Sashe 40
Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
BAKIN CIKI 2***9 Abba bai ga ta zama ba, 7:30 suka kama hanyar minna shida Alh. Adamu tare da Umma, domin ita tana bukatar ganin likita. Saboda ha ane aka tafi da Inna saude don ta rinka taimaka mata. Basu iske abdulkareem a gida ba, ya riga ya fita aiki. Hankalin Aunty Rabi ya dugunxuma nan da nan ta dauki waya ta kita wayar ofis dince, Yaya abdul yaji kamar zai mutu, saboda tsabar bacin rai, amma ba yadda zaiyi ya fito saboda tsarin aiki irin na banki. Daga nana aunty amina ta kira, itama ta shaida mata, kafin ayi haka labari ya gauraye ko'ina. Asibiti suka fara aje Umma tare da inna saude. Aunty Rabi itace jagora domin asibitin da banki ke da reg da su ne. Daga can da Abba da alh. Adamu suka dumfari gidan marafa. Da ganin su, gaban Mami ya fadi, fara'ar karfin hali kawai takeyi. Bayan su natsu a falo. Abba ya tambayi marafa? Tace, ai kuwa yayi sammako ya tafi Lafai, don shaidawa mutannan gida maganar daurin auren, shi kuwa ango na san ya ma kai zariya yanxun Insha Allahu. Kasan a can yawancin abokansa suke saboda can yayi krt. Ina fatan lfya? Ya sauke numfashi idanuwan sa suka kara juyewa yace, babu lfya Hjya, Ki Innalillahi Wa inna ilaihir raji'un! Alh. Adamu ya gaya mata. Ya gayara xama, yace hajiya wannnan al'amari babu dadin ji, a takaice dai sakeena ta gudu tun jiya har yanxu ba mu san inda take ba. Tsaye ta mike dafe da kirji, ta yi me? Ta kame a hakan bata iya kara komai ba. Abba yace, nayi iya yina Hajiya, amma mama ta nuna min ta karfina, hanyar da zabarwa kanta ta wuce da sani nan. Kuyi hkr hajiya, ni ban ma san da kalmar da xan gaya maku ba. Ta koma a hankali ta zauna cikin kasala tace, ai shikenan, duk abinda Allah yayi daidai ne, mu mun hkr, Allah ya musanya wa Al- ameen da mafi alkhairi, sukayi ji. Shiru kafin Abba yace mu na nan garin nasan har Alhji ya dawo. Itama hajiya tana nan na kawo ta asibiti tun jiya ciwon ta ya tashi abin sai yadda Allah yayi. Ta maida tagumi tace, dole Umma tayi ciwo, ubangiji Allah ya bata sauki ya kuma shirya mana zuri'a, suka amsa amin. Suka mike sukayi mata sallama suka tafi. Hawaye suka kubcewa mami, hannunta a kunci tace, ta faru ta kare kowa sai ya hkr! Tab, wannan yarinya ta daure min kai. Allah kayiwa Al-ameen sakayya! Iya da ladi suka jiyo hajiya na sambatu, suka fito suka taushi xuciyarta, babu bata tym ta sa driver ya kaita Lafai. Gado aka ba Umma, saboda yanayin jikin nata, yana bukatar kulawar likita sosai domin jininta ya hau, har ya haye yadda ko alama ba 'a so. Anan su abba suka ci gaba da zama har karfe 4. Yaya abdulkrm ya samu ya baro ofis. Kai tsayr asibitin ya nufa a sukwane. Da ka dube shi, kasan ransa a nbace yake, yana ganin Umma kuma al'amarin ya kara gigita shi. Ya dubi Abba ido jajur! Yace, yanxun wane mataki aka dauka? Abba yace, ni na sallama mama, tunda ta iya toazarta ni haka. Na kuma je gidan su Al-ameen, matslar kawai ban same su bam duk sun tafi raba goron gayyata, sai hajiya na samu shaida mata. Alh. Adamu yace amma ni ina ganin zai fi kyau abada cigiyar a gidajen Radio da Tv. Abba ya amshe, da kudin wa? Saceta akayi? Ba xan kara asara ba, yadda ta sa kafa ta bar gidana, ta tozarta ni, ta wulaknata ni, ta nuna min ban isa da ita ba. Wlh ni ma na hkr da ita. Ba xan yi mata baki ba, dan ko bance wani abu, tabbas ita da kanta ta kai kanta mkrntar koyo hankali. Za ku ce na gaya maku. Taje duniya cem ta ishi kowa riga da wando har da mayafin yafawa. Ya abdulkrm ya numfasa, yace ta yiwa knata, Allah ya shiryar da ita, yasa ta gane, suka amsa da amin. Jimawa kadan ya ba Aunty Rabi mukullin mota ta wuce dauko su Ameera daga sch. Kai tsaye ta wuce da su gida. Ta kama hidimar shirya abinci. Tana gamawa ta kwashe gaba daya da yaran suka koma asibiti. Ta iske kofar dkin da Umma take dankam! Da Jam'a, ashe bayan tafiyarta kadan su ya Abdul kadir da abdulrhmn suka iso. Can kuma sai ga dady da mami. Al-ameen ne kadai bai dawo ba. Duk tabisu ta gaida su. Dady kam yama rasa yadda xai fassara al'amarin Allah ya sa bai riga ya yayyada xancen ba ko 'ina, iyakar sa cikin babban gidansu. Allah ya kawo Mami tayi masa birki. Shi kansa yadda yakeji a tym din, idan xa'a gwada jininsa dole ace ya hau, amma daya iso ya dubi halin da iyayen Mama ke ciki sai yaga ashe shi nafila ne, tashin hankali na inda yake. Shi yasa ya nutsu sukayi magana ta fahimta da abba...... Ya Dubi halin da Iyayen Mama ke ciki sai ya ga ashe shi nafila ne, tashin hankali na inda yake. Shi yasa ya nutsu sukayi magana ta fahimta da Abba. Suka dauki komai suka barwa Allah tare da rokon Abba daya amince ya bawa mama wanda ta sake xaba. Abba bai ce komai ba anan. Don baya jin zai iya ba Danliti 'yarsa su hada zuri'a da mutuncin sa da komai a gari. Yanxun tunaninsu dan gogan. Yaya al'amarain zai kasance? Bayan abba ya kauda masa duk wani shakku, ya bashi tabbacin babu wani face shi, shi ya kara karfafa masa gwiuwa har ya sami kafar tafiya gayyato abokan taya shi murnar angwanci? Wannan amsa sai wanda ya gani da idanuwansa. Gab! Da kiran sallah magriba duk suka bar asibitin, aka bar Inna saude ita kadai tare da Umman, wacce har yanxun barci takeyi, domin allurar da akayi mata mai karfi ce sosai, saboda ana son ta samu hutu kwarai da gaske. Su dady na isa gida, kamar tare suke da Al-ameen. Bai fhimci komai a fuskokinsu ba, don basu yarda yaga sauyi ba ya baje a kujera yace, wsh! Ai fah an fara kenanm kinji yadda naga ji Mami? Ta danyi murmushi tace, dan Iya kena, to abinda ya kamata ka hanzarta yin wanke ne, don gab ake da kiran magriba. Haka za'ayi Mami na, dadi ya aka baro mutanan Lafai? Ina fatan zaka jaddada musu su taso da wuri? Wannan ai dole ne, kama san kawunka ba shi da wasa. Yana ta far'a gaskiyya ne ni ma frnds dina ne ce masu kai tsaye su wuce Fandagori, ai gidan Uban dawaki ba boyayye bane, suna tambaya za'a nunna masu. Dadi yace, kayi daidai, yanxun tashi ka shiga wankan nnima shi xanyi aga wanda xai riga fitowa cin abinci. Ya mike xumbur! Yana dariya ni ne xan riga Dadi, to shikenan, mami ki na ji ko? Idan kuma na riga shi bulala tara, tace ni kuma xan cikashe dayar, su zama goma. Na yada. Bai jira komai ba ya kwasa da gudu, ya shige bangarensa. Mami ta bishi da kallo. Dadi ya sa hannu ya cire mata tagumi yace, ke ma tashi ki daina damuwa. Ta sauke numfashi, amma ba tace komai ba, ta yunkura ya taimaka mata ta tashi suka wuce. Kowa ya shige dakinsa. Al- ameen ya fara fitowa falon, ya nufi gefen tebur inda ya hangi ladi na jera abinci. Ya isa wajen yana fadin, angaida Maman abinci. Tayi dan murmushi. Tace ni ma na gaida dr. Yace na kusa dina cin abincinki Ladi, ina ganin daga yau nai masa bye bye. Tayi 'yar dariya, to aci gaba ne dr. Amma ina ganin akwai gobe kafin amaryar ta iso ko? Ya gyada kai, yana dan murmushi, wa ya gaya miki xan dawo ni kadai? Tana 'yar dariya ta amsa, au can xaka zauna? Kafata, kafarta, zata sake magana, ya dakatar da ita, shisshhh... Tayi tsit! Tana kallon sa yana boyewa bayan kujeru. Dadi ya fito mami na biye dashi, madalla, kinga bulala ta hau kan danki, kira shi na tsatstsala masa. Tace, yanxunn nan ma xaka ganshi a sukwane, kwai ganin sa sukayi yana gyara xaman kujera xai xauna. Gaba daya suka kwashe da dariya. Ladi na tasya su sannan ta bar wajen. Dady yace, gaskiyya ba haka ake yi ba, ai dai sai ya bari mu fito tare ko mami? Dariyar Al-ameen ta karu, yayin da Mami ke fadun, kaji wayau! Ta xuba wa kowa abinci yaci, suka kashi suna ta biye masa, suna labarin biki. Bukatarsu ya cika cikinsa, kuma ya ci sosai. Bayan su kammala Dady ne ya fara barin tebur din Al-ameen ya byi shi xasu yi wata magana, nan da nan ya mike ya bi bayansa. Mami ta kwala wa Ladi kira tace ta gyara kan tebur din, ita ma kai tsaye ta wuce, ta iske su xaune bisa kafet. Dayan gefen ta xauna, suka sanya shi tsakiya. Dadi yayi gyarn murya yace, wasu 'yan tamnbayoyi xan yi maka Al- ameen, ina fatan xaka nutsu ka bani amsa shakikiya. Da farko dai shin Al-ameen wa yake badawa, wa yake hanawa? Yace, Allah. To idan ya baka, sannan ya dawo ya karba, me yakamata kayi? Ya amsa, nayi masa gdya, watakila ya musanya min da alkhairi, ko Mami? Tace, Gaskiyya ne! Dadi yace, Madalla, abinda nake ka sanya wa ranka kenan. Idan har ka tabbata tsakanin ka da Allah ka amsa min tambayoyi na. Ka kuma san imani shine cikar dan musulmi, ko ba haka ba? A salube yace, sosai dady. Yauwa, to kayi hkr maganar da xan gaya maka. Nasan ka na son sakeena, sannan kayi imani Allah ne ya hadu ku ya sanya maka sonta, a da mu na ganin kamar itama tana sonka, kamar yarda kake sonta. Amma yanxun ta nuna yaudara ce kawai, saboda haka ka hkr da ita. Kamar yadda kace Allah xai musanya maka alkhairi. Ya dubi Mami, ya juya ya dube shi, Dady ban fahimce ka ba, ai sakeena na so na, xuga ce kawai kuma na tabbata da xarar aka daura auranmu, ni masan yadda xan da hankalinta gareni. Dady ya ka kada kai, maganar ka dawo da hankalinta gareka duk