Sashe 39
Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
dafin da xai wuya na sami maganinsa. Xan iya mutuwa Gambo, domin gaba daya na sallama kaina gareta. Ko kasan inda nake da mishkila ka gaya min in gyara? Gaba daya tausayin sa ya lullube gambo, ya kada kai da sauri, yace babu inda kake da mishkila Yallabai, sai dai ko ajizanci na dan adam. Ni kaina ban yarda sakeena bata sonka ba, watakila ciwo ne rudata yace, kai ma ka yarda bata da lfya ko? Amma kowa yace kalau take, ni nasan sakeena bazata ki ni haka kawai ba, zuciya na wasi-wasi. Gambo yace , kar ka damu Yallabai, Allah zai warware komai, sakeena zata zama matarka. Ya sauke numfashi mai karfi yace, wannan shine babban burina a duniya, komai Allah ya bani na gode masa, saura wannan burin ya rage min. Shima zaka sameshi Insha Allahu. Yayi dan shiru, sannan ya kada kai yace, laifi nane, rashin kasancewa ta kusa da sakeena, shi ya jawo shaidani ya shiga tsakanin mu. Lallai mata na da rauni Gambo, ba taba tunanin sakeena zata iya hango wani har ya rikita ta amince dukkan amanar da muka damka ma juna. Al'amarin na daure min kai, na rasa yadda xan fassara shi. Yace, haka ne yallabai, amma idan ka barwa Allah komi na tabbata xai maka zabin alkhairi. Ka sani ko wata jarabawa ce Ubangiji yake yi ma don ya gwada imanin ka. Kar ka damu Yallabai, Allah ba zai hana ka sakeena ba, idan har kayi imani shine mai hanawa da badawa. Ya sake jingina da kujera, ya runtse ido ka fadi gaskiyya Gambo, na gode. Bai sake tankaea ba haka kuma bai daina tunanin xuci ba, ma'ana sakeena bata daina xuwa cikin idanuwan sa dauke da lallausan murmushinta mai sanyaya masa rai, tana tura hularasa gaban goshi bakinta na fadin, so much! Shi ya sa baya aikin komai face ajiya xuciya. Gambo na jinsa tausayinsa nakara zama cikin ransa. Karfe daya dai-dai na dare motarsu na tsayuwa kofar gate din gidansu. Gambo yayi hon, nan da nan Mai gadi ya shaida hon din motar mami ne, ya taso a guje ya bude kofar, motar ta shige kai tsaye kofar shiga ya tsaya. Al-ameen ya fito, sannan ya wuce ma'ajiya motaci. Tun kafin ya kwankwasa, yaji ana kokarin budewa, don haka ya dakata hannayensa biyu cikin aljihu. Marafa ne da kansa ya bude kofar, suka zuba juna ido, daga bisani ne mami ta bayyana wajen har ta riga marafa magana, Al- ameen . Idanuwansa suka yi tam da kwalla, ta yi azama ta jawo shi ciki, daddynsa ya maida kofar ya rufe. Don me ka iyo daren nan Al-ameen? Sai kace babu inda zaka raba ka kwana! Ya zauna dabas! Ya kama hannaye biyu, Marafa ya xauna kusa shi. Ya rungumo kafadunsa, yace baka kyauta min ba Al-ameen, da ka dauko hanya cikin daren nan dan kuskure kadan za'asamu, shikenan ka ajwo mana tashin hankali, karfa ka manta, kai ke nan guda daya muke kallo zukatan mu na wankewa daga radadin rashin da. Ya dube shi ido jajur! Yayin da Mami itama ta xauna daya gefen suka sanya shi tsakiya. Yace, na kosa in ganka Dady, sakon Abba xan gaya maka, yace gobe yana nan tafe maganar aure na sakeena, kafin in koma yake so a daura shi. Mami tace, kun daidaita da sakeenar ne? Ya dan kada kai yace, sakeena ba warke ba Mami, hasalima bata gane ni ba, shiyasa tun farko nace a kaita asibiti, kowa yaki amincea da ni, ga shi nan kwakwalwarta ta tabu. Sakeena ta kasa ganeni Mami, ni kuma bazan fasa auran ta ba, domin shine babban buri na a duniya. Su abba sun goya min baya, kuma ku taimaka min buri na ya cika don girman Allah. Gaba daya ya kara daga musu hankali babu kamar Marafa da ko alama baya kaunar yaga dansa na kukan neman wani abu, shi yasa nan take ya ji ko ana ba maza ha mata, sai Al-ameen ya auri mama. Amma ita Mami bata an ta dosa ba, don haka tace. Al-ameen bania ron hankalin kanan, na ga alama baka yarda Sakeena lfy lau take ba.... Ku kuka gaya min ai Mami... Yanxun kuma ni na gaya maka lfya, kawai cin amanar ka tayi, tunda kaje bata saurare ka ba, kai ma ka manta da ita kawai, ka roki Allah ya musanya maka da mafi alkahiri. Bafa sakeena kadai ce ta yalwatu da dukkan abubuwan da kake so ba. Saboda haka ka kama kanka, ka nutsu ka gane cewa ko an daura auran, ba zaku zauna lfya ba, tunda idon ta ya bude, tana takamar tana da kyau, kowa na kallonta, kajini? Ya girgiza kai, idonsa xuru yana kallonta, tace au baka ji ni ba? Menene nufinka? Marafa ya amshe don Allah, don Annabi ki kyale shi, ba yace Uban dawaki na taf ba? Allah ya kaimu goben lfya, shi aure ai nufi ne na Allah. Yanun kaje ka kwanta mu saurari goben, kaji? Yace naji dady, don Allah ku tayni da addu'a sakeena kadai nake so. Yace na sani, addua kuwa kullum munayi, kayi alwala ka sami koda raka'a 2 ne kafin ka kwanta, na tabbata zaka sami nutsuwa ok? Ya amsa da kai ya dan bubbuga kafadarsa yace, yau dan Dady, Allah ya bamu alkhairi. Bai dai tanka ba, ya mike ya bar falon. Mami ta cire tagumi tace, sai Allah yayi wa yaron nan sakayya! Yadda tai masa haka Allah zai mata. In banda idon Al-ameen ya rufe a kanta, me zaici da ita? Yarinyar da gwaggo tace shagon saurayi take su raba dare suna.... Marafa ya katse ta, don son Annabi, ki bar wannan magana haba. Ki yi masa fatan alkkhairi kawai. Cikin bacin rai ta mike ta koma daki. BAKIN CIKI kamar ya kasheta. Shi kuwa Al-ameen yana can yana nafilfili kamar yadda dadinsa ya umarce shi. Da safe ya fito gaba daya ya zabge, kallo daya za kai masa ka tabbatar da hakan. Gaban mami ya fadi ta kwala wa Ladi kira ta zo a gigice. Tace, to hajiya. Ta juya da sauri ta fice. Mami ta dube shi tace, matso nan kusa da ni. Ya kara matsowa yace, ina kwana? Ta amsa tana shafar kansa. Ina dadina, bai tashi bane? Tace, kwana yayi baiyi barci ba, sai bayan sallahr asuba barcin ya sace shi. Tana rufe baki ladi na sallama da tiran abinci ta dire gabansu. Tace ga shi hajiya dr, Iya tace in gaida ka, yanxun xata shigo. Yace ina amsawa. Ta fita ta bar dakin. Mami ta jawo tiren ta hada masu shayi ta mika masa, ungo nan dan iya. Daute ka sha kaji karfin jikinka. Ya sanya kofi a baki ya kurba kadan. Wlh daci mami ba xan iya sha ba. Tace don me? Ka cigaba da sha za kaji bakin ya washe. Ga kuma farfesun, bude bakin in xuba maka. Ya bude 'yar kular ta debo a cokali ta mika masa, karbi ka gani mana. Ya bude bakin ta xuba masa tace, yauwa ko kai fah? Yanxun idan Abba ya zo maganar auranta kankama, haka za'a ga ango a rame? Dadi ya lullubeshi yayi wani lallausan murmushi yace, mami na rame ko? Kai baka ji ajikin ka ba? Bana so kayi angwanci a rame, don haka ma za ka kama abinci ka ci. Nan da nan ta ga ya gyara zama ya hau shan farfesu yana kurban shayi, kinsan wani abu Mami? Sai ka fadi, shayin nan ya daian min daci. To yi sauri ka shannye. Ya kuraba ya sake kallonta, yanxu Mami idan aka daura auran anan xan barta? Eh mana, ko ba xan iya kula da ita bane? Yayi dan murmushi, a'a mami na, amma ni na fison mu tafi tare can, kin ga kafin mu dawo ta mance da sakaran Yaron da ya hure mata kunne. Ko ma muyi xaman mu can tana karatunta ina aiki na, ko kuwa? Ta dafa kafadarsa, gaskiyya ne, ina goyan bayanka, sai dai in ta haihu ka kawo min maigida ko kishiya. Ya kyalkyale da dariya, kwalla suka cika idanuwan mami ta bisi da kallo tana gyada kai. Yayi gyatsa kafin yace, ina son twins mami, ko? Sai dai an mai son su baya samun su? Da sauki ya katse ta, no duk canfi ne Mami, ni dai ina so kuma Allah xai bani ameer da ameera. Tayi 'yar dariya tace, duk naji, idan ma 'yan hudu ne Allah ya kawo masu albarka, yanxun tunda ka koshi, kaje ka yi wanka kafin dadin ka ya tashi. Xai ji dadi idan ya ga ango shar! Yace haka ne mamina. Ina xuwa, ya tashi da sauri ya fice. Mami ta ta tallafe kunci ta ce nikam tawa.... Nikam tawa ta sameni, ni Ya su, Allah ka duba mana. A bakin kofa suka hadu da iya suka gaisa. Sannan ya wuce bangarens, ya fada bayi ya sheko wanka, ya kimtsa jikinsa da wani lafiyayyen farin boyel mai taushin gaske. Ya fesa turare, ya dawo dakin Mami, ita ma wanka yi ta sauya kaya. Ta dube shi tana fara'a tace, haba yanxu na ga daidai. Ina ganin ma dai daga yau aka angwancin nan. Ya xauna kusa da ita yana dariya. Tsokanata kike sonyi Mami, me kika gani yanxun? Sai ma ranar kenan. Ki gane Mamina, ranar ba zaki shaida ni ba. Ta ware ido tana 'yar dariya zai hana? Sai dai ko amarya ta kasa shaida kai, amma ina mami zata mance da dan tilon dan ta. Dadi ya kara lullube shi, ya rungumo ta yana fadin Allah sarki mamina, Allah ya bar min ke tare da Dady na. Dadin ne kansa ya amsa, amin amin. Ya kara sa shigowa suna masuayar fara'a. Dadyna ya tashi lfya? Na tashi lfy Doktna. Suka gaishe shi cikin annushuwa, duk da bai san sirrin ba, xuciyarsa tayi masa dadi. Don haka ya xauna aka kawo masa abincinsa su ka fara ci tare suna kara kwantar masa da hankalin. Sosai kuwa hankalinsa ya kwanta, yana ganin tamkar an daura auransa da mama, tunda yana da magoya baya ta kowanne bangare