← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 79

Sashe 29

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

fito aguje da ayuba, mamaki ya rufe ayuba, shi kuwa dan gogan munafuncin ne yasa gaba, sai yazo ya narke a gabanta. Yace, saboda me sakina, kinaso ki rasa ranki ne? Tace gara in mutu da su raba ni da kai, ya dubi Ayuba a gigice. Yace, kawo min mukullin mota ayuba! Ya shige shagon da surinsa, shi kuma ya juyo gunta ya marairaice yake fadin, aure na Allah ne sakeena, ina so ki yarda da wannan. Duk iya son da muke juna idan Allah bai nufi auran mu ba, babu yadda xamuyi. Don me xaki nemi halaka kanki? Bata bashi amsa ba. Ayuba ya mika masa mukulan. Bai jira tace wani abu ba, ya kamo hanninta taso muje asibiti asa miki magani. Dattijon nan ya bisu da kallo, duk tausayi ya rufeshi. Rashin sani kenan, ya fi dare duhu, domin shi gani yake irin haka ke jefa yara yawon banza.. BAKIN CIKI 2***3 (TRUE LIFE STORY) Wasu iyayeyn na da ra'ayin rikau, idan kuma ka bibibya kwadayi ne, wata kila wancan yafi wannan kudi ne? Sai dai kuma ai uban dawaki mutumin kwarai ne, me xai sa ya aikata haka akan yarsa? Duk da cewar dan dattijon nan talaka ne, ya doshi gidan uban dawaki, don ya bashi shawara. Fuskar Umma a sharkaf da hawaye take muryar ta har rawa takeyi, bai kamata ka baro ta can ba abdul... Yaya xanyi umma? Kona cusata cikin, sake fitowa xatayi. Mama ba zata mutu a hannu na ba, umma ta tafi inda take son xuwa, kanta tayi mawa. Fatana kwai Allah ya yaye mata abinda ke damunta. Kuyi hkr ku kyaleta anan domin ina mai tabbatar muku xata xauna can ba dawowa xatayi ba. BAKIN CIKI ya hana abba magana, sai A. Adamu ya iya fadin, gaskiya, gara ta xauna a cigaba da yi mata nasiha watakila a dace. Kuyi hkr Yaya mu dauki wannan a matsayi kaddara. Kai abdul idan ka koma Al-ameen ya kira ka kwantar masa da hankali ka... In ce masa me kawu? Gaskiyya xan gaya masa shi ma ya hkr da ita tunda ba ita kadai bace 'ya mace. Allah xai bashi wata. Ko kuwa? Abba ya dube shi, sai yanxun ya iya cewa, karka gaya masa haka abdul, da yardar Allah sai inda karfina ya kare akan mama. Indai ni na haifeta kuma ni ne xan daura mata aure Insha Allahu shine xai aureta. Kawai ka bashi hkr kayi masa wannan bayanin da naga ya maka yanxun. Ya dafe goshi yayi huci zafi kafin ya dubi Umma. Yace ki share hawayenki, umma ki yi mata addu'a Allah ya shiryata. Ni xan koma sai yadda ta kama. Basu amsa ba, ya mike kawu Basir da Adamu suka yo masa rakiya kuma suna gaya masa kalaman da suka dace ya gayawa Al- ameen. Da dan dattijon nan sukayi kicibis yana sallam cikin xaure suka amsa nan take. Yace baka shaida ni ba ko yaro? Nine wanda yaga lokacin da yarinyar gidan nan ta bude murfin mota ta fito, tayi min bayani ita 'yar mai girma Uban dawaki ce, shine nace ai mai martaba yana da saukin kai xan xo in bashi shawara game da auran dole, yayan ya dube shi da kyau. Yace hakan ta gaya maka? Yace, kwarai hakan ta fada. Yace to tayi maka karya, kawu ka na iya yi masa bayani, don na tabbata abba baxai iya fitowa ba ahalin da yake ciki. Alh. Basiru yace yanxun ina take? Yace tana can ta tsaya wani shago har sun tafi, zai kaita asibiti. Suka dubi juna, yaya yace, kunji ko? Mama ta tafi, bata jin kira saidai addu'ar Allah ya shiryata. Ni na tafi. Ya fice ya barsu nan tsaye. Alh. Basiru ya dubi tsoho yace mun gode baba, amma kayi hkr, bazaka ji komai daga gareni ba, saboda ban sami izinin yin hakan ba. Maganata gaskiyya da nake so ka gane shine karya yarinyar ke maka, tare da shegantaka irin ta yaran yanxun. Mun gode da kulawarka. Tsoho yace, shikenan nima na gode, amma don girman Allah abi a hankali asamu a sulhunta. A. Basiru yace ba komi baba mun gode. Sukayi sallama ya shige gida. Tsho ya kama gabansa cike da wasi-wasi cikin ransa. Falon Uban dawaki A. Basiru ya koma ya xayyane masa labarin da tsho yaxo da shi, da kuma shawarwarin da ya bayar. Abba bai iya cewa komai ba saboda tsabar bacin rai. Sun jima suna tausar xuciyar Abba sannan suka koma sasan su, inda matan suke xaune dirshan suna xuba gulmace gulmace. Suna zagin mama da iyayenta. Basu hanasu ba, hasalima zama sukayi suka dora xancan babu dadin ji, ita kuwa baiwar Allah mama, tana tare da Danliti cikin mota, bayan fitowarsu asibiti, yana ta faman rarrashinta, don ta daina kuka ta kwantar da hankalinta, da kyar ya samu ta nutsu ta daina xubda hawayen. Yayi fakin kofar shagon sa ya juyo ya fuskance ta. Yanxun ya xamuyi mu fuskanci juna abba ya gane cewar idan ba mu auri juna ba, komai zai iya faruwa da mu? Tace, ai ga misali nan na fara nuna masu kuma ba xan fasa ba, ina nan akan baka na. Ya marairaice yace wannan misalin bana son irinsa sakeena, don bana son na rasaki. Gaba ki daya kin fita kamanninki kin kuwa ci abinci yau? Ta kada kai, abinci ba xai iya wuce min ba Dan liti ina cikin wannan masifar meye illar ka? Da abba xai ce samm baka dace dani ba? Ya lumshe ido, ya bude kafin yace, saboda suna ganin ni bako ne, bani da kowa agarin nan..... Ta katse shi, hakan shine xai nuna daga sama ka fado? Wannan ba hujja bace Danliti, son rai ne kawai irin na iyaye ni kuwa ba xan yarda ba, sai dai muyi ta ba juna wahala. Ya ja gwauron numfashi ya sauke, ya lalubo yatsun ta ya runtse su cikin nasa, ya xuba mata ido yace, nasan ki na sona sakeena, amma ki daina damuwa ko sun hana ki xuwa wajena, sannan ki daina wasa da rayuwarki, don tana da muhimmanci aguna. Abu da gaba, ki daina zama da yunwa, ita ma zata iya illata minke. Yaunxu abinda nake so dake, ki zo muje shago in hada miki tea ki sha, sannan kije gida ko sun zage ki, kar ki ce dasu komai, don kar su sami damar dukanki. Kinji bebi na? Ta amsa da ka. Tace, yauwa mai kyau, to dan kalle ni mana, ta dube shi suka yiwa juna xuru, jim kafin ta kauda kai, tana dan murmushi, shima murmushin yayi yana mata kllon kwadayi, ya ja yatsunta xuwa bakinsa ya sumbata. (kuji dan iska). Ta kwace da sauri ta kara sadda kai. Yace, bebi na kenan, sarkin kunya. To muje ko? Zaki iya sauka ko in zo in fito dake? Ta balle murfin batare da tace wani abu ba ta fito, shima yayo waje yana kallon yadda take dingisawa har cikon shagon sa. Ya ba za mata tabarma ta zauna. Ayuba na mata sannu. Akwai wani labule jikin wata kwana a shagon, sai alokacin ta gane daki ne. Cikinsa Dan liti ya shiga ya fito da filas da kofi da cokali ya aje gabanta. Yace ga ruwan zafi, ki daga idonki, ki duba duk irin madarar da kike so, ki zaba na dauko miki. Tana murmushi tace, kai wacce iri kake sha? Yace ai bana shan madara a tea, ganye kawai nake sha. Kinsan buzaye ai? Tayi dariya tace, ba'a raba su da jiko. Yace shayi dai. Ta ciga da dariya tana fadin, to shayi, wai menene sirrin shayin nan ne? Yace xan gaya miki amma da farko wacce madara kika zaba, in dauko miki? Na kowa ki sawa cikinki abinci. Tace, bani peak ta ruwa. Ya mike ya dauko hade da katon bread ya hada mata tea mai kauri, domin duka ya juye peak din. Tana sha, suna hira ya gaya mata ire-iren shayin su. Bayan ta kammala, ya matsa gareta yace, yanxun ya kamata ki koma gida kiyi barci, ki huta kinji? Karki damu ko an hana ki xuwa nan, wane tym zamu hadu. Ke dai kiyi addu'ar fatan samun nasara. Tace, Insha Allahu zanyi. Yana murmushi ya mika baki ya sumbaci kuncinta. Ta sunkuyar da kai tana murza yatsunta. Ya zura mata ido, gaba daya jikinsa yai la'asar, sannan ya dago habarta, suka dubi juna, yace I love U! Tace me too, yace, to ki tashi kije gidan, zaki iya ko? Tace xan iya. Ta yunkura ya taimaka mata mikewa suka fito tare ta sallami Ayuba, ya dan taka mata kadan ya dawo, yana zuwa ya kwashe da dariya, ya mikawa Ayuba hannu suka tafa. Ayuba yace, baka da kyau dan iska. Yace raina kama gayya! Gaskiyya ta gurzu, na tausaya mata wlh. Shegiya akwai taushin fata, baka ji ba kamar auduga, duk ta susuta ni. Ya zura masa ido yace, tunda kuka shiga, na karance ka, shi ya gaba na yayi ta faduwa, kar ka sata labulan nan. Yace, ko na sata ba zata hani ba, nake gaya maka kuma babu abinda zai faru dani. Kawai dai ban yi niyya bane yanxu, ni nasan abinda nake hari. Yace a dai rika tuna Allah Danliti, shagalinka yayi yawa kuma ina ma kwadayin cin ubanta nakeyi, ai har uanxun duniya bata fara zaginta ba. Kaga da sauran mutuncinta. Ya bishi da kallo, bai ce komai ba, yayi tsaki ya tashi ya koma shago abinsa. Tana tafe tana dingishi, ta iso gida, kanta tsaye bata fargabar komai ta fada zaure, kicibus suka yi da Ya Ali sabe da jakar sa zai bar garin. Ko kallon sa batayi ba ta wuce, ya biyota yana kiranta bata waigo ba, balle ta amsa, ta shiga sasan su har falo yana binta. Su abba na kallon ikon Allah, domin dai Mama bata saurara ba, cikin dakinta ta shige. Ya Ali na shigowa ya gansu, ya ja birki amma ransa na son ya shiga wajen mama, yayi magana da ita, abba ya dube shi. Yace, Ali ka daina wahalar da kanka abanza, mama bata bukatar komai sai addu'a. Saboda haka ka kama hanyarka ka koma bakin aikinka. To amma, kayi hkr Abba, don girman Allah karku daketa, kamar yadda kace nayi mata addu'a
Chapter 29 · 0% Book details