Sashe 50
Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ni kike wa rashin kunya? Lallai kin rika, kina gab da tsinka min mari akan Danliti. Sallamar da jiyo, shi yasa tayi shiru. Ta mike ta fito tana amsawa. Inna saude ce da Baraka, saude sannunku da xuwa. Duk suka amsa, yayin da Baraka ta tsugunna ta cigaba da gaisawa. Bayan sun nutsa a falon, inna saude tace, tun jiya naso fitowa, wani axababben ciwon kai ya addabeni. Tace ayya ina fatan yayi sauki. A'a da sauki, ina maman? Tana ciki ta shiga wanka.... Wai dama saboda ita kika zo? Ai da kin yi kwanciyar ki kin huta, domin al'amarin Mama ya zama jiki. Tace, ya xama dole in taso yaya. BAKIN CIKI kuwa baya taba zama jiki sai dai imani. Allah dai ya bamu ikon cinye jarabawar, ta nisa tace amin. Tace, yanxun me kuke ciki? Ta fada mata yadda al-amarin yake, ta cire tagumi. Tace haka shi yafi dacewa, in ma banda sakarci ba ita xata taimaka mana ya turo da wurin a huta ba. Tace ina fa, ai ina mai tabbatar miki tafi son shi akan mu. Allah dai shi kyauta. Ta amsa da amin. Suka ci gaba da hira har suka ji motsin fitowar Baraka ta tashi ta shige dakin. Ba suyi wata hirar kirki ba, domin ra'ayinsu yasha bambam yanxun. Duk mai zagin Danliti Mama bata ganinsa da kima haka ta fada ma baraka, shiyasa ta shiga taitayinta, tafito daga dakin tace xata ganin amare. Mama dataga shirinta can ta sameta dakin amaryar Ya Ali, nan suka shantake, sama da 2hrs sai da Inna saude ta shiryo tafiya tasameta can, ita ma bata yi ma Mama maganar komai ba akan abinda ta aikata. Domin a tunaninta babu wata bakuwar kalmar da xa agaya mata wacce bata sani ba. A wannan daren mama tasa ido taga xuwan Danliti shiru kakeji yasa ta jin haushin rashin dawowar abba. Al- amarin nata cizon ta taga ba xata daure ba, karfe goma harta goa, ta fito ta bude kofar ta fice abinta. Ko kafin Umma ta fito taga wanda ya bude kofar mama har ta kai kofar gidan, ganin bata a dakin ya tabbatarma da Umma ita ta fita. Ta nemi kujera ta xauna hannunta a kunci BAKIN CIKI ykamar ya kasheta. Take nan taji xuciyarta na ciwo, wani abu dum! Cikin kanta kamar xai makantar da ita, tasbihi ta shiga jerawa ko ta samu saukin kan. Ita kuwa mama Tunda ta kwashi sauri bata sausauta ba sai da taje shagon mutumin nata ta ja birki. Ayuba na xaune daga ciki, taga kanta ta shiga tare da sallama. Ya amsa mata ta wuce tana fadin sweetyna naciki ne? Da sauri ya amsa mata ai bayana nan bai gaya miki bane? Ta tsaya cak dauke mamaki, ina yaje? Ya amsa gaskiya bai gaya min ba, cewa yayi xaiyi tafiya kawai. Na xaci ya gaya miki daxun. Ta kada kai, bai gaya min ba wlh, amma xai dawo gobe ko? Yace watakila, ta danyi shiru sannan tace to shikenan sai goben. Allah ya kaimu. Taga kanta ta fice, ya bita da kallo. Duk tasuayinta ya lullbe shi, aransa yace Allah ya kubutar dake daga sharrin Danliti. To nima nace AMEEN! Da babbar murya. Tana tafe tana sakar xuci, wai duk fushin ne yasa Danliti yatfi ba sallama? Ina xansa kaina idan kalaman Abba suka korar min Danliti? Bata samo amsa ba taji ann fige mayafinta, 'yammata ji mana! Firgigi ta waigo hankalinta ta dubi gungun samarin da suka kai kusan shida, kowanne su dauke yake da tabar wiwi. Ta dora hannu bisa kai wayyo nashiga uku, duk suka fashe da dariya, ina kika nufa mu rakaki? Ta durkusa kuyi hkr dan Allah, dariya kwai suke kyakyatawa, 2 daga cikinsu suka kawo mata cafka. Ta xabura ta mike, Allah ya taimaketa ta kutsa ta cikinsu ta xura aguje, dawa Allah ya hada su ba da ita ba, ta watsar da takalma, ko daman gyalen yana hannunsu, taci gudun fitar rai, ta rufta cikin gida, yayin da alh. Adamu, ke kokarin rufe gidan, bakara min figita yayi ba, amma yayi axama ya maida kofar ya jefa sakata. Mama kuwa tuni tana sassansu, ta fadi warwas! Tana maida numfashi tamkar xata mutu, Alh. Adamu ya biyota, ya isketa daidai kasa, ya xura mata ido kafin yace, wai daman mama ce kartin Maxan nan suka biyota? Me kike a waje har 11pm? Umma tayo waje tana sallami, ganin mama a kasa yasa ta dafe kirji lfy? Ya dubeta ido waje, yace, yanxun saboda Allah me yarinyar nan take a waje cikn duhu? Kinga kartin da suka biyo sunyi su 10, wannan ai diban albarka ne da iskanci. Jiri ya soma dibar Umma tana fadin me? Innalillahi Wainna ilaihir raju'un kasan Allah, Alh. Adamu har na rufe kofa naji motsin fitarta, xaune nake kawai narasa inda xansa kaina dan BAKIN CIKI! Ban san yadda mama ta maida rayuwarta ba......... Tana rufe baki, tayi kasa da dafe kirji, saboda ciwon da yake tsananin yi mata. A hankali hawayenta ke fita tana fadin, BAKIN CIKIN ki zai kashe ni Mama.... Alh. Adamu ya daga murya yana masifa, kin shiga 3 mama! Kin maida kanki 'yar iska da karfi da yaji, to ki bi a hankali, muddin kika bari BAKIN CIKI ya kashe mahaifanki, kin buga babbar asara, tashi ki ba mutane wuri, kafin in taka ruwan cikinki. Ta yunkura ta tashi da kyar, amma ta kasa mikewa tsaye, a duddauke ta shige falo a tym din har mutanen gidan sun fara taruwa, don ji me ya faru, Alh Adamu ke daga murya cikin dare? Nan take ya maida yadda akayi har ya dora karya, wai kartin har sun turmusheta, tsawat da yayi masu, yasa suka gudu. Kowa tafa hannu yakeyi yana salati, kusan 12am suna xuba magana. Sannan kowa ya koma sasansu, aka bar Umma kwance da ciwon abubuwa barkatai. Ya ali ne kadai bai tanka ba, don BAKIN CIKIN sa na gaske ne, tamkar yadda UMMa takeji cikin xuciyarta. Dakin amaryarsa ya koma yana kuka da hawayensa. Amina tayi rarrashinsa tana nuna masa addu'a Mama tafi bukata ba kuka ba. Mts!.... Amina ba zata gane ba, BAKIN CIKIN dake cin angonta ba xai iya jurewa ba, tilas sai ya matse shi. Hasalima ba zai iya zama yana kallon irin wadannan abubuwan ba, gara ya koma bakin aiki ko ya kauracewa idanuwansa ganin abinda ya fi komai daga masa ciwon xuciya. Saboda haka yacewa amina ta shirya kayansu gobe zasu koma birnin gwari da yardar Allah. Al'amarin ya daure mata kai, kuma tayi tambayoyin da bata sami amsarsu ba. Washe gari da suke shirin tafiya, taji fashin baki na bakin Haj. Hajjo. Eh lallai biri yayi kama da mutum. Nan take kumallon mata ya taso mata, ya dasa mata kyamar Mama cikin ranta har tafi Ya ali kosawa su bar garin. 12pm kuwa ya samo shatan mota suka damki hanya. Mama bata ma san anayi ba, tana can tana murkususun ciwon ciki ita kadai a daki. Don ko daya shigo yin sallama da umma bai shiga wajenta ba. Sai wajen azahar barci mai nauyi gaske ya dauke ta. Haka ita ma Umma ke ta gyangyadin takaici bisa kujera. Rabonta da abincin kirki tun jiya da daddare motsi taji a falo ana shigowa da kaya, ta taso da sauri ta leko falon. Kalla ta gani da tsirin kwalaye ya aje gefe yana gaisheta. Ta amsa da fara'a ta karfin hali. Bai karasa ficewa ba, abba ya kawo ka falon tilas ya rabe gefe ya bashi wuri ya shigo, sannan ya fice. Alhajin yana fadin, agaida Iyali, yace xasu ji. Kallo daya yayi wa Umma gabansa ya fadi, ya amsa sannu da xuwan da tayi masa. Ya xauna falo. Yayi da ta shiga kitchen dauko masa ruwa ta kawo masa ta xauna gefe tana kara masa sannu da xuwa. Bayan yasha ruwa ya numfasa. Tace an dawo lfy? Ya amsa lfya lau, duk suna gaisheki, ni ne har abuja, daga can na xarce kd yau da safe. Tace, wai kunsha hanya, ina fatan duk lfya ka baro su? Yace kalau, amma sai naga kamar kin rame, ina fatan ba ciwo ne ya tashi ba? Ta kada kai. Kai dai bari Alhaji, ciwo na ba zai taba warkewa ba, idan ban ga yarinyar nan dakin miji ba. Kaci abinci tukunna, kaji abinda ya faru jiya. Yayi dan shiru har ta mike xata dauko abinci kafi, yace ki gaya min kawai Halima, nasan babu bacin ran da xanji wanda ya wuce na baya. Ta dawo ta xauna ta fede masa abinda ya faru. Ya kada kai. Yace ya rage nata, ba burinta ta fita duk tym da ta ga dama ba? Jikinta xai gaya mata, xata gane akwai wadanda suka fita iskannci. Yanxun tana ina? Tana daki, ni yau ko kalarta ban gani ba. Bata xo ta gaisheki ba ke nan? Tace ni a suwa? Bana ma bukatar gaisuwarta, amma tun jiyan na gaya mata idan na mutu, ta sani BAKIN CIKIN tane ya kasheni. Yace, ba xaki mutu ba Halima da Yarda Allah mama ba zata salwantar min da rayuwarki ba. Karki manta, su hudu kika haifa, kuma Allah ya albarkace su dubi tsibin kwalayen nan, duk sakonki ne, kowa na da sa nau'in tsarabar, zabi kalar abubuwan da kika fiso. Bayan haka, jibi asabar duk zasu hadu anan, don su share mana hawayen kukan da Mama ta samu. Don kuwa zau tsaya tsayin daka dole Danliti ya turo wakilnsa a daura masu aure a cikin satin nan. Saboda haka ki kwantar da hankalinki, ki na dasauran 'yal3an da suke bukatar ki kusa da su a koda yaushe. Kinji ni da kyau? Ta goge 'yar kwallan da suka xubo mata, tace naji alhji, Allah yayi musu albarka baki dayansu. Yayi murmushi yana fadin, amin kina iya dauko abincin yanxun. Ta tashi da saurinta, ta wuce, ya raka da ido tausayinta ya kwarara cikn ransa. Ya numfasa yace, mun gode maka Allah da wannan jarabci. Ta fito masa da abin, ya gaugauta ci, domin gab ake da kiran la'asar. Ya kammalawa kuwa tym yayi, ya mike yana fadin, ki shiga ki tasheta tayi sallah. Ta amsa da to, ya wuce dakinsa. Umma ta kwashe kayan ta maida kicin, sannan ta nufi dakin