← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 79

Sashe 44

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ganin aika aikar da ta aikata a garemu, ya cire kai ya dube ta ni kuwa hakan na fi so gwaggo domin na yi imanin ba yin kanta bane sace min ita akayi hure mata kunne akayi da kalmomin shaidan addu'a zatayi maganin abin, da zaki taimake ni da ita ma zan fi farin ciki akan wadannan labaran da ki ke son bani," gwaggo " mami ta karbe za a yi maka in dai addu'a ce ka samu tashi kaje kaci gaba da shirinka bai tofa komai ba ya yunkura ya bar dakin,kamar daman can ya kosa ya barshi,"gwaggo ta dubi mami hankali tashe tace bai kamata ku kyale yaron nan ya koma haka kawai ba tare da wani taimako ba tace tun jiya na je lafai na samo masa wajan baba liman wai nan yama sha ruwan addu'ar ke nan tafdijan ki na kallo fa ko laifinta baya son a fadi wannan so yayi yawa gara ma da auran bai yuwu ba da muna kallo zai zama mijin ta ce,abin haushi nama na jan kare, mami tace me ki ka gani gwaggo?ALLAH dai ya zaba alkairi abin cewa ke nan anan gwaggo ta wuni, Shi kuwa Alameen a dakinsa ya wuni don baya son ana daga masa hankali da labaran sakkena kazantar da baka gani ba tsafta ce,kai a yadda yake jin mama cikin ransa koda ya ga kazantar da idanuwansa zuciyarsa ba za ta amince masa ba bai fito ba sai da gwaggo zata koma suka yi sallama daga nan dakin iya ya shige ya kudundune kamar maraya sama da awa guda tana tausar zuciyar sa da kalamai masu dadi,ya kuwa ji dadin cikin ransa saboda kalaman iya sunfi rinjaye ga. Bashi tabbacin idan sakeena matarsa ce duk rintsi duk wuya sai ya aure ta karfe shidda dai dai dady ya dawo masa da takardun tafiyarsa sun kammalu kuma gobe da yardar ALLAH sha biyu ranan zasu tashi don haka yana gama cin abincin dare mami ta ba shi ruwan addu'a ya kwankwada kai tsaye asibiti ya wuce don yin sallama dasu abba,kowa yayi masa nasiha kuma sun jaddada masa ya maida hankalinsa akan anibda ya kaishi kar ya tsaya bata lokacinsa. Akan tunanin iska wanda ba zai fisheshi ba,sai dai abin yana basu mamaki yadda lafuzzan alameen ke nuni da tsantsan son mama a zuciyarsa. Wanda ko alama na bayyana har yanzu bai yarda sakeena. Taci amanarsa ba, akwai mishkila wani wuri shiyasa yake ta rokansu dasu taya shi addu'a ALLAH yasa wata rana sakeena ra zama mata a gare shi,gaba daya ya kwabe masu guiwa har suka yi masa alkawarin yin yafiya a gareta idan har ta dawo ta nemi gafara,kowa ya dubi alameen sai ya ji tarin kwalla cikin iadanuwansa lokacin da yake barin asibitin yana gugar fuska shi kansa yaya soja a yau zuciyarsa ta karaya,tausayi ya kwarara cikin jikinsa ya nemi haddasa masa abin mamaki domin kwalla ya ji tam da idanuwansa suna zubowa da saurinsa ya bar wajan bai gama ganin wucewar alameen ba AKIN CIKI 2*** 11 Karfe 8am suka dauki hanyar abj tare da mami. Hankalinsu bai gama tashi ba, sai da tym ya cika aka kira passengers. Al- ameen ya rungume su, idanuwan sa cike da hawaye, bakinsa na son yin magana amma kasa, haka su ma Allah ya doro masu nauyin baki, kallon juna sukeyi. Da sauri ya juya ya wuce, yana goge fuska da hankici. Shi yasa suke tafe cikin mota kowa shiru. Mami dauke da taguminta. Tunaninta yay rayuwar dan nata xata kasance a kasar da babu wanda ya damu da wani balle ya sami wata kulawa ta musamman. Dadi yayi tana share hawaye ya dan dube ta, kada kai. Amma bai iya cewa komai ba don ya san mami tana mukatar zubda hawaye ko ta ji dadi cikin ranta, amma da ya ga abin yaki karewa, dole ya tanka, ina ganin bai dace ki ci gaba da bata ranki ba, wanda kika yi ai ya isa, ko sai ya jefa ki wani hali ni in rasa da wanda xanji? Ta goge kwalla, tace Alh. Ba haka bane ganin Al-ameen na da abin fadi, amma yakasa ya wuce da damuwar cikin ransa? Wa zai gaya mawa a can? Kai tsaye ya bata amsa, Allah zai gaya mawa, kin kuwa san ya fini, ya fiki, yafi duk wanda kike tunani zai ba Al-ameen wanni taimako, saboda haka ki bar shi da buwayin sarki, shine xai masa dukkan gudunmawa. Ta zare tagumi ta numfasa, haka ne, Allah ya taimake shi, to amin kuma na tabbatar zai taimakeni shin, tunda kika furta, addu'ar uwar yankan wuka ne, don haka ki kwantar da hankalinki. Ina fatan kin ji ni. Tace, naji alh. Allah ya shige mana gaba, yace amin. Daga nan Mami ta saki jikinta suka ci gaba da hira. Suna shigowa gari, asibiti suka wuce gano jikin Umma. Alhmdlh, Umma na samun sauki, watakila ma xuwa gobe a sallameta. Ba su iske yaya abdulkadeer da Abdul- rahman ba, duk sun koma a wannan yammacin. Sun dan jima asibitin, sannan suka dawo gida. Mami ta dukufa rokon Allah cikin sallolinta, Allah ya sanyaya wa Al-ameen xuciyarsa, ya cire masa wannan makahon so sa ya ke wa Mama. Haka ta kwana tunaninsa har barci tayi mafarkinsa xaune yana wasa da xobunan guda 2. Shiyasa da ta fara tayi ta da na sanin da ta raba shi da zobunan kafin ya tafi. Suna karin safe karfe 8:30, waya ta dauki kuka, mami ta baro tebur ta zo duka tayi sallama. Muryar dan lelenta taji ya amsa. Farin ciki ya lallube ta tace, Allah sarki Dr. An sauka lfya? Yace lfya lau Mami, ina dadina? Ga shi nan, ya taso ya ji kaini, ina fatan ba matsala? Babu mami, na ma iske time table din jarabawar mu ya fito, karatu kawai xa mu fuskanta, ni da abokan karatuna. Dadi ya tsaya wajen tana fadin, kai naji dadi sosai, to Allah ya baku sa'a baki daya. Ga dadinka. Ya ce, to nagode Mami. Dadi ya amsa suka gaisa. Dady time table ya fito a taya mu addu'a. Yace kullum a cikinta muke, amma xa mu kara kaimi. Ubangiji Allah ya taimako. Yace amin. To xan wuce cikin sch, sai kun sake jina. Yace, yayi kyau, all d bst! Cike da fara'a ya amsa. Nagode Dadina. Ya aje waya ya dubi mami yace hankalinki ya kwanta? Bakinta har kunne ta amsa. Kai bari Allah ya kara masa hkr. Yace amin, muje muci abinci ko? Suka koma tebur. Mami tace abinci hankalinta kwance. Ba Haka al'amarin yake wajensu Umma ba, domin yau sun koma Fandagori sun iske da kuara da suka bari baya. Hankulansu su kara tashi yadda xance ke ta yamadidi a agari. Zagi iri-iri babi irn wanda ba'ayi ba wasu suna ba iyayen Mama laifi, amma da dama sunfi zargin mama akan rashin hankali da ta aikata. Wani abinda yafi daga wa Ubandawaki hankali shine, wai gaba daya gundarin labarin daga bakin 'yan uwansa da matayensu ya fara fitowa. Bayan gaskiyya ga tarin karya da karairayin da suka yiwa labarin kawanya, don haka ya tara su falon sa bayan sallar isha'i. Wannan shine karo na 2 da na tara ku akan wasu maganganu na batanci da suke fitowa daga gareku. A zatona ku masu rufa min asiri ne ko bayan raina a matsayin ku na 'yan uwana da muka fito ciki daya. Amma bansan abinda nayi muku ba kuke min bita da kulli, ko kuma ince kuke farinciki don wannan abin ya sameni. To abinda nake so ku gane shine, da frko dai bamu mukayi kanmu ba. Allah ne yayi mu, mu kuma shi ya rubuta duk abinda zai faru da mu. Babu wanda yasan kaddarar mu2m bnalle ya share masa mummuna kafin tazo. Da anayi da na gogewa Mama, don na duk fadin duniyar babu wanda zai kaini BAKIN CIKI, sai kuwa mahaifyar ta. Idan kuwa hakane, bai kamata ace ku da matayenku, ku dauki wannan al'amarin ya zamar maku abin hira a gari ba. Kaddara na kowa, idan baku duba kusancin mu ba, ya kamata ku duba wannan. Allah yai sani ban zalunci kowa ba cikin ku ba, haka ban xalunci mama ba, kamar yadda kuke yadawa cewar mu ne muka dage sai mai kudi xata aura, alhalin kun san komai a game da alkawarin auran ta da Al-ameen. Kun fi kowa sanin gaskiyya, amma kuka boye ta, saboda son rai to na bar kowa da Allah, yayi min sakayya, Da yardar Allah BAKIN CIKIN Mama bazai kashe mu ba, haka zalika ina mata fatana shiriyar koda yaushe. Mai surutu da dariya kuma Allah ya bashi sa'ar yi. Amma kar ya mance kaddara bata fatan shiryar kowa! Yana sa aya, ya mike ya bar falon ba tare da wani yayi magana ba, ita ma umma tashi tayi ta bi bayansa, yayi sauran ke mazuran rashin gaskiya. Haj. Gaje ta buga tsaki, ta bar falon. Daga bisani Haj. Hajjo ta lallaba ta sulale, Alh. Basiru ya dubi Alh. Adamu. Yace mutane munafukai ne, wai daga dawowarsa, an sami wani kusugurmin ya feshe shi, don neman fada. Alh. Adam yace, wai me akace? Au ya faru ba za'a maida yadda akayi ba? Me za'a baoye bayan ta gudun kowa kuma ya sani tare da shegen yaron nan suka tafi! Ai ko ba 'a fada ba, amsar a bayyane take. Tace, bata so, ba sai a kyale ta ba, ta auri dan iskan da ake ganin ba shi da asali ba, ba ita zata zauna da shi ba? Wahalar tace tunda tasan halinsa. Tace sai shi. Wai kuma mu ake ganin laifin mu, don fin karfi! Mts.... Ya ja tsaki yayi waje abin sa. Alh. Basiru ya mike yana kada kai, shi ma ya fice. Zaman doya da maja yaci gaba da yaduwa cikin gidan, duk da ba gaba daya sukeyi ba, amma babu wata kyakkaywar fahimta atsakninsu. Shi uban dawaki yana ganin ya kamata su ba shi hkr a matsayinsa na babban su, sannan yana gani sun yi masa laifi, don sun bada labarin yadda akayi mama ta gudu, tunda ba su suka xuga ta ba, komai ya kwana gidan sauki saboda haka basu ga dalilin da xai sa Uban dawaki Ya dauki dalan
Chapter 44 · 0% Book details