jefa shi da kashi awaki, sai yaya? Washegari, yadda bata sallaci magriba da isha ba haka batayi asuba ba, karfe 7am ta dauko hanya. Gata nan ga nan har gida, salalau- salalau ta karaso ciki, ta iske duk sammakonta Abba ya riga ta tara jama'am don haka tana xuwa tsakar falo, tayi sanrada. Gwiuwa 2 ta xbe ta fara kuka. Kowa ya saki baki yana kallonta, M.kasin ya fara magana, yanxun saboda Allah Mama duk maganganun da aka gaya miki ta bayan kunnunwaki suka wuce? Ashe haka kike da taurin kai? To mu babu ruwan mu, dama rokonsa mukayi, ya ga girman mu ya hkr, tunda ke baki gani ba. Shikenan ga hanya na, ki bi duk wacce kika xaba. Abu yaya kamari har da kwana? Ke Mama kiji tsoron Allah ki tausayawa iyayenki. Ba xata suka ji tana magana, wlh Baba bada niyyara kwana ba na fita, Danliti ne ya sayi gida, yace muje na gani, mun dawo ina hutawa, ban tym din da barci ya kwasheni ba, abba ya xaburo yana fadin, kunaji Maganar Banxan da take fadi ko? Kun tabbatar da cewa abinda nake fadi gaskiyya ne? To ya isheni haka! Ya isheni haka!! BAKIN CIKI ba xai akshe mu ba. Daga nan ki juya ko koma, idan har ki na son kanki da arxiki, wlh! Wlh!! Babu wanda ya ya sake roko na in kyaleki cikin gidan nan! Duniya ce da fadi, karki saurara wajen bin ta kwararo-kwararo har ki gano iyakar ta! Tashi ki bace min da gani, kafin in kusa kashe ki da duka. Gaba daya falon yayi tsit, sai shasheshekar kukan Mama, jim kadan muryar abba ta kara gauraye falon, kai Jama'a! Ina xan kai takaici da BAKIN CIKI? Me nxan yi wa yarinyar nan a dniya na huce, banda in sallama ta, tamkar ban taba haihuwarta ba? Ki tashi fice min nace, in daina ganinki a gabana..... Ki ta... Kawai sai ya yanke jiki ya fadi, gaba daya suka mike da sallalami sukayi kansa...... Toh masu karatu, wannan fa shine wasa farin girki. Nayi iya kar kokarina ace nayi muku sallama anan. Amma ina abin ya faskara, kuyi min hkr karshen badakalar wannan littafi yana cikin 3, ku biyo ni,
Chapter 56 · 0% Book details