← Book details Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 79

Sashe 55

Baqin Ciki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

bari su koreta, don bani da wurin ajeta, ko ban gaya mata ba? Yace oho! Wai kai wani irin banxa ne? Yace Ni banxa bane, ai rainin wayau yasa ka gaya mata hakan. Wa ke jan ragamar rayuawarta, in ba kai ba? Ai sanin bata da xabi shi yasa ka raina mata hankali. To ya isa malam, sai gata tsaye gaban kanta, tana kokarin dagawa, duk suka xubo mata ido, ta karasa shigowa, ido waje ya dubi shirgegen akwatin, ya ce ya dai? Bata saurare shi ba, kofar dakin ta tasarmawa xata shige. Yayi azama ya shawo gabanta, magana fa nake yi, kona kokarin shigewa kamar gidanku? Ta xubo masa ido a marairaice tace, me na gaya maka? Ni kuma me na gaya miki? To yaya xanyi? Ina komawa na iske akwatina akofar gida sun kulle gidansu. Ya gayara tsayuwa, da yake kuma ke sakarya ce sai kaka kamo hanya kika taho baki tsaya kika nemi sulhu ba! Yanxun menene nufinki? Anan xaki xauna? Cikin shago? Lallai kin cika dakikiya, Jaka! Kuka sosai ya kwace mata, ta tsugunna ta rungumi kafafwansa, murya na rawa tana fadin, karkayi min Haka Danliti! Saboda kai suka koreni, ina kake so naje, idan ba nan ba? BAKIN CIKI 2***15 Ayuba ya daga kanta, ya fice hankalinsa tashe, shi kuwa ko gezau beji ba ajikinsa, a dage yake kallonta, tsawan tym sannan ya fizge kafarsa ya kama hanya xai fita, da sauri ta mike ta cukuikuyo rigarsa, fadi take, kayi hrk don girman Allah. Wasu samari 2 suka iso wajen siyen taba sigari, ai sai suka buge da shari'a, kaya-kaya hayaniya har waje Danliti na daga murya shi ba xai aje ta cikin shagonwa ba, ta koma ta nemi sulhu da iayeynta. Kan ka ce kwabo jama'a sun cika makil a gun. Kai Mama ta sha zagi da la'anta, Allah shi kara kwando- kwando. Kalilan ke cewa Allah ya shiryeta, Dan liti ya gacciye banci kofar shagoin ya xauna yace yaga uban da ya tsaya mata agarin nan, wnada xai sashi ya ajeta. Baiwar Allah kuwa na tsugene gaban akwatinta, tana ruasar kuka har karfe 10pm. 'yan ganin kwakwaf suka gaji suka koma gidajen su dauke da labari mai ban al'ajabi. Wasu suna ganin bai kamata Uban dawaki ya koreta ba a matsayin sa na Uba, kuma babban mutum mai sarauta, wasu kuwa suna ganin hakan shine daidai, imna xai sa BAKIN CIKI? Idan bai sallame ta ba, tunda ta tara masa, ya cika masa xuciya, tana neman fashewa ta hallakashi? Ai gara da ya sallamata duniya ta koya mata hankali. Ga darasi na farko nan ta fara gani, duk iskancin Danlitim yace baxai aje taba. Alhalin saboda shi aka koreta. Wannnan ya nuna a fili ita ta nace masa kamar sauran 'yan mata marasa xuciya. Mutane na mamaki abinda Danliti yake da shi wanda yake tsonewa 'yan Mata ido. Su mutu cikin soyayyar sa. In bata ga kyau me yake da shi? Shi babu hali babu kwakkwaran asali. Amma duk wacce ta fada tarkonsa sai gagari iyayenta. Ko don kudi da ya ke kashe mus ne? Shiya sa suka dauki laifi kacokan suka dorawa 'yan Matan masu biye masa don kwadayi da kyalekyalen jikinsa. Wayyi, kai bai san dawan garin ba, dai bai yi tunanin kutsa kansa ciki ba. Tun ciki dare surutai kala- kala suka fara baza gari. Shi kuwa gogan da ya ga kowa ya watse sai ya matso ya xunguri Mama da kafa, ta dago kai da sauri ta dube shi, matso mana nan kiji, ta matsa gareshi, tana hawaye. Ya dubeta da kyau yace, ke banxa ce wlh, shi ya sa kika bani haushi. Nace ba xaki xauna anan ba. In banda hauka irin naki, ya xa'ayi ki xauna tare da mu cikin shago? To ina sane da abinda nakeyi, kin gane? Saboda haka ki koma ki nemi wani wurin ki xauna, ki bani nan da sati xan san abinyi. Murya dushe tace, ni bansan inda xani ba, a'a ko gidan 'yanwanku ba xaki je ba? Ko baku da su ne? Sai dai inje gidan su Baraka, yace ko gidan su Mubarak xaki, sai kinm dawo matsalar kice. Amma ba xaki kwana shagon nan ba. Yauwa, tashi ki sungumi akwatinki, ki wace kar su kulle gidansu. Tace to nagode, sai da safe, Allah ya kaimu 'ya bebine. Muyi fada mu shirya ko? Kar ki damu xan ganki goben. Tayi murmushi, dadi ya rufeta, ta mike tana kara masa godiya, taja akwatinta ta nufi gidansu Baraka. Ya mike janye da benci yana kyalkyala dariya, ya shige shago. Kai mugu dan gidan buzu mai shayi! Yayi wa kansa kirari ya shige daki. Ayuba na kallonsa yana kada kai. Gidan su Bara akulle yake, saboda sha dayan dare tayi ma. Ta shiga bugawa har aka xo aka bude mahaifin Baraka ke tsaye cikin xauran, ya dubeta da kyau yace, Mama ce? Daga ina haka? Ta fara kuka yace shigo shigo ciki! Ta wuce da uban akwati ya maida kofa ya rufe. Tana gaba yana biye da ita yana fadin, subhanalillahi! Dakin Inna saude suka shiga tana tsaye tsakar daki, lfya? Ta xube sharaf! Cikin kuka tace, abba ne ya koreni..... Ina saude ta nemi waje ta xauna, yayin da malam kasim ke fadin, me ya sa Uban dawaki xaiyi hak? Inna saude tace BAKIN CIKIN ta ne ya ishesu. Ace kamar Mama ta gagari kowa duk abinda ya sameta da abinda ake gaya mata ba su isheta nadama ba, idan ba su koreta ba me kike so suyi miki? Ba shashanci kike sha'awar yi ba? To sun baki hanya, meye kuma na kuka? Mal. Kasim yace hakan ba hujja bace, duk abinda xatayi, gara tana gabansu suna tsawata mata, yau da gobe ana hada mata da addu'a, sai Allah ya taimaketa ta gane illar abinda take aikatawa. Saboda haka ta xauna, gobe Allah ya kaimu lfya, xanje in ganshi. Ke kuma je ki kwanta kiyi tunani, meye amfanin lalata rayuwarki da kikeyi? Har jikokinki sai an yi musu gori, wannnan abinda kika aikata! Kina da babban laifi mama, sai kin tuba kin bi Allah kin bi iyayenki sannnan xaki ga daidai a rayuwarki, kinji ni? Ta amsa da kai, yace ta shi ki shiga wajen 'yar uwarji kafin Allah ya kaimu goben. Ta mike simi-simi ta ja akwatinta, inna saude ta xuba mata ido tana mamakinta. Ta kada kai, taca baka ce xata aikata ba, yarinya kyakkyawa, ta lalata rayuwarta. Allah ya shirya mana, yace amin albarkar annabi. Atsakar gida taga Baraka tsaye tana share hwaye, ta matso ta kama mata akwatin suka shiga dakin, kowacce ta nemi wuri ta xauna bakin katifa. Baraka ta dubeta......... Tace anya mama abubuwa da kike yi kanki kalau? Ke bakijin kinya? Baki tunanin gaba daya idanuwan garin nan sun dawo bisa kanki? Baki da martaba da darajar Abba agarin nan? Haba Mama, kamar ba tare muka taso ba? Tarbiyarmu iri daya, nutsuwa da kamun kai, kowa na yabon mu. Mutane na rububin mu, da son hada xuri'a tagari. Ta daga kai sama, idanuwa cike da hawaye ta cigaba, Allah ya isa tsakaninmu da Danliti! Ta dube ta sukayi ma juna xuru kafin Mama tace kar ki sake xagin Danliti Baraka, alhakin sa xai kamaki, laifin mune? Tun tym din da mukace muna son juna, ya kamata su Abba su rungume mu hannu 2 amma suka ki, suka gwammace in kwashe kayana in bishi. A tunanin ki wane sakamako ya kamata su gani? Bayan wannan dake jikina? Baki sake take kallonta, kafin tace, maganar Banza ce, idan duka jina kunnuwa ne xai taba sauraronki ba, wa kika burge don kin aikiata wannnan sakarcin? Shi kansa Danlitin adage yke kallonki. Kin dawo an yi miki afuwa, cikin nman ya bayyana, duk sun hkr, sun shanye, amma ki ntsu xuwa tym din da xaki haihu, a daura maki aure, kar fa ki manta xaman nan naki agida ibadane tunda Allah ya shifida hakan, sai ki ga dalilin xaman, duk xunubunku sun kankare, auran ku yayi karko tare da xuria masu albarka. Ki kwanta kiyi tunani mama, ko asiri Dan liti yayi miki, xakewar taki tayi yawa. Ta sualala kafita ta kwanta, tace, na kwanta shekiya Baraka, sai da safe ko? Ta bita da kallo ta numfasa, tace Allah ya sa ki gane. Amin, ta amsa da gatse ta juya baya abinta. Baraka ta mike ta rufe daki ta dawo ta kwnta. Ta jima bata sami barci ba, saboda juyayin halin da 'yar uwarta ta shiga. Da farar safiya M.kasim ya usa gidan Ubban dawaki yasa aka yi masa sallama da shi, jin cewa shine ke sallam ya sa yace ya shigo cikin gida. Bayan su gaisa. Umma ta fito suka gaisa. Sannan ya maida jawabinsa, a karshe yace, alhaji kar bacin rai yasa ka yanke wannan hukunci, ni ina ganin gara yarinyar nan ta xauna agaban ku, kuna tsawata mata, sai Allah ya taimakemu ya shiryar da ita. Don girman Allah ka yafe mata dawo gida, tunda tayi tunani taxo wajenmu, ta kawo mana kukanta. Abba ya gyara xama yace, a tunanin ka a kashin kanta, ta yanke shawara taje wajen ku? To ba haka xancen yake ba, kila ba xaka sani ba ne, saboda kuan cikin lungu. Amma ni tun jiya na sami labarin wulakancin da yaron nan yayi mata, ya tara mata jama'a, ya tozarta ta, ya kuma ce ba xata xauna masa a shago ba, kaji dalilin nemanku, amma ba nadama tayi ba. Yace, duk da haka ina son ka duba girman da martabar ka agarin nan. Kayi hkri ka amshi rokona, ba don ni ba, sai don girman Allah da darajar iyaye. Ya sunkuar da kai yana kadawa, kafin yace, M.kasim ban ki ta taka ba, amma ba xan iya xama da yarinyar da ban isa in bata umarni ta bi ba. Ta fita tayo shashancinta, ta dawo min gida ta wanke najasa ta kwanta. Mts! Ban jin idanuwana xa su iya jure gainin wannan kaxanta. Gara ta tafu su cikashe. Wlh na hkr da ita, kuma ina rokon Allah ya sanya mana dangani nida Mahaifiyarta, ba kuma xamu gaza ba wajen yi mata addu-ar shiriya. Watakila wata rana taga uwar bari, ta dawo da kanta ta neme mu. Kaga a tym din xan tabbatar
Chapter 55 · 0% Book details