Sashe 54
Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
da dariya, okundirin ne ubansa? Lallai ka samo shi. Yacee to da waye ubansa? Kinga bude ledar nan nama aciki dauko ki ba shi. Yana magana yana shafar kan karen. Tace, taf ya cafke min hannu? Kai dai ka bashi kai da ka siyo masa,don raka asara. Yace karki bani kunya mana, me xai sa ya cije ki, bayan yasan ke bebina ce, ko kare? Ai ka santa ko? Sweetheart dina ce kar ka cije min ita. Tuni kanta ya fasu, ya jawo leda ya bude ta dauko katon yanka ta mika masa tana fadin, abin har da yaji? Sangarta! Ya kwashe da dariya, yace ina ruwanki? Ke dai mika masa gudan. Ta dauko ta mika masa, ya cafke, Dan liti ya runtse ido yace yes! Ya xarce da dairya. Ta xuba masa ido tace, menene abin dariya har da wani cije labe? Yace ji nayi kamar ya hade da hannunki ya gartse. Takai masa bugu a kirji tace amma kai mugu ne! Yace sosai ma ashe baki sani ba yarinya, to tashi kije gida an gama hirar, kinga karen yayi tafiyarsa. Ka gaida okundiri kaji? Ta ci da kyakyata dariya. Yace, ah! Tashi karki sa yarona ya fito yana fito yana kyakyatawa kamar dolo. Ta shi kije gida sai safe. Don Allah kiyi hkr, so nake nayi wanka inyi sallah. Ta fido lah nima har ka tuna min banyi ko magriba ba. Ta juya da sauri tana cewa, sai da safe! Yace Allah ya kaimu. Ya bita da kallo, yace yarinya kin gama yawo kin shiga 3 kin lalace, ya daga murya ki fa sami abinci ki ci. Ta juyo ta amsa, kar ka damu xanci. Suka ja hankalin mutane, don haka yama didi ya biyo baya, masu tsinuwa nayi, masu addu'ae shiriya nayi. A tsakar gida ta iske su Abba na jiran dawowar ta, shi da su Alh. Basiru. Tana shigowa tasha jinin jikinta, ta shiga bin bango, tana so ta shige falo. Alh. Basiru ya daka mata tsawa, ke dawo nan! Simi simi ta matso gun su ta durkusa guiwa 2, batayi aune ba, taji saukar wani wawan mari. Gaba daya ya ratsa kanta, ya gigita ta, ta dunkule ta fasa kuka. A cikin ba tace ga wanda ya xabga mata wannan marin mai tsanannin xafi ba. Sai dai taji muryar Abba na fadin wannan shine gargadi na karshe da xanyi miki, shi ya sa na tara kowa su xama shaida! Idan har ba xaki bi umarni na, ki xauna a gida ba, to wlh sai dai ki xaba, ko mu ko Danliti! BAKIN CIKIn nan ya ishe mu mama. Gara in sallama ki, in tabbatar da kinfi karfina xaman kanki kikeyi. Saboda haka daga yau kika kara sa kafarki kika fita kikaje gun yaron nan, to kar ki dawo, ki yi zaman ki can wajensa ku sha shagalinku yadda kuke so. Duniya ce Mama, mai dauke da axuxuwa babu adadi! Ina fatan kinji kuma kowa ya shaida! Alh. Basir ya karbe karuwa kike so ki xama ko? To Allah ya baki sa'a, mu dai ba xa mu hana shi ba, duk ranar da koreki. Alh. Adamu yace dama saboda me xamu hana shi? Cikin shege ne fah ajikinki, amma bai sa kinyi nadama ba, to me xai sanya ki kuwa? Karkiji da wai, mun tsame hannun a kanki, haka xuri'ar gidan nan kaf! Kar ki ce kin san daya daga cikinsu, duk ranar da wuya ta koro ki! Ta shi ki bace mana da gani shashasha sakarya. Ta mike da gudu ta fada dakinta, ta dasa kukanta, a fusace abba ya bar wajen kowa ya kama gabanmsa, suka cigaba da yada xancan a sasan su. Daren nan su ma Umma basuyi barci ba, musamman Umma da tabbatar wa kanta ciwon xuciya ya kamata. Da safe ta atashi xuru-xuru baki daya idanuwanta sun xurma, shi kansa Abba ya rame ta maxa kawai yakeyi yana wa Umma fada kar ta salwantar da rayuwarta akan Mama. Ita Mama ba wannan ta aje ranta ba, kawau burinta kasance tare da Danliti, don haka take ganin kowa ya tsangwame ta saboda kiyayya. Kafin safiya ma ta mance duk kalaman su Abba da kawunninta. Allah Allah takyi ta sami saukin laulayin safe dake damunta ta lababa taje ta gano Danlitin ta. Xuwa 12noon ta iya shiga kicin, ta dan tsiyayi ruwan lipton, ta dawo ta shanye. Xufa ta keto mata, danji dadi ajikinta, kana ta shiga bayi tayi wanka da sabulun wanki maras kamshi. Ta kimtsa, tsaf, duk da tayi haske sosai, ta kuma rame kwarai, kana iya gane kyanta na asali mai daukar hankali. Ta koma ta kwanta yana kllon agogo 1:00 ta tashi tayo alwala tayi sallah, ta dauko gyalemnta ta xura takalma ta leko falo bataji motsin kowa ba, ta kwahi sauri ta fice abinta. Yara suna ce mata sai kin dawo aunty Mama! Jin haka yasa Umma yanke sallah, ta fito da sauri ta tambayi yaran ina maman? Sukace yanxun ta fita. Tabi xauran, yaran suka biyota ta tura su tace, ku kira min ita. Yara suka fice da gudu suna kwala mata kira, Aunty Mama, ki zo Umma na kira! Haka suke ta gudu suna fadi har suka isketa, ta dube su tace, sai na ci ubanku in kuna kwala min kira haka! Ni sa'ar kuce don Ubanku? Ku tafi ku ban wuri kafin in fallawa yaro mari! Mts..... Taja tsaki, ta wuce abinta, yara suka dawo a guje suka iske Umma a xaure sukace, wai sai ta ci ubanmu idan muka sake kiranta! Ta dafe kirji tace, ta kyauta, kuje wasan ku. Ta dawo cikin gida a salube tare da mamakin taurin kai irin na Mama, me take nufi kenan? Ta xauna a falo tana juyayi. Da kyar ta sake mikewa ta shiga dakin Abba, ta tashe shi barcin ramakon da yakeyi. Ya farka yana kallonta...... Yace, azahar tayi ko? Tace tayi alhaji. Ya yankura ya tashi yace menene na ganki a salube? Tace tasake fita, wa? Mama mana. Cike da mamaki yace ta fita? Yanxun nan kuwa, kamar fako na takeyi, har yaran nasa su kirata, ta dinga kunduma musu xagi, taki dawowa. Ita Maman ta zage su? Tayi murmushin takaici, tace kana mamaki ne? Bai kamata kayi ba alhji. Ta kuwa tafi kenan, kinsa Allah ba zata dawo ckin gidan nan ba. Kiyi hkr, duk abinda ke ranki na so da kaunar Mama, ki cire ki dangana da ita, nima na hkr da ita. Umma ta fasa kuka, ta tashi da asauri ta bar dakin. Hankalin Abba ya kara tashi, ya taso ya biyota dakinta, tana xaune bakin gado kukan kawai takeyi. Ya tsaya kanta, yace saboda Allah ya kike so nayi Halima? Ta cira kai murya na rawa. Tace har ga Allah ba korar Mama ke sanya ni kuka ba, tausayin rayuwarta ke bani, yadda ta ka sa gane cewar mu ba tsangwamarta mukeyi ba, saboda tana son Danliti. Yanxun shikenan ba xata gane cewar alabarkar mu itace kwanciyar hankalinta ba, duk tsananin son da Danliti ke mata, shikenan ta xabi cigaba da xaman shashanci akan ta nutsu, dn tym kankani a daura masu aure? Wannan rayuawar tana cike da tausayi da ban Mamaki, kamar Ya asirce Mama? Ta kada kai ta ciga, ba haka Mamar mu take ba alhji, ta sauya saboda soyayya, kenan ta fi son shi a kanmu? Ina xan samo amsoshin nan Alhji? Ina xan..... Ya rufe bakin da sauri, ya ace ya isa haka! Kar ki jefa kanki damuwar da xata tada miki ciwo, ki kauda kanki ki akan komai, sannan ki nisanta xuciyarki ga irin wadannan tambayoyin da kike wa kanki. Xaki xautu saboda yarinyar da bata damu da lfyarki ba, xamani ne Allah ya kawo mu da yara ke rufe idanuwan su akan abinda suke so. Suyi ta fada da iyeyensu har xuciyoyin iyayen su fara xargin asirce su akayi. Xan ji dadi da farin ciki idan xa'a ce, duk wannan abubuwan da suke faruwa, ki dauke shi amatsayin mafarki mai wucewa, tamkar baki taba haihuwar wata mai suna sakeena ba. Ta dube shi xai yuwu ko? Mai hana? Idan har zaki dage da adduoi, ubangiji ba xai barki haka ba, ta goge hawayenta ta sauke gwauran numfashi tace, xan yi iya kokarina Alhji. Ya jinjina kai. Yace haka nafiso sadiya, kin san ina jin dadin xama dake, kuma tun ina saurayi ban taba son wat 'ya mace ba sai ke. Ban fatan abinda xai salwantar min da rayuwarki, ya kasance wata kaddara tasa kin fara barina cikin duniyar nan. Kullum nayi sallah, sai na roki Allah ya fara daukar raina saboda ba xan iya ganin gawarki ba halima. Idanuwanta suka kara tara hawaye. Tace ka daina fadar maganar nan Alhji..... Ya katse ta, ni ma ba ason raina na fadi ba, domin sirri nane wanda nake xaton shi kdai ne ban taba gaya miki ba, sai yau, dole ce ta sanyani, don ina son ki sami nutsuwa sadiya. Ta matse ido kwallatana suka kwararo ya mika hannu ya goge mata yace, sha kurkuminki Maman abdul 3, gwarazan samarin nan masu takama da baiwar Allah. Ta numfasa tace, Allah yayi masu albarka baki dayansu. Kina nufin har da sakeena ko? Ta amsa da kai, kafin tace, ai mu na mata fatan shiriya ko? Yace haka ne, toh Allah ya shiryta. Amin ta amsa. Haka yayi ta rarrashinta, ta samu nutsuwa, sannan sukayi sallah suma mika kukan su ga Allah. Na san kilan kuyi musu ko mamaki idan nagaya muku Mama bata dawo gida ba, sai bayan sallar magriba. Abu na farko da ta fara cin karo da shi a kofar sasansu dake kulle, shine akwatin kayanta. Taja cak! Ta tsya ta xura masa ido tsawon tym, kana ta matsa ta tura kofar taji ga,! A kulle. Ta tabe baki tare da jan tsaki, ta figi akwatin ta juya tana fadin a ranta, sai aga na kwana a titi. Kai tsaye Danliti ta dosa, yana xaune kofar shagonsa, inda ta basa. Yana hangota da akwati, ya mike ya shige daga ciki yana gayawa Ayuba ga mutuniyar can tafe da akwati, ko maganarta tace ta tabbata? Ayuba ya murtuke fuska yace ni xaka tambaya? Au haushi kaji? Amma dai kana ji na gaya mata kar ta kuskura ta