← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 79

Sashe 8

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ya kasa tada motar. Ta sake lekowa tayi masa bye-bye shima ya daga mata hannu sannan ya sami karfin tada motar yayi ribas yai kwana ya fada hanya ya kara dago mata hannu ya wuce cike da begenta tamkar yadda takeji a ranta. Tana shiga cikin gida muryar Ya Ali kawai ke tashi yana bambamin fada "ai dama haka rayuwa take kiri'kiri jininka saiya wulakantaka don baka da kudi! Muma muna kan hanya indai arzikine abuna Allah! (Kana da gsky Baffaba!) Mama tayi tsaye jikin kofar sassansu tana saurare haj Hajjo tace nace dai kayi shiru haka ko? To kaci gaba idan hakan shi zai sa a baka ita. Mama dai ba saurana mata tafi ba ga yanmata nan bila adadin duk wacce ka zaba sonka zatayi idan ita ma ba kwadayi tasa wa ranta ba. Sbd haka kar in sake jin wata magana ta fito daga bakinka akan wata Mama! BARKA DA SALLAH HAUSA Novels BOOK BAKIN CIKI 1****5 H. Gaje ta cafe, "ki kyale shi ya amayar da bacin ransa, kar ya zame masa ciwo! Da wanne zai ji?" yace, "ai inna ba zata gane ba mama gaje, wannan rainin arziki ne a ckn gida. Uwa daya uba daya? Haba! Ya kamata a duba!". H. Hajo tace, "wa zai duba? Lallai ranka zai fita idan har zaka kwallafa wa kanka wannan maganar!" Tana sa aya daidai da sallamar uban dawaki, yayi tsaye yana kalln mama na zubda kwalla, yaynda yaji muryar h. Gaje na fadin, "babu wnda zai duba wannan al'amari, tnda dai shi da kansa alh. Babban ya ya yamutsa al'amarin!". Kalaman da suka fada kunnuwan uban dawaki tare da bugun zcy, ya zurawa mama ido tamkar ynda take kallnsa, "me ke faruwa?". Bai gama rufe baki ba yaga Ali ya fito a fusace, idanuwnsa na tsatso kwalla. Shi kansa gabnsa yayi mugun faduwa, kasala ta kama shi, ya rage sauri, "kai ali lfy?". Ya gnge fuska, ya dan rankwafa yace, "sannu abba!" "nace me ya faru?" "babu komai" "ina wasa da kai ne? Kake gaya min babu komai!". Mama tace, "abba tun jiya gidan nan a yamutse yake, ana ta habaici tare da yada magana akan zancen al'ameen. Umma taki gaya maka ne sbd gudun fitina. Amma kowa gani yake yi sbd kudi ne yasa ka amince inyi aure, bayn ka hana kowa kace karatu zanyi. Me yasa za'ayi mana mugun zato?" Nan da nan ransa ya baci, yayi fushi sosai, ya kwalawa umma kira. Ta fito ta samesu ransa bace. Ckn fushi yace, "kira min matan gidan nan!" "lfya alh?" yace, "ban son jin wata magana". Tace, "alh ka kwntar da hnkalnka kayi hakuri har zuwa lokcn da mazajnsu zasu dawo. Zai fi kyau duk abnda zaka fadi ka fada a gabnsu. Ina rokn wannan alfarmar don girmn Allah!". Alh. yayi jim! Shiru yana kalln umma, kafn ya dubi mama yace, "kin shirya kayanki?" tace, "eh" "to kwaso ki zuba a mota maza mu tafi". Ya wuce da sauri daknsa, kowa ya kama gabnsa, har da ali ba tare da wani ya kara cewa komai ba. Kayn jiknsa kawai uban dawaki ya canza, yayi rawani kamar ynda ya saba, ya fito lokacn mama na tsakar gida da jakar kaynta tare da tsarabar da umma ta bayar a kaiwa yara. "Baki kai kayan motar ba?" inji abba. Tace, "ai basu da yawa, su kenan" "wuce muje". Umma tace, "Allah ya tsare, a sauka lfya". Ya amsa da amin, yayi waje. Mama ta biyo baynsa. Ali na zaune bisa dakali tmkar yayi bindiga sbd tsabar fushi da kishi, domin sosai yake son mama. Kuma yayi wa ransa alkawari zai ci gaba da farautarta, sai yaga abnda ya turewa buzu nad'i. Shi yasa ya aje wa ransa zai iya jiran ta gama karatnta. Shi kuma zai ci gaba da gina kansa da duk wani tanadi wnda zaizo daidai da jin dadin rayuwr aurnsu. Ina zai sa ransa yau yaji dadi? Yana ganin mama ta shige mota idanuwnsa suka yo tam! da hawaye. Musamman wannan zuwan ita yazo gani, sanin cewa sunyi hutu. Kamar ya kwarma ihu. Ya mike ya sake fadawa ckn gida. Alh. Ya bude mota, kalla ya matso, "ranka ya dade tfya za kuyi?" yace, "ai tare zamu tafi da kai, taso ka shiga mota. Minna zan kai mama na" yace, "to shi kenan". Ya mika masa makulli, "ka tuka motar kalla, bana jin dadin jiki na". Ya amsa yana fadin, "assha! Allah ya sauwake" "amin". Ya bude gidan baya inda mama take, shima ya shiga. Jikn mama ya kara sanyi, tasan abbanta ya kanso suyi tfya su 2 kacal! Suna tafe yana bata labarin duniya. Ta tabbata bacin rai ne yasa ya gayyato kalla ya tuka su, gudun afkuwar wani abu. Sun mika tfya shi babu mai magana, shirun sam baya mata dadi, sbd haka tace, "Abbana kayi hakuri don girman Allah, kar hnkalnka ya tashi akan wannan maganar". Ya dubeta sosai yace, "dole raina ya baci, sbd an zarge ni akan abnda ba shine a ckn zcyata ba. 'Yan uwana basu yi min adalci ba, na tabbatar da saninsu mataynsu ke yada habaici da kananan maganganu. Amma zanyi wa tufkar hanci. Tnda babu wnda ya haifa min ke". "kara kayi fada dasu abba....." yace, "ya za'ayi in tsaya ina fada da kannina? Umarni kawai zan bayar, kuma dole kowa yabi idan ana son zaman lfya. A iya sanina na basu hakknsu, na zauna da su na gaya musu uzuri na. Amma duk da haka basu gane cewar komai na Allah bane. Ke dai abnda nake soki dashi, ki rike yarn nan amana, sannan ki kara kula da kanki, don tsare martabar gidan nan" tace, "Allah ya taimaki mai martaba. Mamanka na tare da albarkar umma da abbanta, da yardar Allah ba zata basu kunya ba". Yayi dan murmushi yace, "Allah ya kara yi miki albarka". Tare da kalla suka amsa, "Amin abba Sun iso minna la'asar sakaliya, shi yasa ruwan alwala kawai alh. Ya fara tambaya. Yayi sallah a babban falon gidan, yaynda jerin kayan abincnsa ke jiransa. 'yan jikoknsa kuwa sai safa da marwa suke yi. Ya idar da sallar, suna jiran su tumurmushe shi. Ilai kuwa yana idarwa suka zube a jiknsa, yana drya ya soma tsokanarsu" "ameera tsohuwa mai majina" tace, "Allah ameer ne mai majina" ameer yace, "karya ne abba, kullum wa ake ba tishu in zamu skul?". Abba yace, "kyaleta Uwair, waye bai san halima tsohuwa bace? Mai majina kawai". Ai nan da nan tayi fushi ta tashi fuu.... Zata fice,suna mata drya. Sai ga sallamar anti Rabi. "momy kin gansu ko? Wai nice mai majina". Ita ma dryar tayi ta wuce ta zube gabn abba ta kwashi gaisuwa, sannan ta tambayi mutan gida. Yace, "duk lfyrsu kalau" Kuka ameera ke yi, yaynda mama ta shigo da ita falon, "ynzu don Allah wa ya taba min umma na?" yace, "kyale ta mai majina ce, ni bana auranta!". Ta kara kware baki, mama ta rungume ta, "kiyi shiru ki kyale shi, ke ma baki auran. Me zaki yi da shi tsoho?" ameer sai drya yake mata. Da yaga kukan da gaske take ynsa sai ya jawota jiknsa, "wanene ya taba min madam dita? Manta da ameer, tsoho ne shima. Ina dady bai dawo bane?" ta amsa da kai tana murzar ido. Anti rabi tace, "bai shigo gida ba tukuna, amma yana bisa hnya". Yace, "To Allah ya dawo dashi lfya" suka ce amin..anti rabi da mama suka bashi wuri yaci abinci tare da jikoknsa. Yan minticoci bayan kammalawarsa motar Ya Abdulkareem tayi fakin a harabar gidan, ganin motar Abbansu yasa ya fito da sauri kalla ya tarbe shi ya karbi jakarsa yayi masa sannu da zuwa suka gaisa, tare suka shigo falon ya zube gaban Alh yana fadin oyoyo abbanmu! Yace Abdulkareem dan Abba sadauki! Ya kara fadada dariyarsa domin yana jin dadin kirarin da Abba yake masa tun yana yaro sbd tsananin kokarinsa wajen neman duk abnd yake so musamman ilimi. A yaran gidan kaf! Babu wanda ya fara sauke Qur'ani da karancin shekaru sai shi, yana 14yrs yayi sauka kuma yasan littattafai dayawa. Daka dubeshi kaga Mama illa dara daran idanuwanta ne kadai suka banbantasu. Kazo lfy Abba? Yasu Umma? Yace lfy lau Mamana na kawo maka hutu.....Mama? Yanzu haka tana ciki? Sai gata ta shigo falon ta karaso gunsa da gudu ta zube jikinsa Yayana!. Ya kamo kunnenta ba wani yayankitashi zakiyi ki koma inda kika fito! Tace Allah sarki yayana dan Abba sadauki! Ya dada mata duka suna ta dariya "maras kunya ba Abj kika fiso ba? Ai dama nace duk randa kikazo yan kafafuwan zan karya.. Tace, "tuba nake yayana, daga yau duk hutu anan zan yi shi" yace, "naji amma ban yarda ba, ke da soja ai sai Allah, watakila kema sojan zaki aura". Ta kada kai ckn shagwaba, "a'a!" Abba yace, "ai baka ma sani ba? To karkade kunnenka kasha labari". "ko abba? To bani insha". Abba na bashi labari, ita kuma mama na boye a bayn yayn nata. Tas! Ya zayyane masa abnda ke faruwa. Abdul-kareem ya cika da mamaki, "to menene abn tashn hnkali a nan?" yace, "nima shi na gani, har ga Allah zcya ta bata da wani nufi akan wannan al'amari, amma tnda haka suka dauko zamu tafi a hakan, kuma mama zata auri wnda take so". Ya dan kada kai yace, "kayi hakuri abba, kasan shi mutm a kullm yakan fi son kansa maimakn neman zabn Allah. Abu kankani sai a ruruta shi yayi girman da zai rarraba kan zumunci. Abba ka dauki girma kamar ynda ka saba, ka dauke kai ga tsegunguman mata". Ya zura masa ido yana murmushi, "dan abba sadauki! Duk abnda ka fadi gskiya ne, shi yasa ma bazan gaya wa yaynku ba, don nasan halnsa, daga ali har mutn gidan babu wnda zai kyale idan hauknsa ta tashi". Yace, "haka ne, kuma nasan ali yana son mama, dole yaji zafi a rnsa, amma su a matsaynsu na manya ai bai kamata su rika tnzira shi ba. Abnda ya dace shine su nuna masa komai na Allah ne. Amma muna musu fatan Allah ya ganas da su. Ke kuma mama ki rike amana, domin duk garin nan babu wnda bai san familn marafan lafai
Chapter 8 · 0% Book details